NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 127 of 323

kawai ake shansa?, kawai daka sami magani sai kace dole sai na sha. ka barni na wuce please Kaka na can na jirana". ya janyota ta zaune kan kujerar kusa da shi. zai ƙwace roban malt ɗin ta damƙe da kyau. ya dinƙa kallonta da mamaki kafin ya iya buɗe baki yace mata,"aje". ta maƙe kafaɗa ba tare da tace komai ba. ya ƙara ware idonsa yana kallonta, ta rufe ido ta cije fuska tana son janyewa a kusa da shi ta tashi. jin ba zai saketa ba ta buɗe ido ta kallesa tace,"ni wannan nake son sha ba magani ba, don Allah ka bar min". bai san time ɗin da ya saki baki ba yana kallonta, in bai manta ba lokacin da aka kwantar da ita a asibiti uban malts ɗin da aka ajiye ai duk ƴan dubiya aka dinƙa bawa saboda bata sha, hasalima ko anyi forcing nata tasha sai tayi amansa, amma yanzu shi take ce malt take son sha. sai ya sassauta riƙon da yay mata yana ƙara tamke fuskarsa yace,"aje nace". ta kallesa taga yanda idonsa ya kaɗa yay jawur, sai kawai ta kifa goshinta akan ƙafarsa ta fashe da kuka. ya waiga yaga har yanzu Ilham bata fito a kitchen ba, dan haka da azama ya miƙe ya ɗau ledan drugs ɗin sannan ya kama hannun Fillo ya jata suka fice daga parlon, tana ta tirjewa yaƙi sakinta har sai da suka shiga ɗakinsa, ya wurgata kan gado yana saka key ajikin ƙofar, sai dai abinda ya matuƙar bashi mamaki yana waigowa yaga ta buɗe roban malt ɗin tana zubar da shi a ƙasan tiles ɗin. _manage please._ *vote, comment and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *30* Turaki ya harɗe hannayensa a ƙirji yana ta kallon yanda Fillo ke juye malt akan tiles, sai da ta juye tass tukunna ta turo ɗan ƙaramin bakinta da ya ƙurawa ido, yaga ta tashi without looking at inda yake tsaye ta wuce inda wani ƙofa yake ta buɗe, waje ne kamar balcony, mopper ta ɗauko ta dawo tukunna ta shiga toilet ta ɗebo ruwa ta dawo ta goge wurin tas da turaren ƙamshi me daɗi. kamar yanda bai san me zai ce mata ba haka bai san abinda zai yi mata ba. duk tana jin yacca kallonsa ke shiga jikinta amma tayi kamar ta manta tare suka shigo ɗakin, in ace ba Turaki ba ne ba zata taɓa yarda ta ɗau tsayin sakanni ba balle mintuna tare da wani ƙato a ɗaki ɗaya, but shi ko da yaushe zuciyarta faɗa mata take yi he is a good person, he will not hurt you, sai dai ma ya kare mutuncinki da iyakar ƙarfinsa. kuma kamar yanda zuciyartata ta faɗa mata haka Hajiya Madina ta faɗa mata,_"me babban suna ba zai taɓa cutar dake ba Fillo, ko kaffara ba zanyi ba akan hakan, saboda haka karki taɓa jin ɗarr dan kun kasancewa wuri ɗaya tare da shi"._ kuma in the same day ne bayan ta koma ɓangarensu, da Kaka ta ganta a firgice ta tambayeta lafiya?, ta faɗa mata cewar tana ɗakin Maama ne Turaki ya shigo, kuma ya hanata fita yace taci gaba da aikinta shi kuma ya kwanta kan kujera. abinda Kaka tace mata a lokacin shine,_"ba'a shaidar ɗan kuturu sai ya kwana 100 da yatsa, to amma ni zan shaidi Turaki, ba wuri ɗaya muke kwana mu tashi ba, ban san halinsa ba, amma zanyi rantsuwa kan cewar Turaki ba zai cuci ƴa mace ba, ko da ace kuwa zasu kwana wuri guda. kawai dai ki kula sosai Fillo"._ sai da ta gama mopping en sannan tayi bakin ƙofar wurin da har yanzu yake tsaye, tai ƙasa da kanta sosai ƙirjinta sai bugawa yake yi, tana ta aikin jan yatsu shi kuma yay shiru kamar baya wurin. sai da ta gaji da tsayuwa tukunna tace masa,"dare yayi, Kaka tana jirana". tai maganar a sanyaye. ya sauke hannayensa ya zuba su cikin aljihu sannan yace mata,"kin gama shan malt ɗin?". da mamakinsa sai yaga ta ɗaga masa kai alamar eh, ya ƙara cewa,"ya isheki ko a ƙaro?". tace,"ya isheni". hannunta kawai ya kama suka koma zuwa ciki, har yanzu jikinta kwai zafi sosai. yay mata nuni da bakin gadon na alamar ta zauna, tace"don Allah". maganar ta katse dalilin haɗa idon da suka yi yana jifanta da wani kallo. babu shiri ta zauna hawaye na biyo kuncinta, yaja stool ya zauna yana ce mata,"tare aka haife ku da kuka ne?". tai saurin girgiza kai, yace,"to yi min shiru, in kuma anan kike so ki kwana karki fasa". babu shiri tayi ɗif tana goge hawayenta da gyalenta. shiru ya gimla cikin wasu ƴan sakanni, tana ɗago ido ta kallesa taga yana ɓallo magani, bata san lokacin da tace,"ni kam na shiga uku". yaci gaba da ɓallan maganin sannan yace da ita,"bani ruwa". cikin azama ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita, a dabararta na in ta fita ba zata dawo ba, amma tana zuwa taji yasa key a ƙofan, ta waigo tana ce masa,"ƙofan rufe yake". ba tare da ya kalli inda take ba yace,"not necessary sai kin fita, ga ruwa nan akan drower". taji kamar tai ihu, sai kace wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta wuce inda roban faro yake ta ɗauko tare da cup, ta kawo masa yace ta zuba ruwan a cup, ta zuba sannan ya kamo hannunta ya zuba maganin yace ta shanye. da ƙyar ta sha maganin tana sha tana hawaye, suma da guda ɗai-ɗai ta dinƙa sha, tana gama sha sai ga amai nan ya taho, ta miƙe da sauri tayi hanyar toilet taji yace,"idan
🏠