su shigar da adu'a kafin tashin ɗalibai a makaranta".
Yami tace,"haka ne kuma, tunda su gidan malamai ne ko saukar ƙur'ani a iya yi cikin ƙaramin lokaci".
Maijidda ce ta kira Amir, kuma tun kamin ta sanar masa yasan babu lafiya tunda yaji muryarta tana kuka. kuma zata iya rantsewa da ta faɗa masa faɗuwa yayi a inda yake saboda yanda taji ya saki salati a gigice.
ƙarar salatin da kowa sai da ya jiyo daga cikin wayar, wannan yasa Kaka ta ƙara ruɗewa hankalinta yayi ƙololuwar tashi.
kowa dai a wajen yayi shiru, zuciyar kowa da abinda take saƙawa, daga ƙarshe dai Baffa yace su Zaytuna su kwaso kayan Kaka a taho da ita ɓangarensu, hakan kuma akayi suka ɗaukar mata abinda zata buƙata suka taho da ita wajensu ita da Maijidda da har yanzu ita ɗaya ce bata bar kukan fili ba.
kuma ita kowa yafi jin tausayi bayan Kaka, tsabar kuka idonta sunyi luhu-luhu.
ɓangaren Ameer kuwa har drip aka saka masa, dan lokacin da aka faɗa masa akan machine yake bai san ma sanda ya saki kan machine ba ya faɗa wani rami shi da machine ɗin, duk ya kurkurje yay rauni a duk jikinsa, ƙarshe sai wasu bayin Allah ne suka kaishi asibiti, a asibitin ya bayar da lambar Mahaifinsa aka kira nan da nan kuwa sai ga asibiti ya cika da mutane, abinka da me tarin ƴan'uwa.
Innarsa na zuwa ya faɗa mata abinda ya faru, kuma take ta ƙaryata tace sai dai in ko yaranne a ƙuruciyarsu suke so su gwada shi da irin son da yakewa Fillo, sai dai itama ko da ta kira abinda Yami ta faɗa mata kenan, Amir dai nata kallonta with his all hope ace ƙaryar suke yi masa, gwada shi suke so suyi, kuma in har gwajin ne yasan yayi nasara, sai dai zai faɗa musu kar su ƙara yi masa irin wannan wasan gudun rasa rai wataran.
sai dai tana ajiye wayar yaji tana faɗawa mahaifinsa halin da ake ciki, dan haka nan da nan brothers ɗinsa suka watse akayi gida dan fara karatu da adu'oi. faɗar dai tsananin tashin hankalin da Amir ke ciki ba zai misaltu ba, don lokaci ɗaya har ya faɗa kamar wanda ya jima yana jinya, Dr ma har yana cewa in ba'a kiyaye an nema masa abinda yake nema ba zuciyarsa zata iya taɓuwa.
a daren wannan ranar dai Kamar yadda Fillo bata iya runtsawa ba, haka ma Hajiya Madina, Kaka, Maijidda da kuma Amir, dan Amir saura kaɗan ya rage ma ya bar asibiti a daren ya fita nemanta.
Tashin hankali dai duk bai bar kowa ya runtsa ba, yaran Hajiya Madina kansu sun kasa bacci saboda halin da mahaifiyar su ke ciki, shi kansa Baffa har sannan yana kan matarsa yana bata baki.
at the end dai Baffa yaga zaman kukan duk ba shi bane, dan haka yace kowa yay sallah ai adua, a haka suka raya wannan daren daga masu sallah sai masu karatun qur'ani sai masu tasbihi haka har asuba da tayi.
bayan sunyi sallar asuba Anty Zulfa ƙanwar Hajiya Madina da tazo ita ta zauna tana jero Adduo'i kowa na amsawa, cikin adu'ar suna roƙon Allah ya kare Fillo a duk inda take, ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, da ameen suka amsa har ta idar suka shafa, suka shafa aduar a daidai sanda Baffa ya turo ƙofa ya shigo.
ya zauna akan kujera idon kowa akansa, ya numfasa sannan ya shiga yi musu bayanin abinda police suka ce game da report ɗin da aka shigar.
yace,"ku kwantar da hankalinku dan Allah tunda dai har Police sun riga sun shiga maganar, kuma yanzu zasu ƙara bazama gurin nemanta".
ya kalli Kaka yace,"na basu hotonta da shi saurayin nata ya bamu, kuma duk an baza shi a lunguna da saƙunan garin nan, an miƙa cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hoton nata".
cikin kuka Hajiya Madina tace,"to amma me yasa zasu shigo da tunanin cewar Kidnappers ne suka ɗauketa. Baffa idan sune ai da tuni sun kira waya, mun kwana na biyu fa kenan Baffa, Kidnappers ba zasu yi shiru har haka ba. dan Allah Baffa a dai ƙara bincikawa ƙila wani wurin tayi, idan kuma kidnappers ɗinne a nemo su, su faɗa mana abinda suke so". ƙarfin kukanta ya katse maganar tata.
to wasa-wasa dai har tsawon kwana uku lamarin Fillo shiru, Kidnappers ɗin da aketa tunani suma shiru basu kira ba, wannan ya ƙara ɗaga hankalin kowa, aka kuma bar tunanin cewa kidnapping Fillo akai, dan idan shine tuni sun kira waya, abin dai yafi kama da ɓata, Kaka na batun ita gwarama taga gawarta ta huta.
adu'a kawai ake ta ko'ina, sadaƙa kuwa a gidan Alƙali Dikko babu dare babu rana.
Amir kuwa yana can ba ci babu sha saboda tsananin damuwa, musamman idan ya zauna yana tuna moments ɗinsu shi da ita.
lamari fa ya ƙara ta'azzara, dan tun ana lissafin kwanaki aka daina aka shiga sati, to abu kamar wasa daga sati ɗaya sai gashi an tafi sati na biyu har an shiga na uku.
daga nan kowa ya saddaqar da cewar an rasa Fillo har a bada, kuma duk wannan bidiri da ake Turaki bai sani ba, da ya kira waya Zaytuna kawai shaida masa tayi sunyi tafiya ita da Kaka zasu yi wata guda.
amma tun ranar da sukai waya da Maama yaji hankalinsa bai kwanta ba, tace masa kar ya damu ciwon kai ne ba wata matsala ba, ya zauna yay concentrating kan sabon project ɗin da Baffa yasa su.
haka kuma d