NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 12 of 323

e". "yayi muku kyau ai, kuyi ta biye mata tana hanaku baccin kirki, bayan ita ta riga tayi nata tun yarinta". Zaytun tai murmushi me ƙarfin sauti ba tare da tace komai ba, kasancewar ita ɗin ba mai yawan magana bace. Turaki ya ƙara cewa,"dama i just call to check on you, I hope all is well?". "komai lafiya Hammah nah". Yay ɗan jim before saying,"idan kinyi breakfast let me know...amma yanzu fa za ki tashi bana son zama da yunwa, ki kalla time ki gani ƙarfe nawa". Ba tare da ta duba komai ɗin ba tace,"Yanzu fa Safiyan yay Hammah". Tai maganar a shagwaɓe. "shafo cikin ki sai ki faɗa min yanda yake". Ta kai hannu kan stomach ɗinta sannan tace,"Hammah nan yana nan yanda ka san shi a shamule". "to kinga alamar yana buƙatar abinci kenan, i keep telling you babu namijin da zai ɗauke ki alhalin yasan cikinki da bayanki a haɗe suke, he will think you can not bear him a child". Tabbas ya faɗi maganar ne to entertain her, kuma hakan ce ta kasance, dan sai da tayi dariya sosai har baccin da bai bar idonta ba ya saketa lokaci ɗaya, ta miƙe zaune akan gadon tana ɗora pillow akan cinyarta, fuskarta cike da annashuwa tace da shi. "ni da nake so ko da Allah bai azurtani da ƴaƴa da yawa ba, ya bani guda ɗaya tilo da zan saka masa sunan Hammah nah. Dan haka dole na tashi naje naci abinci ko da banyi niyya ba...ni Hammah idan ma kaga ana tallan maganin dake ƙara tumbi ka sayo min kawai". Turaki yay siririyar dariya da cewar,"wasu na neman ragewa mu kuma muna nema". Yay maganar yana mai duban agogon hannunsa sannan yace,"zan wuce office na kusa late". Daga haka sukai sallama cike da kewar juna. *After 10minutes, Growth Stack Software.* *Zone 5, 1st Floor Novare Central, Dalaba St, Wuse 900285, Abuja.* Motarsa ta shigo cikin company ta ƙarasa zuwa wurin da aka tanadarwa ma'aikata domin aje motoci. Tun kafin ya ƙarasa buɗe murfin motar wani tsoho ya ƙaraso wajen cikin sassarfa. "sannu da zuwa ranka ya daɗe". "yauwa Baba sannunmu". Ya faɗa a sanda yake fitowa daga motar ya rufe. Tsohon ya buɗe bayan motar ya ɗauki ƴar ƙaramar jakar laptop ɗinsa, sannan yay cikin office ɗin da ita. Shi kuma Turaki ya mara masa baya, tunda staffs ɗin wurin suka ganshi suke ta rissinawa suna gaida shi matsayinsa na Managing Director a ma'aikatar. Bai shiga office ɗinsa ba kai tsaye ya wuce zuwa ofishin Manager, ya ɗauki kusan 5minutes sannan ya fito ya wuce nasa office ɗin bayan Manager ya shaida masa ya tsayar musu da lokacin da zasu shiga meeting ɗin. Zamansa kenan akan kujerarsa sai ga Saktariyarsa ta shigo, ta aje record book ɗin dake hannunta a saman table ɗinsa, ya janyo shi zuwa gabansa yay rubutu ajiki sannan ya ƙara miƙa mata. Ta ɗauka sannan tace da shi. "ranka ya daɗe PWC sun shigo tun aroud 8:30". Ya ɗago daga kan computernsa ya kalleta, yana mai ɗan ƙanƙance idonsa cikin yin nazari kafin yace da ita. "dama muna da Appointment ne da wasu this week?". "a'a ranka ya daɗe, nima dai nayi mamakin zuwansu..to amma da suka ce min daga ofishin Manager suke sai na tsammaci shi ya turo su wurinka". Ta faɗa tana buɗe wani file na daban dake hannunta ta ciro wani envelop aciki, sannan ta miƙa masa. "sunce na baka wannan". Duk acikin harshen turanci ta ke maganar. Ya miƙa hannu ya karɓi envelop ɗin ya buɗe, cikin seconds ɗin da basu haura 10 ba ya gama karanta abinda ke jikin takardar. Bayan ya gama ya miƙa mata tare da cewa. "ki kai office ɗin Manager, zamu yi waya da shi yanzu". Ta rissina tare da karɓa sannan ta fita daga office ɗin. Don Allah share to other groups🙏 Follow me on: ArewaBooks-Halimahz OkadaBooks-Halima_hz Wattpad-Halima_hz Youtube Channel-Sahaz Multimedia *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *5* Fitarta da minti biyar akai knocking ɗin door, ba tare daya ɗago kansa daga kan system ba yace,"yes come in". Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa. Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi. "sai yanzu ka ga damar fitowan?". Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gareni ba balle na sami me tashina da wuri". Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kai auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka". Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?". Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado". Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara". Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?". "yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka". Bello dake masa wani kallo yace,"Baka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi ma
🏠