a suka ɗauke Fillo suka fito daga cikin gari, lokacin ne kuma suka ƙara speed na motar, gudu na fitar hankali suka dinga shararawa akan titin da babu kowa, gudu na ganganci kamar basa son rayukansu. sai da suka yi tafiya a ƙalla ta awa guda sannan suka shigo cikin wata unguwa, daga nan kuma suka fara tafiya with normal speed gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sosai sannan suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, haka suka dinga wuce gidaje da shaguna, sai da suka zo kan wani incomplete building tukunna sukai parking motar, ɗaya daga cikin su ya fita ya buɗe gate suka shiga da motar ciki.
compound ɗin gidan ƙato ne, sai da suka je har entrance na shiga cikin gidan sannan sukai parking a wajen. na gaban motar shi ya fata fitowa yana cire face mask ɗin fuskarsa da ya dame shi, sannan wanda yay driving motar ya fito, sai ɗayan da ya rage a baya ya cicciɓo Fillo kamar wata jaririya, shima ya fito sannan suka nufi cikin gidan a tare da sauran. Babban parlo ne da ba'a gama ginasa ba but ansa tiles anyi filasta paint ne kawai ba'ayi ba sai ƙarashen wearing, suka wuce zuwa wani dogon corridor inda ananne zaka tarar da jerin ƙofafi na rooms, a ƙofa ta ukun ƙarshe suka tsaya, ogan nasu shi ya buɗe sannan wanda ke saɓe da Fillo a kafaɗa ya fara shiga, yana shiga ya kwantar da Fillo kan wani ƙaramin gado kamar gawa.
Madaidaicin bedroom ne da shi kaɗai akai completing gininsa acikin ɗakunan dake gidan kusan guda 7. ogansu ya ƙaraso gadon ya zauna daga gefe, yasa hannu ya mammari fuskar Fillo don tabbatar da nauyin sumanta, sannan ya ɗago kansa ya kalla ɗaya daga cikin yaransa yay masa alama da yazo.
mutumin da duk cikinsu shine ƙato yazo ya hau kan gadon riƙe da shimfiɗeɗiyar igiya a hannunsa, ya jirkitar da Fillo gefe ya ɗaure mata hannayenta ta bayanta, ya kuma haɗa ƙafafuwanta wuri ɗaya suma duka ya ɗaure, sannan ɗaya daga cikinsu ya miƙo masa masking tape ya nannaɗe bakinta da shi.
Sai da suka tabbatar ko da ta farka babu ta yanda zata iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi tukunna duk suka fice daga ɗakin suka barta ita ɗaya suka rufe da key.
Fillo dai bata farka ba sai da ana tada iƙama na sallar asuba, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin nauyi, ga warin wani abu a ƙofofin hancinta, gaba ɗaya wani irin ciwo jikinta keyi mata tamkar wadda aka ɗau kwanaki ana duka, ta rufe idonta ta rumtse sose sannan ta buɗe tana jin eyelid nata yay mata nauyi sosai, sai a sannan kuma ta fara bin ɗakin da kallo har ta sauke ganinta akan roof na ɗakin, sose take kallonsa da mamaki sannan ta ƙara juyar da ƙwayar idonta ta sauke akan ƙofar ɗakin, daga roof ɗin har ƙofar basa cikin irin waɗanda ta sani, ba ƙuma sa cikin inda tasan tana kwana. daga paint na ɗakin har kan gadon da take duk bata san su ba, to aina take?.
tana ci gaba da bin ɗakin da kallo tana so ta tuna a inda take, da kuma yacca akayi tazo nan ɗin amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta cunkushe taƙi yin tunanin abinda take so. sai tayi ƙoƙarin motsawa don ta tashi amma sai taji ta kasa, ta ƙara yunƙurawa taji babu ta yanda za'ai ko da hannunta ya motsa balle ƙafarta, wannan ya tabbatar mata da cewar a ɗaɗɗaure ta ke gaba ɗayanta.
sai sannan tayi ƙoƙarin buɗe bakinta tayi magana shima sai taji bakin a liƙe yake, ta hanci kawai ta ke numfashi banda baki. sai ta rufe idonta tana juyar da fuskarta ɗayan side ɗin sannan ta buɗe idon, nan ta ƙara tabbatar da bata san ina ne nan ɗin ba, take ta fara kokawa da numfashinta saboda tsoro, dai-dai lokacin kuma taji ana sallamewa daga sallah a masallaci, sallar da ta fahimci sallar asuba ce tunda raka'a biyu taji anyi, cikin kanta taji ƙwaƙwalwarta na biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kuma a hankali cikin ikon ubangiji tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata.
sai ta rumtse idonta hoton komai na haska mata tarr tun daga ɗora wuƙa a maƙoshinta, da shigar da ita cikin mota, da kuma juyowa da akayi aka toshe mata hanci. take tayi ƙoƙarin ƙwalla razananniyar ƙara sai taji ashe fa bakinta a manne yake.
to Ina ne nan ɗin?, waɗanda suka ɗaukota su waye?, me yasa suka yi mata irin wannan ɗaukowar?, nan ɗin da suka kawota me zasu yi mata?, me yasa suka ɗaɗɗaureta haka har da toshe baki?. tarin tambayoyin da ta yiwa kanta kenan, kuma take ƙwaƙwalwarta ta bata amsa da,_"you have been kidnapped"._ take kuma zuciyarta ta ƙara maimaita mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
ƙirjinta ya dinga bugawa hawaye nabin kuncinta, tashin hankalinta ɗaya shin wanne hali Kaka ta ke ciki yanzu?, Wanne hali Amir yake ciki?, wanne hali Maijidda da Yami suke ciki?, ya Hajiya Madina zata kasance idan ta dawo taga babu ita?.
idan har kidnappers ne suka ɗauketa shin sunyi contacting da wani nata?, wa suka tuntuɓa?, adadin nawa suka nema kuɗin fansarta?, wa zai biya maƙudan da suka ambata?, sai brain ɗinta ta ƙara biyo mata innalillahi wa'i