NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 130 of 323

jikinsa duka. he took a deep breath hugging her more, yasa hannu yana shafa sumar kanta a hankali ya kasa cewa komai. kusan 3minutes yana jin yanda heart ɗinta ke beating fast, a hankali yace"menene?, me ya tsorata ki?, kiyi shiru babu komai, am with you". ya furta cikin sigar rarrashi yana riƙe da hannunta guda. acikin fizgar numfashi tace,"Maciji ne". yace,"aina?". ta daɗa shigewa jikinsa sosai tace,"a ƙafata, ka kore shi please, gashi nan zai shige jikina". tai maganar duk a ruɗe tana daɗa ƙanƙamesa. ya sauke numfashin yana murza tafin hannunta murya can ƙasa yace,"babu wani maciji fa, buɗe idonki ki gani". ta girgiza kanta dake kan cikinsa tace,"a'a akwai, kai ne ka faɗa". yace,"to aini waya nake yi". ta ƙara girgiza kanta, yayinda Turaki ke rufe idonsa yana jin wani iri a jikinsa. tace,"ai sanda ka faɗa shine sai na jisa a jikina". ba tare da ya buɗe idonsa ba yace,"to ai ya tafi, buɗe idon ki gani babu komai, na kore shi". tace,"to ka kunna light". yace,"a kunne yake". ta buɗe idonta a hankali hasken ɗakin na shigewa cikin idonta, sannan ta zare jikinta daga nasa tana jin yanda gabanta ke faɗuwa har sannan, hannuwanta sai kyarma suke yi. Turaki yay saurin sauka akan gadon ya buɗe ƙofa ya fita, for few minutes sai gashi ya dawo da cup a hannunsa ɗauke da ruwa aciki me sanyi. har sannan Fillo na takure akan gadon waje ɗaya sai raba idanuwa take yi, motsi kaɗan take jira ta kurma ihu, ya ƙaraso gaban gadon fuska babu yabo babu fallasa, ya miƙa mata cup ɗin, ta kallesa ta kalli transparent glass cup ɗin a hankali tace,"dan Allah...". bai barta ta ƙarasa ba yace,"amsa Malama ruwa ne". ta ɗaga hannuwanta da har lokacin kyarma suke yi ta karɓa tasha sannan ta miƙa masa cup ɗin ya ajiye. "sakko ki tafi to". da sauri ta ɗago ta kallesa tace,"inje ina?". yay mata wani kallo kamin yace,"Kaka na can na jiranki". sai tayi narai-narai da idanu tana marairaice fuska ta leƙo da kanta ƙasa wai ta gani ko macijin yana nan har time ɗin. "ɗaure kanki". ta lalubo ɗankwalinta da yay can gefe ta ɗaure tujajjan gashinta. "oya to yafa mayafinki ki sakko ki wuce". tuni hawaye ya sakko mata muryarta na rawa tace,"wallahi ba zan iya sakkowa ba". looking at her yace,"saboda?". tace,"kamar na daina tafiya". wata dariya ta tahowa Turaki amma ya gimtse, babu me ganinta a wannan condition ɗin bai yi dariya ba. ya isa bakin ƙofa ya buɗe ba tare da ya kalleta ba raising his voice up yace,"zo ki fice". ta kallesa ta tuna zancen macijin da yay kawai sai ta fashe da kuka sose, ta shiga roƙonsa tana faɗin,"dan Allah don Annabi ka ƙyaleni anan, ba zan iya tafiya ba ƙafana ya daina aiki". sai kuma ta goge hawayen ta ɗago ta kallesa tace,"to ka ɗauko min wayan Yami a perlon Boɗejo sai na kira Kaka tazo ta ɗaukeni". ya haɗe rai ganin tana kallonsa yace,"Kakan ce zata zo ta ɗauke ki?, rashin imanin naki har ya kai haka?, and you even have the guts to send me right?, yaronki ne ni?". tace,"Allah baka haƙuri, kuma ni ba zan iya tafiya da ƙafata ba a yanzu, tsoro nake ji dan Allah ka barni sai da safe". ya zaro ido waje yace,"a ɗakin nawa?". ta gwame fuska tana jin komai babu daɗi a tare da ita tace,"to ni ya zanyi, idan na sakko fa majicin zai kuma bin ƙafata, dan Allah ka ƙyaleni anan sai ka tafi ɗakin Hammah Khalil". yace,"ke zo ki tafi can ɗin". tai shiru bata ce komai ba, yanda tai laƙwas tai mugun basa tausayi, yace,"to idan na barki anan ni aina zan kwanta?, kuma ai kince babu kyau". tana goge hawayen fuskarta tace,"ai nasan ba zakayi min komai ba. kuma ai ga kujera can sai ka kwanta akai, amma ka kira Kaka ka faɗa mata". ya maida ƙofan ya rufe ya dawo ciki ya wuce kan kujera ya zauna. har sha ɗaya na dare yana kan computer, kuma a lokacin suka yi waya da Bello yake faɗa masa flight ɗin 8 zasu bi gobe in Allah ya kaimu. a wannan lokacin Turaki bai iya amsawa ba har Bello ya gaji da hello hello ya kashe wayar. zuciyarsa kawai yake ji tana bugawa, kamar yanda gabansa ya tsananta faɗuwa, me ke shirin faru da shi?, tunda yake bai taɓa jin irin haka a tare da shi ba. doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciya akan kujeran, ya rufe idonsa da zummar yin bacci amma sai ya kasa, wannan faɗuwar gaban nasa ya tsananta har ya kai stage ɗin da baya jin zai iya yin bacci sai dai in ɓarawon bacci ya ɗaukesa. tashi yay ya shiga toilet yayo alwala yay nafila raka'a huɗu, ya ɗan jima yana ta adu'a kamin ya tashi ya buɗe closet ya ɗauko pijams nasa ya saka. gaba ɗaya ya manta da wata Fillo a ɗakin sai yanzu da zai hau kan gado, yasa hannu ya dafe goshinsa, me ya sa me shi ne?, agogo ya kalla yaga har 12 tayi babu damar ya tasheta yace zai rakata. ƙaramin tsaki yay ya hau gadon ya kwata ta gefe, ita kuma tana daga tsakiya ta dunƙule rufe da blanket sai baccinta take, baccin da bata san lokacin da ya ɗauketa ba. wasa-wasa dai har ƙarfe ɗaya Turaki na kwance idonsa a lumshe ya kasa bacci, ya miƙe zaune yana kun
🏠