NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 133 of 323

e kawai, ni bana son kuka yana ɗaga min hankali". Khalil wanda zai driving nasu yace,"Allah babu da wadda zan tafi da ita, ina sauke su nima da inda zanje". Boɗejo na hararsa tace,"kana kama da mutanen kirki amma ba haka kake ba, in motar kai ka saya sai ka hanasu shiga ai". Khalil dai ya tubure babu me binsa, har sai da Hajiya Madina tasa baki, amma hakan bai sa ya yarda sun tafi da kowa ba. ƙarfe tara Fillo ta tashi, ta tashi a firgice tana bin ɗakin da kallo, ta sauko daga kan gadon da sauri tana rarrabawa idanuwa. har yanzu babu alamar ya shigo, to taya zata fita daga ɗakin alhalin yasa key?. tana ta ɓata rai ta shiga gyara ɗakin, tana gyaran gado taci karo da farar takarda a ninke, ta ɗauke ta aje kan side drower sai kuma taji tana buƙatar buɗewa, bata san ba ko yana da alaƙa da mugwayen mutanencen. ta zauna gefen gadon ta warware takardan, farkon abinda ya fara burgeta handwritting ɗin jiki, sai kuma zanen heart da peppern ke ɗauke da shi. sannan tabi rubutun da kallo tana karantawa acikin yaran fulatancin da aka rubuta. _Nisa tsakanin zuƙata biyu ba ya nufin shinge fa ce tuna kyakykyawar alaƙa dake tsakani...ƙwarai akwai wanda yake ƙaunarki kwatankwacin yadda makaho ke buƙatar ido, fiye da yadda kurma ke buƙatar ji, fiye da yadda gurgu ke buƙatar ƙafa, Dai-dai da yadda mara lafiya ke buƙatar lafiya, cikin ƙanƙanen lokaci yana jin kin zama rayuwarsa gaba ɗaya, kula da kanki shine mafi abinda yafi so daga gareki kiyi masa a sanda yay nisa dake, amana!, amana!, amanar kanki a tafin hannunki daga gare shi._ haka siddan Ilham ta faɗo cikin zuciyarta a sanda ta gama karantawa, ba wai don ta santa ba ko tasan matsayinta, tana hasko hoton yanda ta same su jiya a ɗakin Boɗejo. ta taɓe baki ta miƙe tana jefar da takardar a ƙasa, tabi ta kanta ta wuce ta gyara kan table ɗin dake hargitse da takardunsa, tana gyaran ɗakin tana kumbura ba tare da sanin dalili ba, kuma har ta gama gyaran bata bi ta kan gadon da ta soma gyarawa ba, saboda haka ɗaya taji gyarasa baida wani amfani duk da ita ta kwanta akai. tana riƙe da kwanukan abinci a hannunta taji an turo ƙofar ɗakin an shigo, idonta ya manne akan Ilham dake shigowa kamar wacca ƙwai ya fashe mata a ciki, fuskarta duk hawaye, ta shigo ba ko sallama ta wuce ta gaban Fillo ta faɗa kan gado tana ɗauko pillow ta rungume a ƙirjinta. wani abu da Fillo bata san ko menene ba ya tokare mata a maƙoshi, tasa kai ta fice a ɗakin da sauri. _ba fa kwa yin comment, kar kusa nai zuciya na dire typing ɗin._ *vote, comment and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Avoid error mistakes._ *31* wani abu da Fillo ke ji akan Ilham ya tsaya mata a ƙirji kamar ƙurji, har ta baro upstairs ɗin wani irin ɗaci take ji a tare da ita da bata san dalilinsa ba. lokacin da ta fito compound zata wuce ɓangarensu ta tarar ana rage flowers ɗin gidan, wajen duk yay kaca-kaca, tausayin masu aikin cirewar da gyara wurin ya kamata, neman halal da wuya, kuma a haka namiji ke fita yasha wahala ya kawo macen da bata arziƙi ba tayi masa ɗiban albarka, ta girgiza kai tana me jin tausayin kowanne namiji acikin ranta amma banda Hayyo mahaifinta. sai da taje gab da shiga gate ɗin nasu kawai maganar macijin jiya ta dawo sabuwa acikin kanta, take kuma tsananin tsoro ya rufeta ganin wani reshe na flower da aka sare wada yay kama da jikin macijin, ba shiri ta kurma uban ihu tana duƙewa a wajen sai kururuwa take, da sauri masu aikin suka yo kanta suna tambayar lafiya, dai-dai nan Khalil ya ƙaraso wajen shima yana duƙawa gabanta da tambayar lafiya. cikin kukan da take tace,"maciji ne". with suprise kowa ya ƙara maimaita abinda tace,"maciji kuma?". ta ɗaga kanta jikinta sai rawa yake yi. nan da nan masu aikin suka shiga laluben wajen, Khalil kuma yace ta tashi sai ta girgiza masa kanta tace,"ba zan iya ba". yace,"kin gurɗe ne?". ta ƙara girgiza masa kai ba tare da tace komai ba. yana murmushi yace,"daure ki tashi babu komai anan, macijin ai ya tafi ga shi can sun kashe shi". tun ɗazu da ta duƙe sai a yanzu ta ɗago da kanta tana rarraba idanuwa, yacca take yi ɗin ba ƙaramin bawa Khalil dariya tayi ba. bai kasa riƙe dariyarsa ba ya saki yana ce mata,"tashi na raka ki". ya faɗa saboda yanda yaga duk ta firgice, firgicewar da ba zata iya tafiya ita ɗaya ba. ta miƙe da ƙyar sai ƙanƙame ƙafarta da jikinta takeyi, ya wuce gaba yana cewa,"muje". idonta ya sauka cikin compound ɗin nasu, maganar Turaki ta cewar ai wadda ma macijin ya maƙale mata mutuwa tayi, sai taji inaa ba zata taɓa iya shiga ɓangarensu ba, tana jin ma kamar sai dai Kaka ta dawo nan itama. ba shiri taja da baya tace da Khalil,"Hammah Khalil ba nan zani ba ɗakinmu zan wuce". tana tafe tana ɗage ƙafafu haka ya rakata har ƙofar ɗakinsu, zaune ta sami Ɗausiyya na gyaran zogale, ganin Fillo yasa Ɗausiyyan ƙyalƙyalewa da dariya tace,"matsoraciyar kawai". Fillo na hararta tace,"tsoro ai halal ne, kuma tsoron me
🏠