NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 143 of 323

nna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil. ta buɗe idanunta ruwayen hawayen ciki na samun damar gangarowa, kuma a sannan ta fahimci hasken dake ta wajen window da take gani gari ya fara wayewa kenan?. take kuma ta tuna da cewar fa bata yi sallar magriba da isha'i ba, ga asuba ma a kunnenta akayi amma bata yi ba. taja ƙafafuwanta da suka sandare tana so ta lanƙwasa su sai taji kamar zasu karye idan tayi hakan, saboda azabar ciwon da suke yi mata. babu ta yanda zata iya miƙewa ta tashi ko da zaune ne, balle kuma ta iya sauka daga kan gadon, dan haka kawai sai ta fashe da kuka sosai, can bayan wasu awanni taji muryar mutane ƙasa-ƙasa a bakin ƙofar ɗakin. Ta juyo da fuskarta tana kallon ƙofar, tana kallo aka turo ƙofar mutane uku suka shigo, Ƙaton cikinsu shi ya fara shigowa tukunna wasu sirara suka biyo bayansa bayan ɗayan cikinsu ya maida ƙofa ya rufe. tana kallo su suka ƙaraso bakin gadon, Ƙaton ya jawo wata kujera ya zauna yana facing ɗinta, tana kallo yaywa ɗaya daga cikinsu alama wanda shine duk yafi siranta a cikinsu, ya zagayo daga bayansa ya hau kan gadon ya ɗagata ya zaunar da ita, sai a sannan ta sami damar ƙarewa inda take kallo da kyau da kuma mutanen dake tare da ita fuskokinsu duka a rufe. ƙatoton ya auna Fillo da bakin bindigar da take hannunsa yace,"zamu buɗe maka bakinka, idan har muka buɗe kayi wani yunƙuri na yin magana ko kuma ihu sai na fasa kanka da alburushi". Ya faɗa muryarsa da ƙarfi har tana amsawa a ɗakin, sai dai kana jin hausar tasa kasan riƙaƙƙen inyamuri ne. hawayen Fillo ya ƙaru akan fuskarta, tana jijjiga masa kai alamar taji me yace cike da tsanin tsoro gami da tashin hankali. Ƙaton ya kalli tsamurmurin dake kan Fillo tsaye yay masa alama da bakin bindigarsa. take tsamurmurin yasa hannu ya ɗaye masking tape dake manne da bakin Fillo, tsananin azaba yasa ta rumtse ido don ji tayi kamar ya haɗo da fatar bakin nata ne ta cire. so ta ke tasa hannu ta shafa wurin ko ta sosa amma babu dama, tunda basu kunce mata hannu ba, saboda haka sai ta rumtse idonta sosai tana jinginar da kanta da bango har sai da taji zafin ya lafa tukunna ta buɗe. ta buɗe ido ta sauke kan ƙaton mutumin dake latsa waya, rabin fuskarsa rufe take da hanky, tana kallo ya ɗaga hannunsa, ɗayan mutumin dake tsaye tun ɗazu a bayansa ya zagayo ya dire kwanon abinci a gabanta da pure water guda ɗaya. sai tabi kwanon abincin da kallo sannan ta ɗago ta kalli ƙaton dake saita da ita da bindiga, ya zare mata manyan idanuwansa yace,"buɗe kaci". tana ƙoƙarin danne kukanta tace,"dan Allah zan fara yin sallah tukunna". mutumin ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata, a tsawace yace,"kaga nayi kama da wanda ke yin Sallah?, to nan wurin da kake gani ba'a sallah, ko adu'a muka ji kayi sai mun ɓula kanka da alburushi. adu'a ɗaya muka yarda kayi shine a biya kuɗin fansarka, daga wannan bamu yarda da kowanne kalan adu'a daga bakinka ba, do you hear me well?". da sauri ta ɗaga kanta sai dai bata jin zata iya ta zama haka ba tare da sallah ba, don haka ta ƙara buɗe baki tace,"nayi muku alƙawarin wallahi ba zanyi wani motsi ba, ko adu'ar ficewata daga nan ma ba zanyi ba muddin ba zaku cutar da ni ba, amma don girman Allah ku barni nayi sallah, ko magriba da isha'i na jiya banyi ba". tana rufe baki mutumin ya buga mata bindigar hannunsa a bakinta yace,"only when you are out of here shine zaka je kayi ta sallolinka, but not in this place, sallah acikin wurin nan is prohibited from you". sai kawai ta fashe da kuka sose tare da faɗin,"to su waye ku?, Me nayi muku?, Me kuke so tare da ni?". ƙaton mutumin ya bushe da dariya yace,"mu kidnappers ne, kuma ba zamu sakeka ba har sai an biya kuɗin fansarka naira miliyan biyar, idan kuma ba'a biya ba zamu yi gunduwa-gunduwa da namanka sannan muka aikawa da iyayenka". cikin matsanancin kuka Fillo ta ambaci kalmar innalillahi a karo na babu adadi tun bayan farkawarta, suna batun miloyan biyar kafin a karɓeta. wa take da shi da zai biya waɗannan maƙudan kuɗin?, me Kaka zata ɗaga ta siyar a sami waɗannan kuɗin?, ta san babu me biyan waɗannan kuɗin a karɓeta kamar yanda babu abinda Kaka zata ɗaga ta siyar a sami wannan uban kuɗin. saboda haka sai kawai ta rumtse ido tana jin tana sallamawa da duniyar, ita kuma haka kalar ƙaddarar take?, fatanta guda ɗaya ko da ace ba zata fita anan tana roƙon Allah yasa kar mutanen su cutar da ita su rabata da mutuncinta, a hankali yanda ba zasu ji me tace ba ta furta,"Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan cikin amincinka da salamarka". Ƙaton mutumin ya ƙara sakar mata tsawa yana cewa,"buɗe abinci kaci". tana kuka cikin firgici da razanin da take ciki tace,"babu ta yanda zanci ai". sai a sannan ya tuna da cewar a ƙulle take, ya daɗa kallon wanda ke tsaye kanta ya bashi umarnin kunceta. cikin zafin nama tsamurmurin ya kunceta kamar zai wurgata ta faɗo ƙasa, sanda ya gama kunceta ɗin sai ta sauke ajiyar zuciya saboda relief da ta samu, ta kama ha
🏠