ɗan ya zuba tea ɗin, soyayyan bread da ƙwai ne, slice biyu ya ɗauka yaci.
zuwa lokacin bacci har ya fara ɗaukar Fillo, ta kifa kai a jikin gadon. a cikin baccin nata taji yana waya yana cewa,"haka fa, ai dalilin da yasa ma ba'a fiya son a tsaya ƙofar gidan ba kenan, both the two side, an ma fi samun wannan matsalar daga ta gate ɗin ma'aikatan gida. yes, ai kwanaki ma akwai baƙuwa da muka yi tana taɗi anan main gate so basu ankare ba sai jin abu tayi ya nannaɗe mata jiki, ana dubawa akaga ashe maciji ne. the same abinda ya faru da wata ƴar aiki ma, tana compound nasu ne ko tana bakin gate tana taɗi, na dai manta but itama ce akai abu kawai taji yana shiga cikin kayanta, ashe wani tsohon maciji ne yayi girmana, da ƙyar aka cire macijin nan a jikinta, ƙarshe ma mutuwa yarinyar tayi, shiyasa ai duk wanda ya san hakan yana kiyaye tsayuwa a compound ko bakin gate, don akwai ɓoyayyun macizai da yawa, shiga jikin mutum kawai suke kamar an aiko su, most especially masu tsayawa suyi zancen nan, suna tsaye sai dai suji maciji ya shige jikin...".
ai bai ƙarasa ba Fillo ta kurma wani uban ihu tana haɗewa da salati, cikin second ɗaya ta tashi a ƙasa ta dire akan gado. ta cure a wuri ɗaya tana faɗin,"na shiga uku na lallace, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, maciji wayyo Allah na". faɗa take tana ƙara maimaitawa ataimaka mata maciji ne, maciji ya shige mata jiki, shi dai kawai yana zaune yana kallonta kamar tv, yay hanging wayar ƙaryar da yake yi, sai da ya tabbatar tsoron ya shigeta sosai ta yanda gobe ko uban Amir ne yazo ba zata sa ƙafa ta fita wajen ba, tukunna ya buɗe baki yace,"keee".
ya faɗa da ɗan ƙarfi, wannan kiran sai ya ƙara tunzurata ta saki ƙara me uban ƙarfi tana dunƙulewa ta kai ƙarshen gadon ta cure wuri guda.
"ka kore shi dan zatin Allah, wayyo gashi nan ya hau ƙafata, innalillahi Kaka kizo ki taimka min, Maciji ne ajikina gashi nan yana bina". tunda Fillo take bata taɓa tsorata irin yau ba, hawaye a fuskarta kam tamkar an kunna famfo, acikin blanket ɗin da ta rufe kanta da shi ta ɗan buɗe ido kaɗan sai taga duhu, nan ta ƙara sakin wani uban ƙaran da yafi wancan, ɗiff kuma sai tai shiru kamar ruwa ya cinyeta.
wannan shirun nata sai Turaki yay zaton ko tsoronne yasa ta ɗauke wuta, saboda haka kawai ya ɗauke kansa akanta yaci gaba da aikinsa, computer yake kallo amma babu abinda ke haska masa acikin ido sai lokacin da Amir ya riƙe hannunta ya kuma ja hancinta.
haka ɗaya kuma yaji ya kasa natsuwa, yaji kamar tsoro na so ya kamasa, yana typing a wayar hannunsa yana kallon kan gadon inda ta dunƙule, a ransa yaji kamar shirun nata ba lafiya ba, in bacci ne takeyi minutes ɗin da tai taking a haka tuni ta mirgina, in kuma tsoronne zuwa yanzu ai ya barta, sai yaji hankalinsa bai kwanta da hakan ba, ya ajiye wayarsa ya miƙe ya isa kan gadon yana dukan ƙafarta dake cikin blanket, shiru shiru bata motsa ba.
sai yaji kamar zuciyarsa ta harba a lokaci ɗaya, ta-ke ya haye kan gadon ya yaye blanket ɗin, yana taɓata yaji jikinta ya saki ta tafi luu ta faɗa gefensa, tuni idonsa yayo waje yana furta innalillahi, kamin ya diro akan gadon ya shiga toilet ya ɗebo ruwa.
tun bai haye kan gadon ba ya watsa mata ruwan a fuska sai gata ta farka a matuƙar firgice tana ƙwala kiran,"Umminaaaa". ta faɗa tare da fashewa da raunataccen kuka, irin kukan da duk wanda yaji sai ya taɓa zuciyarsa.
tsakiyar gadon ya haye ya janyota jikinsa ya kewayeta da hannayensa duka biyun yana me rufe idonsa. wani abu da bai san menene ba yaji ya tsarga tun daga tsakiyar kansa har tsakiyar tafin ƙafarsa, sunan Ummina da ta ambata shi ya daki zuciyarsa, bai taɓa jin tausayinta ba sai ayau.
"Ummina". ya ƙara jin sunan ya haska cikin kansa, kenan ta tsorata ainun, tsoron da ya kai gejin da har take ganin babu mai iya cetarta sai Umminta, ta tsorata ta kira sunan Ummin da bata raye akan tazo ta taimaka mata.
idonsa ya buɗe ya sauke a tsakiyar kanta, tunawa yake da sanda Kaka ke shaida masa cewar,"marainiya ce Mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta ma haka". to amma har yau neman dalilin da yasa Kaka ta ɓoye masa cewar mahaifinta ya rasu yake, sai dai tunaninsa na bashi ko don saboda Hayyo baida kyan hali ne.
sai yaji ruwa ya cika idonsa kamar zai yi kuka, bata da Ummi bata da Abba amma tana da shi, tana da shi har abadan abadina, kuma alƙawarinsa ne zai tsaya mata kamar Umminta, zai tsaya mata ba kamar Hayyo da ya sani ba, zai tsaya mata ne kamar nagartaccen uba.
sai ya ƙara rungumeta a jikinsa yana jin yanda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso ƙirjinta saboda firgicin da ta ke aciki, numfashinta kuma na fita a wani fiffizga, tana ta kiran sunan Ummi a hankali.
ya buɗe baki zai yi magana yafi sau uku duk sai yaji yama rasa me zai ce. can kuma a hankali ya kira sunanta dai-dai satin kunnenta,"Fulaniii". ya ambaci sunan kamar me koyon magana, haka kuma amon muryar kamar ba nasa ba.
Fillo ta ƙara ƙanƙame shi tana daɗa tattarewa a jikinsa kamar me shirin shigewa