NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 132 of 323

yi sam baya son yaje, dan ba shi da yanda zai yi tunda Maama tace yaje ɗin, amma ji yake kamar in yafi wani abun zai faru, kamar tafiyar tasa zai sa ya rasa ɓarin jikinsa. Fillo dai da asuban bayan fitar Turaki masallaci ba daɗewa ta tashi, taga ita kaɗai ce a ɗakin, cikin ranta ta ƙara yabon kyan hali irin na Turaki, watakam bai ma iya kwana the same room da ita ba, ta sauko a gadon tana tafiya a hankali saɗaf saɗaf saboda har sannan tsoron daren jiya bai barta ba, abinda ta fara tunawa ma kenan da ta buɗe idonta, maciji a compound da kuma bakin gate, yo ita kuwa me zai sake tsayar da ita a wannan wurin, ai har mutuwa. a rufe taji ƙofan sanda taje buɗewa, ta ɓata fuska ta dawo ciki ta shiga toilet tayi alwala ta fito, tana idar da sallah ana ɗauke wuta, hakan yasa a sukwane ta koma kan gadon ta kwanta tana ƙudundunewa tana adu'a a fili, har bacci ya ɗauketa. Turaki ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, darduman sallah kawai ya kalla ya shaida tayi sallah ta koma ta kwanta, a yanayin kwanciyar kuma yasan tsoron jiya dai har yanzu bai barta ba. kayansa ya cire ya shiga yay wanka, komai a hankali yake yinsa gudun kar ya tasheta, 7:30am ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya da bai cika sasu ba, ya ɗauka brief case daidai nan Zaytuna ta shigo ɗakin. duk da ita tasan Fillo matar Turaki ce hakan bai hanata jin kunya ba da ta shigo ta tarar da shi yana kissing forehead ɗinta. sai ta tsaya ɗaga bakin ƙofan tace,"B Ƙaraye yazo". ta faɗa tana murmushi. ya ƙaraso gabanta ya kama kumatunta yace,"ki zage ki dinƙa faɗar sunansa Bello, dan shi gatsal yake faɗar Zaytun a gabana". tasa hannu ta rufe fuska tace,"ai ni baya faɗa a gabana". Turaki yay murmushi yay mata side hug yace,"ki kula min da kanku, mussaman waccen fitinanniyar, dan Allah kisa ido akanta sosai kin riga dai kin san bata ji, sanya kai a hatsari shi yafi komai sauƙi a wurinta. ki faɗawa Kaka zata dawo wajenki da zama for some days dan na riga na tsoratata ba lallai ne take iya zaryan zuwa side ɗinsu da nan ba. ki sa ido akan fitarta, bata son cin abinci, bata son shan magani, na baki amanarta na baki amanar Maama na kuma baki amanar kanki, just 4days zanyi in dawo". ya ƙarasa faɗa Zaytuna ta rungume shi. cikin kukan da take yi tace masa,"jiya nayi mafarki Mum ta dawo, ta dawo hannunta da ƙafarta duk ciwo". ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"ta kusa dawowa da izinin Allah, ina dawowa zamu nemota ni da Fulani". a sanyaye tace,"Hammah bana tunanin Mum na raye". yace,"yaro ma na riga babba mutuwa, so shekaru ba sune mutuwar mutum ba, gamu da Maama har yanzu a raye, kisa a ranki Mum ta kusa dawowa garemu da ranta da lafiyarta, zan faɗawa Fulani issue ɗin da zarar na dawo". kiran wayar Bello da ya shigo a karo na kusan huɗu yasa shi sakinta yana waiga yana daɗa kallon Fillo. ji yake kamar kar ya tafi, ya kama hannun Zaytun suka fita yana faɗa mata,"idan kinje wurin Kaka ki ɗauko cream ɗin da ta ke shafawa ki jefar, i don't think wanda kika saya ranar nan take shafawa". Zaytuna tace,"tayi haske sosai ko?, nayi zaton ma wanda na sayo mata ne so after na tambayeta tace min bata fara using da shi ba, tana shafa wani da aka kawo musu, Kaka ta hanata buɗe sabon wai almubazzaranci, but zanje ɗin sai na ɗauke". suka fito compound ɗin Bello dai na tsaye sai hararsa yake, Turaki ma ya hararesa ya ƙarasa wurin Maama, sallama dai kamar kar ai tafiyar, kuma kamar wannan ne karo na farko da zai fara tafiya, Nihal ma ta dage cewar ita dai zata bisa, yace sunyi late ai da tun jiya ta faɗa masa sai a anso tictiket har ita, Samha ma ta riƙesa tana faɗin kawai ba sai ya tafi ba ita bata so yana nisa da su, Hajiya Madina ta zabga mata harara tana me jin wani ɗaci da baƙin ciki na kasancewar Samha ƴarta. Ilham kam da ta kwana a gidan tana riƙe da hannun Boɗejo tana goge hawaye. Boɗejo tace,"ni wallahi duk kun saka jikina yayi sanyi, tafiya sai kace yau zai fara, ko saboda kawai ya jima bai yi nesa daku ba?. fisabilillahi irin wannan sallamar da kuke yi ai ta masu bankwana da juna ce, irin fa wannan sallamar akeyi idan mutum zai mutu. to ni dai gaskiya idan tafiyar nan bata zama dole ba ke Madina sai kisa shi ya haƙura". ta kalla Hajiya Madina taga tana goge hawaye tace,"ka ga wani ƙarin tsinkar da zuciya kuma". Turaki dai yana tsaye jikinsa duk yay sanyi, shima ji yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, sai kallon side ɗinsu yake yi, kamar zai ga Fillo ta leƙo ta window, kamar zata leƙo suyi sallama. ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan Ilham, ta ɗago tana goge hawaye ta tafi zuwa gabansa, ya ɗauke hannunta daga fuskarta yana sa handky ɗinsa ya goge mata fuskar, a hankali yace,"kukan mene?". tace,"nace zan bika tun jiya". yay murmushi yace,"4days fa kawai zanyi na dawo". ya faɗa yana ɗago kai ya kalla Nihal yace,"auta zo". tazo itama nata hawayen na sauka a lokacin. yace,"ku shiga kuyi min rakiya to". Boɗejo tace,"kaga in ɗaukowa Ilham mayafinta ku tafi tar
🏠