NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 123 of 323

glass ɗin. Fillo ganinsa yasa gaba ɗaya ta tsure, da ƙyar ta tattaro yawun bakinta tace,"gani". ta faɗa kamar me koyon magana, bala'in tsoro na kamata saboda yanayinsa da ta gani, ita ko babu yanayinsa ma tana jin tsoronsa. "buɗe ki shigo". haka taji amon muryarsa tamkar saukar aradu aka. zata tsaya tunanin maganar tasa taga ya juyo a fusace ya zuba mata rikitattun idanuwansa da suka koma kamar na tiger. babu shiri ta nufi ƙofar baya zata buɗe a tsawace taji yace,"kika shiga nan babu abinda zai hanani ɓalla ƙasusuwanki na zubar a wajenan". take ruwan hawaye ya sakko mata ta dawo tana buɗe gaba ta shiga da tsananin ruɗewa, duk ta firgice ta gigice. ta rufo ƙofar motar tana kifa kai akan cinyarta ta fashe da kuka. Turaki ya dinƙa kallonta babu ko ƙifta ido, a hankali kuma ya mayar da ƙwayar idonsa kan hannun hagunta da Amir ya riƙe for morethan 2tyms, yaji zuciyarsa ta ƙara tamkewa, trying his best to be very calm gudun kar ya illata ƴar mutane, ya damƙo tsintsiyar hannunta dake rawa yana mata mugun riƙo kamar zai karya ƙashin wajen. ta ɗago da kanta a gigice tana kallonsa da tsananin jin zafin riƙon. cikin muryar kuka tace,"me nayi maka?". tambayartata yaji kamar ya tsinka mata marin da zai yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta gaba ɗaya, wataƙila hakan yasa tasan laifinta. acikin rishin kukan da take yi tace,"jiya fa kace ka haƙura, amma tunda baka haƙura ba i will give you half of the money now, ending month sai na cika maka sauran". shi dai kallonta kawai yake yi yana tunani iri iri cikin ransa, tana batun ta basa 25k now, aina ta samu 25k?, wanda ya tafi ne ya bata?, me tayi masa ya bata?. sai ya rumtse ido gam yana ƙara damƙe hannun da mugun ƙarfin da yafi na ɗazu har sai da ƙashinta yayi ƙara, idan ce masa akayi an ganta da wani ba zai taɓa yarda ba don ba tayi kama da wadda zata tsaya da namiji ba, amma with his own 2eyes ya ganta tsaye da namiji a inda babu kowa sai su kaɗai, ƙofar gidan da babu masu wucewa, sama da rabin awa suna hira cikin nishaɗi har tana wage masa all her 32teeths. which kind of purnishment did he supposed to give her?, shin ya ɗimautata da sanar da ita cewar akwai igiyoyin auren wani akanta guda uku reras?, ko kuma yayi mata abinda ba zata ƙara kallon wani namiji ba a rayuwarta?, balle harta bari ya riƙe mata hannu har tai masa dariya har ta barsa yaja hancinta. "wallah zan baka 25k daga baya zan cika maka sauran, amma kayi haƙuri ka sakar min hannu da zafi wallahi, ƙashina ma har ya ɓalle ina jin". tsabar ƙuluwa Turaki bai san lokacin da ya dunƙule hannunsa ya daki bakinta ba ya fashe, shi zata faɗawa ya sakar mata hannu bayan ita halalinsa ce?, and ta iya barin wani ƙaton banza can daban da ba muharraminta ba ya riƙe mata hannu ba tare da ta hanasa ba?. Fillo ta fashe da kuka sosai tana sa gefen mayafinta ta danne leɓenta da ya fashe. "ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?". kuka take sosai tayi maganar, idon Turaki manne akanta yana hasko tsayuwarsu da Amir, cikin jin zafi a heart ɗinsa ya kulle idonsa, yaja motar with high speed kamar duniya zata tashi, tayoyin motar suka bada sautin ƙuuuuu akan kwalta, wannan ƙarar ta haddasa tsoro na bala'i a zuciyar Fillo, kuma tsananin tsoron yasa farat ɗaya ta ɗago da kanta dake kan cinyarta, ganin yanda yake zabga mugun gudu akan titi tayi jikinsa a rikice ta riƙosa tana faɗin,"kayi a hankali dan Allah zamu yi accident fa, ka daina nufar bishiyan can". *Please vote, comment and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *29* motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company ɗin su, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abinda ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa. yay parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. ya kalli Fillo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun sanda ta ke roƙon yay driving nasu a hankali taga baida hankalin dainawa shikenan sai tayi shiru, kuma tsoron da takeji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa. wucewar 20seconds yana kallonta, yana jin yanda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa tai luff kamar wadda baccinta yay mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta ka
🏠