"to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan".
da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti.
Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa.
ganinsa yasa Ɗan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita.
"Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer.
ya kalla Baffa yace,"Patient ɗin ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci ɗaya shiyasa BP ɗinta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai."
Ɗakin Baffa ya shiga ya tarar da ita a kwance tana bacci, ya zauna gefenta ya kamo hannunta yana ta kallonta, tausayinta yayi matuƙar kama shi, ya sa ni fiye da hawan jini ma za'a iya faɗa indai akanta ne, saboda ita macece da bata iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa nan da nan musamman akan ƴaƴanta, haka ma akan wanda ta damu da shi, ta kan kasa juriya da dauriya.
ya san tana matuƙar son Fillo, dan ko da yaushe suka zauna tana yawan masa labarin yarinyar, irin tarbiyar yarinyar da hankalinta da natsuwarta da kamun kanta, har ta kance masa ita ina ma ace yarinyar ta zama rabon wani acikin Khalil ko Turaki.
kuma sau tari tana faɗa masa insha'Allahu zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin itama rayuwarta ta inganta, yarinyar ba kalar yaran da za'a banzatar da rayuwarsu ba ne.
Hajiya Madina bata farfaɗo ba sai bayan sallar isha'i, kuma tana farkawa idonta ya sauka akan Baffa dake waya da wani police yana shaida masa ɓatan Fillo, sai dai suna haɗa ido yay saurin sallama da police ɗin gudun kar taji a ƙara samun matsala.
ta kama hannunsa tana faɗin,"Baffa yarinyar mutane, ƴar mutane ta ɓata a hannuna Baffa, me zance da iyayenta Baffa?, me zan faɗawa mijin da zata aura Baffa?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi wallahi banda masaniyar inda tayi, Baffa wallahi da nasan hakan zata faru ba zan fita da ita ba".
daga yanayin yanda take maganar kasan bata cikin hayyacinta.
sai kuma tayi shiru tana kallonsa kamin cikin sanyin murya tace,"Baffa an ganta ne?, Ɗan Usaini ya nuna motar mutanen?". ta faɗa tana sakin kuka me ban tausayi.
Baffa Ya kama hannunta sosai, ya kwantar da murya yace,"Please stop crying, Insha'Allahu za'a ganta very soon, ba wai ɓata tayi kamar yanda muke tunani ba insha'Allah".
tace,"Baffa ta ya?, Ɗan Usaini fa yace yaga motar da bai yarda da ita ba, kuma fa lokacin ne ta fito ta kawo min wayata, Baffa me kake tunanin ya faru?".
Baffa ya ƙara sauke numfashi sannan yace,"ki bar wannan tunanin Madina. kuma insha'Allah cikin daren nan zamu ganta, nayi report mawa police and zasu fara aikin nemanta yanzu".
sai ya ɗauko wayarsa yay dialling numbern Inspecter Sise, yana ɗagawa yace da shi,"ta farka, wanne irin bayani kuke buƙata daga wajenta?".
Inspecter Sise yace,"ka bata wayar muyi magana". Baffa ya kalla Hajiya Madina sannan yace da Inspecter,"tana da saurin ruɗewa, please a san irin tambayar da za'ayi mata".
tambayar kayan dake jikin Fillo da kuma yanayin yarinyar da kamanninta da yanda akayi ta fito duk su Inspecter ɗin yaywa Hajiya Madina, kuma duk ta ba shi amsa, sai dai daya tambayi hoto tace gaskiya bata tunanin yarinyar na da hoto ma.
daga nan kuma inspecter ɗin ya ƙara cewa da Baffa zasu yi arresting Ɗan Usaini domin shima zai iya zama suspect nasu.
motar police tazo asibitin cikin ƙanƙanen lokaci, aka sawa Ɗan Usaini handcuff aka wuce da shi, hankalinsa a tashe yana ta rantse-rantsen shi wallahi bai san komai ba akan ɓatanta, yaje kama ruwa lokacin, ai masa rai wallahi baida hannu.
To har wajen dai sha ɗaya na dare babu wani batu na ganin Fillo ko alamun ganinta, tun Baffa yana ganin ɓatan kamar da wasa har ya dawo ya ɗauke shi da gaske, a sannan kuma shima hankalinsa ya fara tashi. Hajiya Madina dai har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abinda takeyi, ƙememe kuma taƙi yarda aje gida a tambaya ko ta koma, sai Khalil kawai ta yarda Baffa ya kira ya gargarɗe shi akan kar ya bar kowa yaji zancen, kawai dai ya san yanda zai shiga wajen Kaka su gaisa ya gani ko yarinyar ta koma, shima kuma letter ya kira ya sanar musu bata nan.
a sanda waɗand