nnun nata tana shafawa, jinin da ya daskare waje ɗaya na saki yana bin ko'ina, kamin a hankali taji dama-dama.
ba ta so ya ƙara yi mata tsawa don haka ta ɗauka pure water ɗin ta kuskuren bakinta ta zubar da ruwan a jikinta, sannan ta janyo kwanon abincin ta buɗe, taliya ce jallof babu kyan gani, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta tashi, amma saboda babu yanda zata yi dole ta shiga cusawa a bakinta tana taunawa da ƙyar.
ganin ta fara cin abincin suka tashi suka nufi ƙofa zasu fita, tai ƙarfin halin cewa,"bani da kowa sai Kakata, ku taimaka min dan Allah".
suka mata shiru suka fice suna rufe ƙofar, sai kuma taji an ƙara buɗewa ƙaton mutumin ya leƙo yana faɗa mata,"if you dare try to make any sound, i swear I will fill your brain with this". ya faɗa yana mata nuni da bindigar hannunsa, kuma ta tabbata he means it.
taji alamun an saka key a jikin ƙofar which means sun ƙulleta kenan, sai ta ture kwanon abincin dake gabanta, tabi ƙafarta da kallo tana noticing yanda ta kumbura sosai, ta jawo ƙafar da ƙyar tana shafata sannan tayi ƙokarin zuro ƙofar ta sauko daga kan gadon tana tsayawa akanta.
da ƙyar taja ƙafarta bayan ta ɗauko pure water ɗin ta isa bakin wata ƙofa da ta gani acikin ɗakin, daban da wacce suka shkigo. ta kama handle ta buɗe ƙofar a hankali sai taga banɗaki ne, tai saurin faɗawa ciki tai tsarki sannan tayi alwala ta fito.
ɗankwalinta tasa ta tattare ƙasan wajen, bata san ina ne gabas ba, kuma lokaci ɗaya maganar Amir ta haska mata sanda yake cewa shi addini ɗan sauƙi ne, idan ka tsinci kanka a garin da ba naka ba, kuma babu mutane a wajen da zaka yi sallah balle ka tambaya, to kana iya fuskantar ko'ina ne ka tada sallarka, don haka ta fuskanci inda take jin yafi kwanta mata ta tada sallarta da babban mayafin dake jikinta, sai da ta rama sallolin jiya dake kanta tukunna tayi asuba ta kuma yi sallar wadha ɗin da bata wuceta.
Bayan ta idar bata yi saurin tashi a wurin ba sai da tayi dogayen adduoi sannan tai saurin miƙewa ta koma kan gadon gudun kar su dawo ɗakin su sameta.
ta zauna da yaƙinin duk sanda suka kawo mata abinci zata yi amfani da ruwan wajen yin ibadarta. kuma zamanta kenan cikinta ya murɗa, tasan ba komai bane face yunwa, kuma take sai amai saboda tuntuni take jin zuciyarta na tashi saboda wannan farar taliyar da ta ci mara ɗanɗano.
har yanzu tunaninta guda ɗaya ne, ta ina zasu fara neman wanda suke saka ran zasu biya kuɗin fansarta?, alhalin a wannan duniyar babu wanda ya san da su banda Allahn da ya halicce su.
a can ɓangaren kuwa tunda gari ya waye ƴan sanda suka ƙara tsananta bincikensu, har sannan kuma ba'a sallami Hajiya Madina ba don ita tace gwara a barta a asibitin har sanda za'a ga Fillo sannan ta koma gida ta iya haɗa ido da Kaka, amma banda cikin critical situation ɗin nan da suke ciki.
sai dai tunda ta farka ta tashi da zullumin ko zasu ji labarin cewar an ganta, amma police ɗin na daɗa faɗa musu shiru babu labarin yarinyar, sai dai sun sanar da Baffa cewa za su cigaba da bincike insha'Allah, kuma ganin har rana tayi still babu wani labari ya saka dole aka sanar da Kaka halin da ake ciki.
ba Kaka kaɗai ba, hatta ƴaƴan Hajiya Madina sai a sannan suka san abinda ya faru banda Khalil da ya san komai tun a jiya. dan Baffa ce musu yayi sun ɗauki hanyar abuja a lokacin Maama na da seminar a gobe ƙarfe 8.
Kaka dai mutuwar zaune tayi daga inda take, tabi Hajiya Madina da Baffa da Khalil da kallo, kamar dai bata fahimci zancen da suke mata ba, kamar ba dai-dai taji ba, kamar suna so suce Fillo ta ɓata tun daren jiya kuma har zuwa yammacin yau ba'a ganta ba, wannan mummunan labari ne, kuma bata tunanin waɗannan salihan bayin zasu iya zuwar mata da shi.
Hajiya Madina ta fashe da kuka ganin yanda Kaka ta daskare, tana cewa,"ki yafe min Kaka, wallahi ban san hakan zata faru ba da ban fita da ita ba".
Yami dake tsaye itama ta kasa motsi take kallon Maama da tausayawa tace,"ki daina kuka Hajiya, tsautsayi ne, kuma cikinmu babu wanda bai san ƙaddara ba me kyau ko mara kyau".
sai sannan hawaye ya sauko a fuskar Kaka, dai-dai take ji da gaske faɗa mata suke jikarta ta ɓata, tayi inda ba'a san ta nufa ba, kuma yini guda babu ita babu labarinta.
cikin muryar kuka tace,""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Rahimu ka bayyana mana yarinyar nan a duk inda take, ka dawo da ita garemu cikin amincinka".
ta faɗa tana mayar da idonta kan Hajiya Madina tace,"ki daina kuka Hajiya, ba ki da laifi ko ɗaya, dama ubangiji tuni ya shirya faruwar hakan, ko ace bata dalilin fitarku ba, ni musulma ce nayi imani da ƙaddara, saboda haka ki daina ɗorawa kanki laifi, ki share hawayenki don Allah, adu'a kawai ya kamata muyi Allah ya tsareta a duk inda take ya kuma dawo da ita garemu cikin amincinsa".
sannan Kaka ta ƙara maida dubanta ga Maijidda dake ta uban kuka, tace da ita,"ki kira Amir a waya ki sanar masa".
Yami tace,"a sanar masa kuwa?".
Kaka tace,"to ɓoyuwar ai babu amfani, gwara a faɗa masa ɗin sai