en magani iri-iri, dama tun washe garin da aka kawo kayan Maijidda ta fesa mata labari wai Yami tasa a kawo mata magungunan da zasu gyarata tun daga sokoto da niger, ita dai haushi ne ya tuƙeta a lokacin saboda taƙi jinin taji ana cewa,"maganin mata ko kuma maganin gyara mace".
Yami ta ware wasu ta zuba a leda tace,"gasu nan ki tafi da su, basu da ɗaci babu bauri babu komai, su zama sune ruwan shanki kinji ko. wannan kuma haɗin zuma ne itama kike sha akai-akai, dan Allah Fillo karki mana asarar kuɗinmu, in kin mayar da hankali kinyi amfani da su kanki kika taimaka".
ita dai Kaka na daga gefe tana jinsu, bata ce komai ba har sai da Yami ta gama sannan tace,"da ki haɗa mata da wannan ruwan tsarkin ko, tunda naji Babuwan tace shima da wuri zata fara amfani da shi".
Yami tace,"kinga kuwa na manta, shi da tace ma ya rage wata biyun zata fara amfani da shi".
nan dai Yami ta haɗa mata duk abinda ya kamata ta kuma yi mata bayani.
wajen biyar da rabi na yamma Hajiya Madina ta kira Fillo tace taje ta ɗauko mayafinta tazo ta rakata anguwa. wata sabuwar shadda da Maama ta ɗinka musu ita da Ɗausiyya ta saka, shaddan ash colour me duhu, an mata ɗinki me kyau ajiki kai ba kace ɗinkawa akayi dan a bawa ƴan aiki ba.
tana zaune a parlo Hajiya Madina ta sauko daga stairs, waya ce riƙe a hannunta suna vedio call da Turaki, tana faɗa masa irin yacca kowa ke missing ɗinsa har Baffa, tana basa labarin Ilham ma jiya ta ke cewa zata biyo shi sai taji cewar baya Hong kong yanzu.
irin yacca suke hirar kamar ba ɗa da uwa ba. Bello a gefensa yace,"Maama ni ba kuyi missing ɗina ba kenan, alhalin ni ke kulawa da shi".
cike da tsokana Maaman tace,"Bello ke kuma wa acikin kayan miya, a'a Hammanmu dai shi muka sani, hatta ƴan aikin gidan nan sunyi kewarsa, yaushe rabon yay nisa damu irin haka, wlh gidan duk ba daɗi".
ta miƙawa Fillo jakar hannunta tana cewa da Turaki,"tom zan fita ne, zanje wajen wannan matar da na faɗa maka nasa ta nema min marayun da za'a ke taimaka musu kullum, to shine zanje naga inda take da zama".
Turaki yace,"ok to Allah ya taimaka ya bada lada, Nihal ce kusa da ke?".
tace,"a'a su duk sun fice ai, ana bikin ƙawar Zaytuna sunje dinner party, ka san Baffanku ba so yake ba shisa nace suje mata da wuri su dawo da wuri, yafi ace basu je ba gaba ɗaya".
Turaki ya sauke numfashi kaɗan yace,"Maama ke ɗaya kuma za ki fita?, ki bari mana gobe sa raka ki".
tace,"ni da Fillo zamu je, bani ɗaya zan tafi ba me Babban suna".
yace,"yauwa hakan yafi ai".
sai kuma ya shafo wuyansa yace,"Maama please ko za ki bata ta kaiwa Salihu(me gadi), akwai saƙo dana bar masa, ina so naji ko yay concluding abin".
ta miƙawa Fillo wayar tace,"kaiwa me gadi da sauri".
Fillo ta miƙe tana ajiye jakar hannunta akan kujera, Hajiya Madina tace,"no tafi da jakar ai yanzu zan fito".
Fillo dai tunda ta amsa wayar ta fito bata kalla screen ɗin ba, tafiyarta kawai take yi shi kuma yana ta kallon fuskarta da ta haska.
ta kaiwa me gadi wayar ta dawo bakin mota tana jiran Maama, wucewar minti biyu sai ga me gadin ya dawo mata da wayar ta karɓa tana kallon screen ɗin, ganinsa yasa ta gaida shi.
ya amsa yana ƙarewa kwalliyarta kallo duk da ba wani kwalliya tai ba, farar powder kawai ta sha sai lip balm. tace,"in mayarwa da Maama wayan?".
yace,"no, i just want to say ki kula da kanki sosai kinji, hakama ki kula min da Maama, karki barta kuyi dare a inda zaku ɗin".
ta amsa da,"to". he have alot to say to her but dole ya taƙaita, at last kawai ya tambayeta,"kina da wata matsala ne". ta girgiza masa kai alamar a'a. shi kuma ya kashe wayar, Fillo tabi wayar da kallo tana jin kamar wani abu a tare da ita na tafiya da katsewar wayar. ta tuna yanda yake kallonta yana tambayar kamar yana magana da matarsa.
ko da suka je gidan Asabe Ƙuli, basu jima acan ba, kan hanyar su ta dawowa Hajiya Madina ta tsayar da driver a ƙofar wani store. a mota ta bar Fillo da Drivern bayan tace mata,"Fillo bari yanzu zan fito kinji. rigar jarirai kawai zan sayo inda muka je ɗin nan ne jikarta ta haihu".
Fillo tace,"tom Maama sai kin dawo". har Hajiya Madina ta fita a motar sai kuma ta dawo ta miƙowa Fillo wayarta tace,"bana son zaman shiru riƙe wayan ko ƙur'ani kya karanta, ko kuma za ki biyoni ne?".
Fillo ta girgiza kanta tace,"a'a Maama sai kin dawo ɗin". ta faɗa tana amsar wayar.
game ɗin da take yawan ganin Maama nayi ita ta shiga, tana cikin yi sai ga kira ya shigo wayar, ganin sunan,"My Husband". na yawo jikin screen ɗin yasa ta fita daga motar tace da drivern bari ta shiga ta kaiwa Maama.
sai da ta fito taji garin so silent, babu ma inuwar mutane dake giftawa, tana shiga ta bawa Hajiya Madina wayar ta fito.
duk da tana hasko motarsu dake tsallake haka ta taho a ɗan tsorace ta tsallaka, sai dai sanda tazo bakin motar ta buɗe ƙofar motar zata shiga taji wani abu mai sanyi a wuyanta, sanyi irin na ƙarfen wuƙa.
da sauri tayi yunƙurin juyawa bayanta jin numfashin mutum akanta, nan da