mar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abinda zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken.
kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido.
tana ganin yacca ƴan tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu.
duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji.
wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa.
sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo.
Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abinda tayi ba abinda zai hana sa illata. sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking.
Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita ta windown.
tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa dake tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa.
bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe.
"come out". taji muryarsa ta shiga kunnenta sanda take buɗe idonta duka.
kamar tai banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki.
ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me".
tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki.
suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce ciki inda wani ƙaton parlo yake, inda anan ne yake Turaki ke hutawa.
"kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna inda ƙaton farar cushion yake.
Fillo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata.
kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali tace,"banda alwala".
yanda tayi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma yaji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai aciki. sosai yake kallonta da son gano abinda yasa tayi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?.
jin yay shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. shi kuma yay mata nuni da hannu yana mata nuni da inda toilet yake.
bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in yaso daga baya ta rama sallolin.
da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"don't waste my time".
yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. tai alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani.
la'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau.
minti 1,2,3 har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi jira take ya koma yace mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon.
zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman me lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga da