NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 126 of 323

ma zan biyaka insha'Allah". a sannan Turaki ya buɗe idonsa yana ɗauke hannayensa akanta. yana kallon gefe daban kamar zai yi magana sai ya fasa ya miƙe. ya nufi ƙofar fita yana cewa da ita,"biyo ni". ta tashi cikin sauri tabi bayansa. tunda suka hau titi take ta kallon hanya har suka iso asibitin Miyetti, fita yay a motar ya barta ita ɗaya ya shiga pharmacy ya sayo magunguna ya dawo, sannan suka ɗau hanyar gida. ko da suka ƙarasa gida Turaki yay parking a parking lots sai Fillo ta kasa fitowa a motar, ta tsinci ƙafafunta da kasa yin motsi su fita daga motar. tana kallo ya fice ya barta aciki, sai ta bisa da ido tana kallo ya wuce side ɗin Boɗejo, gaba ɗaya ta rasa me take ji a tare da ita, tasa hannu zata buɗe motar ta fita sai ga motar Samha tayi parking kusa da ta Turaki. da dukkan alama tun fitar safe da tayi sai yanzu ta dawo, Fillo tai saurin maida ƙofar tana rufewa a hankali gudun karta ji ƙara, kasancewar tend glass ne amotar hakan yasa babu me hangota aciki sai dai ita ta ga na waje. tai ɗuff ta ɗauke wuta dan ji take kamar zasu iya jiyo numfashinta. Sameer taga ya fito daga driver seat sannan Samha ta fito ta ɗayan seat ɗin, ta zagayo ta side ɗin Sameer ta karɓi roban Maltina a hannun Sameer, sun ɗauka atleast 2minutes suna magana kamin su saki murmushi, tukunna suka bar wajen suna wucewa cikin gida. Fillo taji ta wani girgiza, bata san wannan shirin nasu kuma na menene ba, bata ji su ba, bata san me suka ce ba. taja nunfashi ya ɗauka ledar maganin da Turaki ya tsaya ya saya ta fita daga motar, cikin saurin tafiyarta tai side na Boɗejo cikin zuciyarta tana ta fatan kar Allah ya bawa Samha ikon ganin Turaki, haka kawai zuciyarta ke faɗa mata wannan roban malt ɗin ba malt bane kawai aciki da akwai wani mugun abin aciki, haka kuma ba don kowa aka shigo da shi ba sai don Turaki, tafiya take tana harɗewa tana ƙara jin tsoron mutum acikin ranta, idan ba a film ba bata taɓa tunanin za'a iya samun siblings ɗin da zasu iya kashe ɗan uwansu a gaske ba, sai ga shi yanzu ta gani a zahiri, abin na faruwa a inda take rayuwa. maganar Hajiya Madina ta haska cikin kanta, santa take ce mata,_"ba halina ba ne, ba haka zuciyata take ba, tunda Allah ya halicceni banda mugun nufi akan kowa, zuciyata bata da tsatsa ko kaɗan, kullum roƙon Allah nake kar yasa na cuci wani a rayuwata, amma ban san a ina Samha da Sameer suka ɗauko wannan mugun halin ba, ban sa ni ba, dan ba halin mahaifinsu ba ne..."._ kasa ƙarasa maganar tayi a lokacin saboda kukan da ya ƙwace mata. kamar wadda tayi gudun famfalaki haka Fillo ta shiga parlon Boɗejo, gaba ɗaya ma sallamar ta mance da ita. babu kowa a parlo dan haka kai tsaye bedroom na Boɗejon ta wuce, ta san ba zai wuce can Turaki yayi ba, ta buɗe ƙofar tana shiga da sallama. Ilham dake gefen Turaki a zaune ta amsa sallamar tana faɗin,"bismillah". gaba ɗaya Fillo sai taji ƙafafuwanta sunyi matuƙar sanyi, bata san dalili ba amma haka kawai taji gabanta ya faɗi da ganin Ilham da tayi da kuma yacca ta ganta zaune manne ajikin Turaki. zuciyarta taji na faɗa mata cewar kawai tayi reverse, amma sai taji ta kasa gaba ta kasa baya. Ilham na kallonta sosai tace,"ki shigo mana, ba aiki zaki yi ba?". kan Fillo a ƙasa tace,"ehh". Ilham tace,"to bismillah". Fillo ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, ta shigo ciki idonta a rufe tana jin kamar jiri ne ke neman ɗibarta ya zubar. Ilham na riƙe da hannun Turaki tace,"to Hammah ba sai mu tafi tare ba, tun fa dana dawo ban ƙara zuwa ko'ina ba, Mami sai tace wai a'a, kuma ni ko dubai ina so naje na sha iska, please Hammah zan bika". ya kama hancinta yaja ba tare daya ce komai ba, wucewar 3seconds ya miƙe ya fita Ilham tabi bayansa, Fillo kuma dake tsaye gefe guda ta bisu da kallo. suna fita ta jefar da ledar dake hannunta akan kujera, taji kamar tana so tayi kuka, amma ba zata yin ba saboda har yanzu kanta ciwo yake yi mata. ta rumtse idonta sosai, da ƙyar ta iya gyara abinda zata gyara a ɗakin cikin few minutes ta fice. tana fitowa parlon ta tadda Turaki zaune a kan kujera shi ɗaya, da remote hannunsa yana sauya channel. ta tsaya tana kalle-kalle ko zata ga Ilham, sai dai da dukkan alama bata nan. table ɗin dake gabansa tabi da kallo, fruites ne acikin plate sai roban malt a gefen plate ɗin. tai tsaye daga inda take sai kallon roban take yi, kamar me son ganin wani abu aciki. taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai, bata san me yasa ba haka kawai taji tana mugun jin haushinsa for the first time. inda yake ta ƙarasa ta aje ledan maganin kusa da shi tana cewa,"ka manta a mota". sannan ta kai hannu kan table ɗin ta ɗauke roban malt ɗin zata bar wajen. yay saurin riƙo hannunta ya dawo da ita,"ɗauka ki tafi da su". ta waiga ta kalla ledan sannan ta kallesa, tace,"maganin da ka saya ne fa". shima ɗin yana kallonta yace,"nayi miki kama da mara lafiya?". sai ya galla mata harara yace,"ɗauka ki wuce da shi". kamar zata yi kuka tace,"shi maganin dama haka
🏠