ka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?".
Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure".
Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zaije ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school".
"to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya ɗauko ta ko".
Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop ɗinsa dake cikin jaka. Yay danne danne aciki ya juyar da fuskar laptop ɗin yana nunawa Turaki.
"Na sami number'n contractor ɗin, zanyi waya da shi zuwa dare". Turaki ya faɗa a sanda ya gama karanta rubutun dake jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta.
Bello Ƙaraye na binsa da kallo har sanda ya taka steps hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file dake ƙunshe da takardu fal aciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon dake cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya.
Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali.
Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa".
Ya faɗa sannan ya juyo ya zauna kan kujerar dake fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company ɗin ba".
Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?".
"yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan".
"ta ina kai ka gansu?".
"a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya ɗebe su".
Ya faɗa ƙwayar idonsa na haskawa da dimbin ɓacin ran dake ciki, ya ɗora ƙafafunsa kan table ɗin dake tsakiyarsu, sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake zaune.
Idanunsa a kulle yake cewa,"rayuwa cike ta ke da marasa halacci, ko kaɗan bana son mutum mara gaskiya".
"So now how are we going to tackle this problem?".
Bellon ya faɗa shima in astonishing at what Turaki had said.
"na san yanda zanyi tackiling ɗin abun, let's get out of the meeting first".
*Gombe, Dukku.*
*Alh. Ahmad Alfindiki Residence, 8:30am.*
"Kaima ai ka sa ni, it's either na kwana gida ko kuma na wuce gidan Khalid, na tsani kwana a hotel if not necessary".
Yusuf ke magana a wayan dake maƙale a kunnensa, yasa key ya rufe motan sannan ya wuce ɓangaren Inna Wuro wato Kakarsu, har lokacin daya shiga parlonta bai gama wayar ba.
Inna Wuro na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun parlon ta kalli Yusuf daya duƙa yana cire takalminsa, ta taɓe baki ta ɗauke kai taci gaba da kallon tv da ta ke.
"yes kusan 2 weeks ma kenan, but i think i will be coming back next tomorrow by God willing. Becox akwai patient ɗin da nake da ita acan".
Yaci gaba da wayar yana ƙarasowa ya zauna kan 1 seater. "alright i will you call before then insha'Allah".
Inna Wuro dai dake kallo hankalinta ya rabu gida biyu, tun shigowarsa ta ke jera ƙwafa. Ji ta ke kamar ta tashi ta fizge wayar ta rotsa ta a ƙasa, sai taga ta tsiyan shigo mata waje babu sallama. Ta lura ma gaba ɗaya yaran gidan sun maida ita ƴar iska, kowa ya tashi shigo mata waje sai ta kaɗo masa yake shigowa da sallama, sun fi gane su shigo kullum suna ɓaɓatu a waya kamar dan su bature ya ƙera wayar.
Yusuf daya gama wayar sai da yay typing message a wayarsa kana ya sakata a aljihu, sannan ya kai idonsa kan Kakarsu yace,"Ina Kwana".
Ba tare da ta dube shi ba a fusa ce tace,"yana kwano".
Yay ɗan murmushi ya ƙara cewa,"kin tashi lafiya?".
"da baka ganni anan ba ai".
Yace,"to Allah ya ƙara lafiya".
Bata dai amsa mishi ba taci gaba da kallonta, kallon da gaba ɗaya ba fahimtarsa ta ke ba. Bakinsu kawai taƙe kallo tana yin dariya a inda ya kamata, ta kuma ja uban tsaki a inda akai mata ba daidai ba.
Ta gefen ido ta ke ta kallon Yusuf, wanda ya sauko ƙasa ya takwashe ƙafafunsa, ba tace da shi ƙala ba sai daya janyo flask gabansa sannan cikin hanzari ta dakatar shi.
"me haka?, kwanon abincinka ko nawa da zaka wani janyo shi gabanka?, ko kuma Uwarka ta dafa ta kawo min ne da zaka nuna min iko da shi?, salon dai neman magana irin ta bawa...ina ce da ka shigo ko sallama baka min ba balle na sami arziƙin gaisuwa, saboda ka maida ni abar banza shine sai da ka gama waya da wanda ya fini tukunna zaka durfafi abincina...to baka isa ba, kuma ba'ai wannan halittar da zata taɓa