NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 128 of 323

kin gama aman sai ki kwanta anan". ya faɗa yana nuna mata gado da bakinsa, tare da miƙewa zai fice. kamar wacce aka dannawa pause haka ta tsaya tana sa hannu ta rufe bakinta, idanuwanta suka firfito waje dan ita ɗaya ta san me take ji, haka har sai da maganin ya koma, tana sauke numfashi tace,"na shanye". yay mata shiru ya fice ya barta, yin duniya ta buɗe ƙofan duk da cewar there is spare key amma ƙofan yaƙi buɗuwa, means ya bar key ta waje kenan, wucewar five minutes sai ga shi ya dawo da coolern abinci a hannunsa, tana kallo ya wuce sai dai at this time ta kasa attempting buɗe ƙofan, binsa tayi da ido kawai har ya zauna kan kujera. ya waigo da kansa yay mata kallo ɗaya, kuma take ta gane nufinsa a sanda suka haɗa ido, ta taho a hankali tazo ta zauna a ƙasa, ta ɗauko coolern dake kan table da plate ta zuba soyayyan taliya da vegetables ta zuba kaɗan, kuma kamar ance ɗago ta ɗago taga ya zabga mata wani nugun kallo, ba shiri ta ƙara abincin ya ɗanyi auki sannan ta fara ci. har ga Allah dama yunwa take ji, rabonta da abinci tun safe, hakan yasa ta zage tana cin abincin, ba ta ankare ba taga har ta cinye. son samu ace tayi ƙari to amma ba zata iya ba, Turaki dai idonsa na cikin glass yana operating laptop ɗin dake gabansa, tana ta kallonsa for almost 2minutes taji agogon ɗakin yayi ƙara, tana dubawa taga har 8:30. ta juyo tana ƙara kallonsa tace,"don Allah ka buɗen ƙofan na tafi, hakan babu kyau, Kaka tana can tana jirana". ya kalleta ya kalla coolern gabanta yace,"kin cinye?". ta girgiza masa kai,"na ƙoshi". yana ta kallon coolern yace,"buɗe na gani". ta buɗe yaga saura kaɗan bai fi spoon goma ba, ya galla mata harara yace,"juye ki ƙarasa cinye shi, wa kike tsammanin ya cinye sauran jagwalgwalonki?". ta marairaice tace,"cikina na ciwo". yace,"zo ɗau magani ki ƙara". sai ta rumtse ido sosai tana yin ƙasa da kanta, ta shiga afa abincin kamar me cin magani. kafin ta ɗago ta kallesa taga yanda idonsa ya sauya kala, haka ɗaya sai taji bala'in tausayinsa cikin ranta. kuka ta ke son yi amma bata so ta yi gudun kar ciwon kanta ya ƙaru, ga shi duk iyakar ƙoƙarinta ta kasa yi masa rashin mutuncin da ba zai ƙara sa shi shigo da ita ɗakinsa ba, infact kallonta ma ba lallai ya ƙara yi ba, to amma daga zaran tai attempt na yi masa wani abu sai wannan girman kwarjinin nasa ya tarwatsa duk plans nata. with breaking voice tace,"baka ci abincin ba, kuma ɗazu kace kana jin yunwa, ka cinye wannan ɗin". kai tsaye ya bata amsa da,"yara ne suka girka". yanda voice ɗinsa ya fita sai ta ƙara jin tausayinsa haka siddan. tace,"to haka zaka kwana da yunwa?". still ba tare da kallonta ba yace,"Maama tayi bacci". sai tai shiru tana kallonsa, taji ƙwalla ta cika idonta da tausayinsa, ta lura ba ya iya sakewa idan ba tare da Hajiya Madina ba, haka kuma magana ma baya iya yinta sai yana tare da Maama ko Zaytuna, da su kaɗai take ganinsa taga yana ta zuba magana har haƙoransa su dinƙa washewa da dariya, to randa kuma aka ce mahaifiyarsa ta dawo fa?, tunda ta fara aiki bata taɓa ji ko ganin yaci abincin da ba Maama ce ta girka ba in har a gida yake, ko office ya fita sai Maama tayi girki an bawa driver ya kai masa, to hana rantsuwa ita yasa ta taɓa dafa masa indomie ya kuma sha kunun da ta dama, wataran har Nihal ke tsokanarta da Fillo ƴar sa'a, Hammanmu yaci abincin hannunki. anan hawayen da suka cika idonta suka sami nasarar gangarowa, kewar tata mahaifiyar ya daɗa kamata, duk da Kaka na faɗa mata zuwa yanzu Ummi ta rasu, amma ita ajikinta ba ta jin hakanne, tana ganin kamin duniya ta tashi kamar zata ga Ummi, kamar zasu ƙara rayuwa tare da Ummi, kamar Ummi ta kusa dawowa gareta, amma sai zuwa yaushe zata ga Hammah Hamid?. wayar Turaki tayi ringing, bai ɗaga kiran ba sai da ya tsayar da duk abinda yake yi, daga yanda ya saita natsuwa zaka san da mutum me muhimmanci zai yi magana. ya ɗaga wayar yana rissinawa tamkar yana gabanta, yace,"kin tashi Maama?". daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"na tashi me Babban suna". yace,"how are you feeling now?". tace,"feeling much better dear son. am sorry nayi bacci ban jira ka dawo ba, Zaytuna ta min allura ban san time da baccin ya ɗauke ni ba". Turaki ya sauke numfashi yana miƙewa tare da ce mata,"naji daɗin hakan ai, atleast kin samu kin huta. gani nan zuwa". tace,"i know you are tired, kayi kwanciyanka sai da safe tukunna. have you eaten your dinner?". yay shiru bai ce komai ba, tace,"na dafa maka tea, yana perlonku ka duba. ka tabbata kaci ka ƙoshi before you sleep". yace,"to Maama, thank you, Allah ya ƙara miki lafiya". tace,"yauwa bye bye, sleep tight. karka manta da adu'a". ya ajiye wayar yana kwantar da kansa jikin kujera. Fillo dai nata kallonsa tana jin wani tausayinsa na ratsata. gani tayi ya tashi ya fita yanayinsa na juyawa zuwa na marasa lafiya, kuma kamin ta yunƙura tabi bayansa sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da basket, ya wuce ya ajiye kan table ya shiga toilet ya fito. ka
🏠