za'a yiwa Yarima aure ko kuma Gimbiya to zaki ga yarda ake ɓarin kuɗi kyace ba'a talauci a nigeria, musamman ma ace bikin sarauta da sarauta ce ta haɗu, to ina faɗa miki in aka tashi kai lefe hatta bayin gidan sai an yi musu sutturu an kuma basu kuɗaɗe. kinga lokacin bikina dangin Mamana sai da suka dinƙa cewa ko dai siyar da ni akayi. yanzu dai ai zaki ganewa idonki tunda muna tare, in bikin Ilham ya tashi uban kayan da zaki samu sai kinsha mamaki, har sai kin kyautar kema".
tun farkon fara labarin Fillo batai magana ba, har Boɗejo ke cewa ko tana ciwon baki ne, amma haka kawai da taji ta ambaci sunan Ilham sai ta sami kanta da tambayar,"Boɗejo wacece Ilham?".
Boɗejo tace,"kul Gimbiya za ki ce, ita ɗin ai ƴar me martaba ce, yanzu in a gaban fadawa kika faɗi sunanta haka gatsal ai kin shiga uku, ƙila ma Fulani tasa a ɗaureki...ita aka sakawa sunana ai shiyasa nake masifar sonta, baki taɓa ganinta ba?".
tace,"ban ma taɓa jin sunanta ba".
Boɗejo tace,"kika ce kuma shekararku biyu a masarauta kafin a ƴanta ku ayo nan da ku...ko da yake zai yiwu ɗin ki kasa saninta, tunda uban ita kaɗai ce baya so, tun tana ƙarama ya kaita can ƙasar arna bata dawo ba sai da ta shekara biyar".
Fillo tai shiru ita dai ƙirjinta sai bugawa yake haka ɗaya babu gaira babu daɗi, wayar Yami dake soke a gefen zanenta tayi ƙara, tai banza da kiran har ya katse, lokaci ɗaya taji sabon ɗaci da ɓacin rai a zuciyarta. sanda kira na biyu ke ƙara shigowa sai taji kamar ta rotsa wayar, Boɗejo dai nata zuba labari tausar ƙafa yayi mata daɗi.
can dai ta gaji tana kallon Fillo tace,"ki ɗaga wayarki mana, anata kira kin sha re, yanzu fa idan samuwa ce shikenan kin yiwa kanki. haba ƙila ma ba lafiya ba tunda kika ga kiran yayi yawa haka, kusan sau shida fa ina jin ma ko bakwai".
Fillo ta ciro wayar hawaye na sakko mata, tabi sunan Amir dake jikin screen da kallo. maganar Kaka ta ɗazu ta haska acikin kanta,_"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni"._
ba don waɗannan maganganun da Kaka ta faɗa mata ba, da idan ta ƙara sauraron Amir a rayuwarta shegiya ta ke, ai me zuciya akewa gori ba mai dukiya ba.
tana ɗaga wayar ba tare da ta amsa sallamarsa ba tace,"ba ta gate ɗin ɓangarenmu ba, main gate na gidan". tana faɗar hakan ta kashe wayar ta cillar tana ɓata fuska.
ta yunƙura zata tashi tana cewa da Boɗejo,"zanje Yayana ne yazo yana ƙofar gida".
Murmushi ya sauka a fuskar Boɗejo tace,"Allah sarki, to gaida shi dan Allah. ki buɗe friedge ki tafi masa da fura tana cikin gora, jiya Nihal ta dama min ita da daddare, akwai inibi ma duk ki haɗa masa da shi, ko kuma zaki shigo da shi ciki ne?, ko can ɓangarenku ɗin zai je?, a'a kinga ma kawai shigo da shi nan ɗin mu gaisa, yanda kike da mutumci ai dole a mutunta baƙonki".
ta girgiza kai tace,"a'a Boɗejo sauri ma yake ai, ba zai shigo ba na sani".
Boɗejo tace,"to ɗaukar masa abin sawa a baki ki kai masa, ba kyaje haka ba gaskiya hannu na dukan cinya".
ba yanda Fillo ta iya haka dole ta ɗauka Furan da inibi saboda takurawan da Boɗejo tayi mata, amma tana fitowa ta bawa me gadi, dan da dai ta bawa Amir gwara ta zubar a kwata, hakan kuma babu kyau.
ta jima tsaye bakin ƙofar gate ɗin kamin tasa ƙafa ta fita saboda bala'in zafin da zuciyarta keyi mata, dole ta fara controlling kanta kamin ta fita.
daga can ƙarshen katangan gidan ta hangosa tsaye jingina akan machine, ta tsaya taƙi ƙarasawa wajen sai shi ya ƙaraso inda take. bata jin zata iya ɗaga ido ta kallesa hakan yasa yana kusantota ta rufe ido da hannunta tana ƙara yin ƙasa da kanta.
Amir na ƙarasowa gabanta sai ya zube a gabanta yana sa dukkan gwiwoyinsa a ƙasa, ya haɗa hannayensa wuri guda alamar roƙo, cikin muryar dake bayyana dana sani da ɗumbin nadama yace,"dan darajar Allah da manzonsa kiyi haƙuri ki yafe min abinda nayi miki, nasan nayi kuskure kuma na karɓi hukuncin da kika min. amma horarwa ta isa haka, da nisanta ni da kanki da kike wallahi tallahi gwara kice na kwanta a akan titi mota tabi ta kaina, and am giving you full assuarance of zanyi hakan domin ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke a tare da ni ba...i know halina ba zai sa ki yafe min ba, but ki ji tausayin Uwar da ta mallaki ɗa guda ɗaya, wannan ɗan nata kuma ya kamu da son mace guda ɗaya, wanda son nata zai iya zama ajalinsa, ita kuma uwar bata so ta rasa ɗanta, ki kwatanta yanda wannan uwar dake son ɗanta zata ji in har ta rasa shi...kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, dan Allah da Annabinsa Halima".
kuka ya kubcewa Fillo, ta sauke hannunta daga fuskarta, ta buɗe idonta a hankali tana sauke su akan Amir, da tsananin mamaki ta ɗan ja da baya saboda ganinsa durƙushe a gabanta yana hawaye, k