kika kalla nayi".
Ɗausiyya tace,"ai ina kallonki sanda kika zube, har nayo wajen naji ana batun maciji babu shiri nayo reverse".
Fillo na ƙara harararta sanda take zama kan gadonsu tace,"ashe kema matsoraciyar ce".
Ɗausiyya tayi dariya tukunna tace,"2days kina makarar shigowa".
Fillo na kwanciya kan gadon tace,"wani lalataccen barci nake fama da shi 2days ɗin, in kuma kina da magani sammani".
tai maganar tana jin jikinta a saɓule, yanayinta duk babu daɗi kamar wani abu na shirin faruwa mara kyau.
Ɗausiyya tace,"aiko dai ki nemi magani. ɗazu da Hammah Babba zai wuce yana cewa da Adda Zaytuna wai in yaje can wurin da zai je zai sayo mata maganin daina bacci, da kina nan kema da kin faɗa masa tunda naga yana da kirki, kawai dai baida sakin fuska, jiya ma 2k ya ban".
lokaci ɗaya Fillo taji allon ƙirjinta ya girgiza, Turaki ya tafi?, when is he coming back?, tare da Bello suka tafi, ta ya zai iya kula da kansa?, ya tafi da maganinsa?.
tarin tambayoyin da suka zowa cikin kanta kenan a lokacin, ga shi babu ɗaya da take da amsarta, dan haka ido kawai ta lumshe kamar me bacci, tana jin Ɗausiyya nata magana amma bata jin zata iya buɗe baki ta amsa mata saboda faɗuwar gaban da take ji, wani irin yanayi da bata taɓa jin kanta aciki ba, like kamar dai something bad will happen soon.
bayan kwana biyu aka kawo akwatin sa ranar auren Fillo daga gidan su Amir, Innarsa da wasu Anties nasa guda biyu na ɓangaren mahaifi sune suka kawo, akwaiti guda ɗaya da atamfa 4 aciki sai less da zai kai 6k guda biyu, shadda ɗaya da material guda ɗaya, da fashion na yari da sarƙa guda biyu sai takalmi da jaka duk guda ɗaya, sai kuma hijabs har ƙasa guda biyar da 5k a haɗe, akasa ranar aure wata biyu masu zuwa.
kaya dai masha'Allah sunyi kyau sosai gwanin san barka, kowa ya gani sai ya yaba, haka akaita zuwa ana gani ana tafiya da masha'Allah, su Yami kam baki har kunne jikarsu tayi goshi.
sai dai fa duk wannan bidiri da akeyi Fillo bata ko ga tayar akwatin ba balle kayan da suke ciki, dan ƙememe tun ranar da Turaki ya tafi ta kasa zuwa ɓangarensu tsaboda bala'in tsoron dake ranta, kayan sawarta ma sai Maijidda ce ta kawo mata tace musu wai jarabawa za'ai musu, kwana suke suna karatu ita da Ɗausiyya shisa.
farko dai a tsorace take da zuwan, to amma da aka kawo kayan sai tsoro ya haɗe da kunya shisa ta kasa ko da zuwa, idan taje bata san taya zata fara haɗa ido da mutane ba, tasan kuma halin Maijidda zata sata a gaba ne da aikin zolaya, dama tun washe gari ma tazo tana mata lissafin abubuwan da zasu yi da biki, ita dai har ta ƙaraci surutunta bata ce mata ƙala ba, Maijidda ma da haushi ya cikata ta karɓi wayar Yami da ta zo amsa tai wucewarta da cewar bata ƙara zuwa, ita zata je tayi nata shirin ita ɗaya.
tun ranar da aka kawo kayan Amir ke ta doka mata kira akan zai zo, tai masa godiyar kaya har yake tambayarta ko sunyi, tace masa sunyi tunda har Maijidda ta faɗa dan ita bata je ta gani ba. Amir dai juyin duniya yazo yaga Fillo sam taƙi, idan tayi kamar tace masa yazo sai taji inaa a dai yi auren tukunna, ai haka taji Turaki yace duk masu yin zance a gidan, shisa ga ƙannensa nan cikinsu babu wadda ke yin zance ashe dalilin kenan, Amir tun yana lallashi da roƙo da ƴar murya Fillo dai taƙi yarda da zuwansa, har yay fushi ma washe garin ranar gaba ɗaya bai kirata ba, kuma sai sauƙi yazo mata ranar Yami ta aiko Maijidda ta karɓar mata wayarta.
kuma da Hajiya Madina tayi mata batun me yasa bata zuwa wurin Kaka sai tai mata ƙaryar ai tayi tafiya ne, sai dai fa a wannan kwanaki biyun Fillo tayi muguwar rama, tun daga kan fuskarta har jikinta, na farko tsoro ya hanata sukuni, na biyu kuma kewar Kaka duk ta addabeta.
ɓangaren Amir dai da yaga ba zai iya da azabtuwar rashin ganin Fillo ba ya kwaso ƙafa yazo gidan, ya sanarwa me gadi cewar wurin Hajiya Madina yazo saboda ya sami damar shiga cikin gidan kai tsaye, ta yanda zai zaƙulo Fillo a duk inda take ya fito da ita, shi ba zai iya da rashin ganinta ba, yana ƙara kwana bai sata a idonsa ba tsab zai iya rasa ransa. Mai gadi ya sanar ma da Hajiya Madina, akayi masa iso zuwa parlon baƙi, taje ta same shi suka gaisa, zatonta ma ko masu buƙatar taimako ne amma sai taji yana mata bayanin wurin Halima yazo.
kusan minti guda Hajiya Madina ta ɗauka tana kallonsa cike da nazarinsa, tare da kuma mamaki matuƙa akan batun wurin wacca yazo, ashe yanda take tunanin Fillo ba haka take ba?. tashi tai tana ce masa ya jira yanzu zata zo, aka kawo masa ruwa da snacks da kuma juice na pineapple, kayan dai na aje kan table ɗin dake gabansa yana kallonsu amma ya kasa ko taɓa ruwan, bini bini sai ya duba agogon hannunsa, shiru shiru Fillo bata fito ba wucewar mintina goma da tafiyar Hajiya Madina, a ransa sai ya fara tunanin kamar ko ba zata zo ba ne, kuma kamar Hajiyar ce ba zata barta ba, sai yaji ransa yay mugun ɓaci.
ɓangaren Fillo kuwa suna can suna aikin suyar wainar shinkafa Baffa zai yi baƙi, suna faɗansu ita da Ɗausiyya ka