n ita Ɗausiyya na cika mai a suyar, ita kuma Fillo na zuba kaɗan, faɗan dai ya tashi akan kowacce ta sakawa ƴar uwarta ido, Zaytuna da Nihal kuma na gefe suna haɗa miyar agusi da ganda, suna jinsu suna yi musu dariya.
Nihal ta waigo ɗauke da dariya a fuskarta tana kallon Ɗausiyya tace,"ke fa kece aikinki baya kyau, mai idan yay yawa a abinci baya daɗi Ɗausiyya kuma kin san dai akwai masu ulcer".
Fillo na kallon Ɗausiyya tai dariya tace,"ah tou kin dai ji, in kuma man kike so ai sai ki bari in tazo ƙarshe ki soya taki da duka galand ɗin, lafiyarki ai ba lafiyar wani ba".
Ɗausiyya ta galla mata harara ta ɗauki waina guda ɗaya acikin wacca Fillon ta soya ta wuce wurin Nihal tana faɗin,"Adda Nihal kalla fa ki gani, abu ƙamas ai sai taja mana magana ace muna da maƙon mai alhalin akwai wadatarsa". ta buɗe cikin wainar tana ƙara faɗin,"ji fa aba a bushe kamar ba'a saka komai ba, yanzu dan Allah cikin abokan Baffa wani ya kai bakinsa ai direta zai yi dan wannan dai ba zata ciyu ba Allah".
Nihal na taɓa wainar tace,"gaskiya kuma fa haka ne, mutane da basa rasa abin faɗa sai su tafi suna cewa Baffa baya wadata gidansa da isassan man abinci".
Ɗausiyya ta kalla yanda Fillo ta cika tai fam tace,"ah tou, dan haka ki zuba mai isashshe kiyi suya Malama, in yaso kyayi tsumulmularsa a gidanki babu ruwan koya, ƙarƙari kijawa mijinki magana wurin abokai da dangina a tafi ana yi da ke biki iya girki ba".
tai ƙarashen maganar tana dariya. Fillo tace,"ko ba komai dai mijina yace ina da tattali, ke kuwa kullum sai kinsha masifa akan haukar almubazzaranci da kike masa".
Zaytuna tai dariya sosai. Nihal da bata fiya shigowa kitchen ɗin ba tace,"haka kuke aikin dama kamar kaji?".
har sannan dariya bai ɗauke akan fuskar Zaytuna ba tace,"kika biye su ba abinda zai hana bakinki yagewa, dan kamin barinki kitchen ɗinn sai kin ji wani complain ɗin na daban".
dai-dai nan Hajiya Madina ta shigo, duk suka yi shiru, ta dubi Zaytuna da Nihal tace,"sannunku da aiki". suka amsa da yauwa, tace da su,"where is Samha?". Nihal tace,"na ga ƙawarta tazo ɗazu sun fita".
Maama bata tace komai ba ta maida kallonta ga Fillo tace,"meet me in my room". ta faɗi hakan tana juyawa ta fita.
Fillo ta miƙe tana wanke hannu a sink, taiwa Ɗausiyya gwalo tace,"kuma ai aiki me kyau in ba haka ba ran mutum ya ɓaci". ta faɗa tana mata gwalo sannan ta fice daga room ɗin.
tun da ta shiga room ɗin Hajiya Madina taga yanayin fuskarta sai jikinta yay sanyi, ta ƙarasa shigowa ta zauna a ƙasa tana fuskantarta, duk lokacin da taga fuskar Maama ahaka tasan to da matsala,so farkon abinda yazo cikin kanta shine Turaki, 4days dama taji Zaytuna na faɗin zai yi, ga shi yau har kwana 5, lafiya?, meke faruwa?, ko kuma yana kan hanya?.
rashin sanin amsa yasa ta ɗago kai da sauri ta kalli Hajiya Madina da ke ta kallonta ta kasa cewa komai. murya a hankali tace,"Maama lafiya?, Hamman har yau bai dawo ba".
Hajiya Madina ta sauke numfashi tace,"zasu taho jiya sai Baffa ya tura su El-Salvador zasu yi signing wani contract da wani kamfanin fulawa acan, jibi insha'Allahu zasu sauka".
Fillo tace,"Allah ya kaimu ya dawo da su lafiya".
ta faɗa kanta na ƙasa. Hajiya Madina na studying nata tace,"kunyi da wani zai zo wurinki ne?".
tambayar taji ta a wani iri, hakan yasa tai saurin ɗago kai tana kallon Maaman, kan tai magana Hajiya Madina ta jefa mata tambayar,"Amir yazo wajena yace min yana son ganinki. waye shi?, aina ku ka haɗu?, dama can ya sanki ne?, da yaushe kika fita har ya ganki ya biyo sawunki?".
Fillo ta sadda kanta ƙasa tana wasa da fingers dinta tace,"wanda zan aura ne, amma wallahi ba muyi da shi cewar zai zo ba yau".
with Astonishment Maama tace,"wanda za ki aura Fillo, asin how?".
Fillo ta kwashe duk bayanin komai har kayan sa ranar da aka kawo ta faɗawa Hajiya Madina. ita dai kallonta kawai take tana ganin kamar yarinyar ƙarya take yi, ƙarama da ita haka age of 17 going to 18 ace za'ai mata aure?, tasan cewar su ƴan ƙauye ne da basu fiya bawa rayuwar ƴa mace muhimmanci akan yanda zamanin yanzu ke tafiya ba, amma bata taɓa tsammanin za'a iya aurar da yarinyar nan kusa ba kasancewarta me ƙaramin jiki sosai, in ba sani ma kayi ba zaka iya rantsewa ba 18 zata shiga ba.
dalilin da yasa tun a ranar da yarinyar ta kwanta mata a rai ba tayi hanzarin shigar da tata buƙatar garesu ba kenan, kiwon Fillo da take yi tanadi ne take taiwa ɗanta Muhammad Turaki, ashe har wasu sun mata shigar sauri, wani ya riga ɗanta, wani daban zai mallaki kamilar yarinya me natsuwa da hankalin da irinta ke da wuyar samu, ba ɗanta Muhammad Turaki ba, wani daban can. yanzu wa zata ƙara kama masa?, har cikin ranta bata ji daɗin wannan batun ba sam, to amma ya zata yi, shirinta da lissafinta daban ne, hakama yanda ubangiji ya shirya lamarinsa daban, kuma na ubangiji shine dai-dai, kuma dama ita kullum adu'arta alkhairi take nema.
dan haka yanzu adu'a ta rage mata akan Allah yaywa Turaki da Khalil zaɓin mace ma