na deemlight. ya matsa tare da ɗago Fillo dan gyara mata kwanciyarta, amma sai yaji cewar ba hakan ya kamata yay ba, ya rufe ido yana cije fuska sannan ya ɗagota gaba ɗaya ya kwantar da ita a jikinsa. dai-dai nan ya ƙara hasken light yana ƙarewa innocent face ɗinta kallo, hawaye duk ya bushe akan fuskar, ta tsuke fuskan kaman wadda za tai dambe, ga zufa da ta ke haɗawa kaman an watsa mata ruwa.
shi jikinsa ba me son sanyi bane dalilin da yasa bai fiya zama da Ac ba kenan, amma haka dole ya sauka yaje ya kunna Ac sannan ya dawo again ya ɗagota zuwa jikinsa ya kwantar, da hannunsa ya dinga goge mata zufar dake kan fuskarta yana jin zuciyarsa na matsewa da zafi zafi.
sai yay hugging ɗinta tightly a jikinsa kanta na mannewa a chest ɗinsa, wani irin baƙon al'amari yake ji tare da shi, gefen fuskarsa ya haɗe da tata fuskar, ya kamo hannunta a hankali ya riƙe cikin nasa.
ya bayar da sadakinta amma yau sai yake jin like he can't believe cewa wannan jaririyar mallakinsa ce, halalinsa, his wife, his only wife da ya gama tsarin rayuwarsa cewar da mace ɗaya zai rayu, ba tare da sanin cewar itan bace, ba kuma tare da ya taɓa lissafin cewa zai rayu da irinta ba ma, is he dreaming?.
sai yaji wani abu me kama da farin ciki a tare da shi, ya ɗago da fuskarsa akan tata yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, yana jin kwantaccen sajenta na burge shi, ɗaya hannun kuma na cikin nata hannun yana murzawa.
maganganun da ta faɗa masa a mota ɗazu suka haska acikin kansa,_"ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?"._
ya ɗora goshinsa kan nata yake cewa,"ban taɓa jin na tsani wani mutum ba balle kuma ke da kika taimake ni, kuma ta ya zan karya siririn hannun da nake kallo yana burgeni?, wannan bakin kuma ban san zai fashe ba Allah, but am so sorry, shinenan?".
maganganun yake yi kamar tana jinsa.
and for the very first time he felt her in his blood, he felt as if his life depended on her, ajikinsa yake jin kamar she needed him at this time, kamar ya fasa yin tafiyar just becouse of her, duk wannan faɗuwar gaban da yake ji akan zai yi nisa da ita ne, abinda bai taɓa ji ba tsayin rayuwarsa ko da akan Maama da Zaytuna da baya so yay nesa da su.
A hankali ya kai fuskarsa daidai tata yana daɗa ƙarewa ramammar fuskarta kallo, fuskar rigima, fuskar kasada, sai yay murmushi yana kai babban finger nasa kan lips ɗinta yana shafawa.
Fillo dai kamar matacciya, baccinta kawai take yi. Turaki still holding her hands da ɗayan hannun kuma yana shafa lips ɗinta yake ta kallon lumsassun idanunta, zai iya rantsewa bai san time ɗin da wani fitinannan murmushi ya ƙwace masa a fuska ba, ya lumshe idanu tare da ƙoƙarin kai lips ɗinsa saman nata trying to kiss her sai kawai yaji zuciyarsa na faɗa masa,"not now, not today, but one day, in that special night, the night that will come not once, but for your entire life".
ya rumtse idonsa sosai tare da jan wani wawiyan ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗago kansa yana kwantar kansa a pillow, ita kuma ya daɗa gyara mata kwaciyarta ajikinsa tare da jan blanket ya rufesu, sai shafa gashin kanta yake yi, duk shafa ɗaya sai yaji zuciyarsa ta buga, haka har ɓarawon bacci ya ɗauke shi.
sai gab da asuba Turaki ya farka, yana tashi yay alwala yay raka'atanil fajr sannan ya wuce masallaci saboda ya makara, ko da ya dawo masallaci side ɗin Maama ya wuce, ya shiga bedroom nata ya sameta ta idar da sallah tana lazimi, anan ya zauna har ta idar suka shafa aduan tare, lokacin 6 har tayi.
gabanta ya zauna ta ɗora hannunta saman kansa, ta dinƙa jero adu'oi tana tofa masa tana hawaye, har sanda ta ɗauki kusan minti 7 a haka sannan ta ƙarashe da faɗin,"Allah ya kai mun ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare min kai, dan Allah ka riƙe ibadarka, kar kayi wasa da azkar da adu'a. Bello yace ƙilan zaku iya kaiwa har 7days, but bana jin hakan zai yiwu, in ya wuce 4days ɗin ko ka taho ko na biyoku, Allah ya tsareku".
Turaki ya amsa da amin yana me ɗago da kansa, ganinta tana hawaye hankalinsa yay mugun tashi. "Maama lafiya?, menene?, in ba kya so naje na haƙura kawai, Bello zai iya komai shi ɗaya and beside zai sami Sameer acan".
ta girgiza masa kai da cewar,"a'a ku tafi tare, Sameer ai ya dawo jiya, yace yaje room ɗinka time kayi bacci".
Turaki ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya rungumo Maama shima hawayen na sakko masa, ya tsani tafiyar nan da zai