NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 323

min kwano ba, ka tashi ka koma ka zauna ko kuma ka bar min parlo tun bamu samu saɓani da kai ba. Ni bana son tashin hankali haka kawai". Yusuf ya miƙe ya koma kan kujerar ya zauna ba tare da yace mata komai ba, ta kalle shi kaɗan ta kwaɓe fuska kamin tace,"yafi maka dai". "amma dai ina ce bayan na gama wayar na gaishe ki". Yace da ita yana kallonta. "bata yi min bane". "wa?". "ita gaisuwar taka". "ohh to Allah huci zuciyarki". Ta amsa da amin. Yaci gaba da danna wayarsa, tsawon mintina kusan uku yaji maganar Inna Wuro na cewa. "aiko ka akayi ne?". Bai zaton da shi ta ke ba, dan farko ɗagowa yay yana dube duben ta inda zaiga mutum, sai da yaga ba kowa sannan yace. "ba wanda ya aiko ni". "to kuma zaman ma mene?, zuwa da sassafe haka, babu fa jimawa aka gama min gyaran wurin nan. bana son a ɓata min waje dan ni ba fiya son ƙazanta nai ba...da ba za'a bar mutum ya huta ba dole sai anzo ɗaukar magana". Rufe bakinta kenan Aliyu ya shigo parlon, ta bishi da ido har sanda ya nemi three seater ya kwanta yana ɗora ƙafafunsa akan hannun kujeran. Haushi ya tuƙeta tace,"idan ka tashi Amadu ya gyaran wajen". Shi dai bai kulata ba ya ɗauko earpice a aljihu ya saka a kunne, Yusuf na kallosa yana mamakinsa, shi dai a wannan zamanin bai ga namiji mara lissafi ba irin Aliyu, yana namiji tunda akai hutun ASUU shikenan ya zama kamar mace, kullum yana gida sai shegen aikin jin waƙoƙin banza, yaƙi sana'ar fari balle ta baƙi, idan anyi magana yace ai Babansa ya tara musu...kuma in ana faɗa masa gaskiya Ammi tace ba haka ba. Ya jijjiga kansa kawai yana jan ƙaramin tsaki na takaici. Aliyu yace da Inna Wuro,"naga mutanen ƙauye sun zo". Tace,"to su tsaya a iya ɓangaren ku bana son gayya". Yay gajeriyar dariya sannan yace,"ya za'ai su zauna a ɓangarenmu?". Tace,"nima ya za'ai su sauka a ɓangarena?, Ni dai magana ta Allah idan kaje ka faɗawa Uwarka kar a soma turo min kowa, dan wancan karan banji daɗin zuwansu ba. Banda Amadu ya gina masai babba da ban san yanda zanyi ba, abunda ban taɓa gani ba sai a lokacin kashi har bakin masaina. Ɗoyi kuwa iri-iri babu kalar da ban guntsa ba, inda ace Uwarku ce kaɗai a gidan nan ai da warin kashin yaran ƙauyen nan shi zai zama ajalina. To sai Allah yasa akwai Falmata, tazo da kanta wallahi ta wanke min banɗaki nan ta sanya masa turaren wuta". Aliyu yace,"itama Ammin ai zata yi miki, dan dai bata sa ni ba ne, kuma ai da sai ki faɗa mata". Ta kama baki tace,"to ina ma ta ke zuwa waje na balle na sanar mata. ni fa idan kaga mun haɗu da ita Amadu ne zai yi tafiya mu haɗu a wajen masa rakiya kamar kishiyoyi, amma ni ina nake da wani arziƙi a wajen Zainabu...kana dai kallo ko gaisuwar safe". Bai sake cewa da ita komai ba. Ta miƙe ta ɗauki flask ɗin abincin da aka kawo mata tun ɗazu bata ci ba ta wuce da shi kitchen, dan idan ta barshi Aliyu ma saka masa hannu zai yi, shi kuma ba jin magana yake ba. Fridge ta buɗe ta saka yanda ma ko da wani ya shigo kitchen ɗin ba zai gani ba, har ta nufi ƙofa zata fita sai ta tuna ta dawo ta sakawa fridge ɗin key dan lemon da yake ciki sauran guda uku, Amadu bai san ya ƙare ba kuma cikin Ƴaƴansa babu mai ɗaukowa a ɓangarensu ya kawo mata, basu iya kawo mata komai ba amma sun iya suzo su cinye mata duk abinda aka ajiye mata. Bata dawo parlo ba sai da tayi sallar walha, tana zuwa ta tarar da Yusrah ta shigo, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ƙarasa bakin ƙofar ta jawo ta rufe tana faɗin,"kamin na huɗu ya shigo, ba dan ba dan ba sai nace Amadu gidan taron jama'a ya buɗe min". Ta murza key tana mitar,"kai da ɓangarenka amma ba za'a barka ka huta ba". Sannan ta saƙala key jikin abin maƙale labule tana cewa da su. "idan zaku fita ga key ɗin anan, idan zaku fita nace ba wai idan kunji knocking ba". Cikinsu babu wanda ya tankawa maganar da ta ke, dan haushi kamar ta rufe su da duka. ta kallesu su duka tace,"Amadu kuka share bani ba". Sannan ta juya ta koma ɗakinta. Yusrah ta zauna kan kujerar da Inna Wuro ta tashi, ta buɗe jakarta ta ɗauko office pins tare da madubi, ta shiga ɗaura ɗankwali. Tana ɗaurin ta ke cewa Yusuf. "Yaya ashe ka shigo. Ɗazu Ammi ke cewa ƙila har ka koma ba lallai ta ganka ba...idan ka gama abinda kake naji dai tana batun zuwa abuja yau". Ya ɗago da ido ya kalleta yace,"me zai kaita Abuja?". Time da ta ke gama ɗaura ɗankwalin tace masa,"biki mana...daughter ɗin ƙawar nan tata da aka haɗaku kaƙi, itace zata auri ɗan gwamnan jigawa". Ya maida idonsa kan wayarsa yace,"When will she come back?". Tace,"I don't know. but i heard her saying sati guda za'ai ana bikin". Karo na biyu ya ɗago ya sake kallonta. "kuma Daddy ya barta?". "kai dai Yaya babu ruwanka. Ka barta taje tai hidimanta ta dawo". Still yana kallonta yace,"ki shirya ku tafi tare". Tayi saurin kallonsa da cewa,"niii babu inda zanje. Haka kawai na bita Ammi ta dinga cusa ni cikin yaran nan masu shegen ji da kai suna min kallon raini". Ya ƙara
🏠