yau faɗa min kalar fitinar da kika yi".
ta waro ido waje taje,"fitina kuma?, ai ni bana fitina, da hankalina".
ya murmusa kunci sosai yace,"kuka fa?".
sai ta sami kanta da ba shi amsa kai tsaye da cewar,"ai dama kaine kake sa ni kukan, kuma baka nan".
yace,"really?". tace,"yeah".
leɓensa ya tale da murmushin da bai shiryawa ba yace,"magani fa?". ta cune fuska tace,"wannan ma ai kaine kake min dole, kuma da baka nan duk bana sha".
yace,"abinci fa?". ta juya idonta tana jin baccin na ƙara zuwa tace,"ina ci mana". ta faɗa tana ɗan shagwaɓe fuska.
Turaki yay shiru bai ƙara cewa komai ba, tsawon 30seconds kallon siraran yatsunta kawai yake da ta tallafe haɓarta da shi.
sanda ya buɗe baki zai ƙara yin magana sai ta riga shi da cewar,"yaushe zaku dawo, Maama duk ta damu".
yace,"ba yanzu ba sai next year". jin hakan bata san sanda ta ɗago ido ta kalle shi ba ta maimaita abinda yace,"next year kuma?".
ya ɗaga mata gira,"yes, Maama zata zo idan tana son ganina, also Zaytun. ko bayan su akwai wanda ya damu da rashina ne?".
tayi shiru bata ce komai ba duk da tana so tace wani abu ɗin.
Turaki yace,"oya kashe wayan, dare yayi Kaka na can na jiranki". ta ɗan kalle shi tace,"to naga duk ka rame, baka da lafiya ne?, ko wani abu yana damunka?".
yace,"lafiyata lau, ina dai kewar Mum ne".
tace,"wacece haka?". ta tambaya as if bata san komai ba.
yace,"Yayar Maama ce, ta daɗe da ɓata bamu ganta ba har yanzu, ki tayamu da adu'a Allah yasa mu ganta very soon. ko idan na dawo za ki taimaka min mu nemota?".
yanayin yacca voice ɗinsa ya fito sai taji tausayinsa sosai, tace,"ka san inda za'a ganta ne?".
yace,"a'a, kawai dai jikina na bani kamar ke za ki ga inda take". tace,"sai dai na tayaku da adu'a, amma ni ban san aina zan ganta ba".
yace,"adu'an ma mun gode. bye". da sauri tace,"da gaske sai next year?". ta tambaya tana tsare shi da ido. sai taga kamar yayi murmushi sannan ya ɗaga girarsa alamar ehh. ta sake cewa,"to kana kula da kanka?". ya girgiza mata kai alamun a'a ba tare da yay magana ba.
tai ajiyar zuciya kamar zata ce wani abu sai ta fasa, haka ɗaya take jin bata so ya yanke kiran, haka ɗaya take ji kamar idan ya kashe wayar shikenan ba zata ƙara ganinsa ba, hakama kamar ba zata ƙara jin voice ɗinsa ba.
ya katse shirun nata da faɗin,"kin daina jin baccin?". ta ɗaga kanta,"ehh ya tafi. ba zaka jira Adda Zaytuna ɗin ta fito ba?". ya girgiza mata kai baice komai ba. tace,"tom shi abokinka ɗin da kuka tafi tare fa?".
yace,"ba sa wayar zanyi?".
ta tura baki gaba tace,"ince masa me?, tambaya nayi ko yana kula da kai".
Turaki na murmushin leɓe yace,"ai ba wanda ya biyasa kuɗin kula da ni. shima ta kansa yake".
tace,"to magani fa?". yace,"haka kawai ake shan magani da ma?". tace,"ai kai baka da lafiya".
daga ita har shi ba wanda ya ƙara cewa komai, tana ta gyangyaɗi riƙe da waya yana kallonta, ƙarshe sai kashe wayar yayi ganin kaman tayi nisa a gyangyanɗin. Zaytuna na fitowa ta sameta akan gadon ta ɓingile tana bacci riƙe da waya a hannu, ta tasheta ta gyara kwanciyarta akan gadon.
washe gari Fillo dai bayan sun gama aiki, leeson teacher nasu ya tafi ta kama hannun Ɗausiyya tayi mata rakiya ɓangarensu.
tana shiga ta faɗa jikin Kaka ta rungumeta cike da murna, Kaka tace,"ai ce nake kin koma can gaba ɗaya?".
Kaka tayi maganar itama cike da jin murnar ganinta, kamar sun shekara basu ga juna ba.
Maijidda ta kama hannunta ta jata zuwa cikin ɗaki tana cewa,"yarinya zo kiga kayanki. wallah sunyi kyau harda irin shaddar ƴar gidan Mamu aciki".
Fillo dai tunda ta zauna gaban ƴar ƙaramar akwatin, kallon yacce Ɗausiyya da Maijidda ke aikin fito da kaya kawai takeyi. ita dai ji take kamar bata murna bata farin ciki da ganin kayan, kuma kamar tana farinciki ta dai rasa taƙamemen abinda take ji ɗin.
har la'asar suna zaune, Maijidda da Zakiyya itama Jikar Yami da tazo hutu har Ɗausiyya suna ta tsara abubuwan da zasu yi lokacin biki. Zakiyya na cewa,"ke Fillo kike cewa ai kar a fara shiri yanzu, lallai baki san halin lokaci ba. to wallah yanzu za kiga wata biyun tayi, gwara duk abinda kika san zaki yi ki fara shi tun lokaci bai ƙure miki ba".
Maijidda ta janyo Fillo jikinta ta raɗa mata abu a kunne tana dariya, Fillo tayi tsaki tana tureta. Maijidda suka tafa ita da Zakiyya suna tsokanar Fillo da cewar,"an matan Amir an kusa shiga sahun manya". Fillo dai babu wanda tanka.
Yami ta shigo ta ƙwalawa Fillo kira ta fito, tazo ta durƙusa tana gaida Yamin, itama Yami na tsokanarta da cewar ai tayi zaton kunyar ba zata ƙara barinta shigowa ba har ai auren.
kunya ta ƙara kama Fillo, Yami ta miƙa mata robar wani magani tace,"shanye wannan yanzu". ta karɓa ta shanye da ƙyar duk ba wani rashin daɗi ne da shi ba.
sannan Yami ta ƙara ce mata,"kun gama jarabawar?". tace,"za dai mu fara Yami". tace,"to za ki ke samun shigowa kullum ko na haɗa miki magungunan ki tafi da su?".
tai shiru bata ce komai ba tana kallon tulin wasu takarc