NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 140 of 323

nan taji numfashinta na seasn, sai kuma taji murya dai-dai kunnenta cikin raɗa da kakkausan amo ance,"wallahi kina ihu ko wani motsi sai na yanka maƙoshinki da kaifin wuƙar nan dake wuyanki". ai sai tayi ɗiff ta fasa yin ihun da tai niyya, idonta ya maƙale a driver seat sai taga drivern baya ciki, dan haka ayanzu bata da wani zaɓi da ya wuce umarnin da aka bata. tayi tsilli-tsilli da idanu tana jin yadda sanyin kaifin wuƙar ke wucewa har cikin zuciyarta. ta runtse ido sosai zuciyarta na tsananta bugawa, cikin kanta ya haska da kalmar mutuwa!, sai kuma gefen ƙwaƙwalwarta ya karanta mata ya ya Kaka zata ji labarin mutuwarta?, wanne hali Amir zai ji a sanda aka faɗa masa ta mutu?. tana ji mutumin yasa tsumma ya toshe bakinta sannan ya shiga janta har suka bar bakin motar, ita dai idonta wurgawa yake yana kallon ƙofar store ɗin da Hajiya Madina ke ciki, so ta ke ta hango fitowarta in yaso ta san ta yadda zata ƙwace bakinta ta ƙwala mata kira, sai dai har suka baro bakin motarsu aka zo da ita wajen da bata san ina ne ba, bata ga kowa a wurin ba ko da kuwa Maama. taji an buɗe motar da suke kusa da ita a yanzu an buɗe ƙofar baya. tana jin sanda wata murya daban da wacce ke riƙe da ita yace,"sakata aciki". duk wannan abin da ake har yanzu wuƙar na wuyanta motsi kaɗan suke jira tayi su fille kan. suka zirata acikin motar, tana kallon wanda ke front seat fuskarsa lulluɓe cikin bakin ƙyalle, wanda ke riƙe da ita yana shigowa ya rufo ƙofar, sannan ya ɗauke tsumman da ya rufe mata baki da shi, daidai da buɗewar bakinta zatai ihu, daidai kuma da juyowar na gaban ya danna mata wani tsumman da ya rufe hancinta da bakinta. take ta shaƙi ƙamshin wani abu a jikin tsumman, bata da ilimin sanin chloroform balle a yanzu da taji ƙamshinsa tayi ƙoƙarin ɗauke numfashinta, kuma wannan ƙamshin abin da ta shaƙa ya wuce har cikin kanta sai taji kamar zata mutu, ƙirjinta kamar ana rura wuta tana ci bal-bal, lokaci ɗaya kuma sai taji numfashinta ya sarƙe gaba ɗaya, ta kasa shaƙar iska, a hankali kuma sai jinta da ganinta suka ɗauke duka, nan take kuma tai laƙwas ta tafi luuu tana faɗawa jikin na kusa da ita. ba tare da ɓata lokaci ba motar ta bar wajen cikin speed ɗin da ba za'a taɓa zargan muggan mutanene acikinta ba. har sanda zasu wuce driver da ya dawo daga fitsarin da yaje ya bi motar da kallo, yana jin kamar bai yarda da motar ba har ta ɓacewa ganinsa. dai-dai nan kuma ya ɗaga kansa yana ganin me tahowa daga bayansa... *LULLUƁIN BIRI.......* *comment, vote and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Avoid error mistakes._ *32* ganin Hajiya Madina yasa drivern tafiya wurinta da sauri ya karɓi ledan kayan dake hannunta, a gaban mota ya aje manyan ledan kayan kusan guda 5, da gani kasan ba siyayya bace ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman tayita don yin kyauta ga Fillo. drivern ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kamin ya zagayo ɓangarensa har Hajiya Madina ta kula da rashin Fillo cikin motar. hakan yasa ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata?, ina Halimatu taje?". Ɗan Usaini ya dakata da buɗe motar yace,"Hajiya ai taje kai miki waya ni kuma naje ɗan yin uzuri". Hajiya Madina tace,"ban gane nufinka ba". yace,"ruwa naje kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo na dai barta ta shiga ciki kai miki waya". lokaci ɗaya Hajiya Madina ta fito a motar gaba ɗaya,"ka daina cewa ta kai min waya. kai wayar tun yaushe ne?, kusan fa minti biyar kenan, tana bani ta fito". Ɗan Usaini na waige yace,"to ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store ɗin". ya faɗa yana barin wajen, Hajiya Madina tabi bayansa. lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fillon zata je?, idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa zasu yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi. daga cikin store dai har wajensa babu Fillo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta. Ɗan Usaini na tare da me gadin store ɗin yace da Hajiya Madina,"ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa tayi". Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yacca take jin numfashinta na neman yankewa, iska ce a wajen ke ta kaɗawa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji ajikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta ya ɗauke. ƴar mutane ta ɓta ata sanadinta?, me zata ce da Kakar yarinya?, me zata ce da wanda ke shirin aurenta?. lokaci ɗaya kanta yay wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka, staffs dake cikin store ɗin suka fito dai anata ƙara lalube, tsawon kusan minti 30 inuwar Fillo ma ba'a gani ba. da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen.
🏠