kin idonta haskowa take yi wai Turaki na driving ga babban mota yayo kansa kuma babu burkin da zai taka ya ƙwace, wanne kalar mummunan haɗari ne zai faru?, wataƙila shikenan rayuwar Turaki ta ƙare kenan kamar yanda suke so, ina alƙawarin kula da su data ɗauka?, tai saurin rumtse ido tana girgiza kanta da kawar da abinda ke cikin kanta.
ta dafa shoulder ɗin Fillo ta ƙara ce mata,"na gode, ina miki godiya da ƙoƙarinki wajen ganin rayuwar ɗana ta kuɓuta, insha'Allahu a wannan shekarar da ke za'a yi aikin hajji, ƙafata ƙafarki zuwa saudiya Fillo".
Fillo na kallon fingers ɗinta tace,"Na gode Maama Allah kuma ya amsa".
sai taji kawai Hajiya Madina ta janyota jikinta tayi mata side hug, tana jin ruwan hawayen da ya fito daga idonta ya sauka akan kafaɗarta. muryarta da rauni tace,"yanzu ba don ace Allah ya nufeki da jinsu ba shikenan komai da suka shirya sai ya faru ko?".
Fillo dai tayi shiru bata ce komai, illa iyaka tsananin tausayin Hajiya Madina dake acikin ranta. ta janye a jikin Maama tasa gefen mayafinta ta goge mata fuska tace,"please Maama stop crying, adu'a kawai zaki ci gaba da yi, Allah ya ƙara kare Hammah su kuma Allah ya shirye su".
Maama tace,"insha'Allahu, je ki sha maganin. hope kinci abinci?". tace,"zanci yanzu sai na sha maganin". Maama tace,"akwai sauran breakfast a dining, ki ɗiba ki wuce da shi ɗakina sai kici acan, ki tabbata fa kinsha maganin".
Fillo bata wuce ba ta sunkuyar da kanta tana wasa da gefen mayafinta, Hajiya Madina ta fahimci tana so tayi magana, hakan yasa ta kamo hannunta tace,"do you have something to say?". ta ɗaga kai tace,"ehh Maama, dama ce zanyi hope ba wanda ya san zaiyi tafiya?".
da mamaki Hajiya Madina ke kallonta, ai tayi zaton daga ita sai Bello suka san da batun tafiyar Turaki Hong kong. kan tai magana Fillo tace,"dama naji yana waya da Hammah Bello ne akan tafiyar". Maama tace,"ehh babu wanda ya sa ni, na kuma hana Khalil yay maganan ma if muna tare. je ki sha maganin bana son ciwonki".
Fillo ta fito a kitchen ɗin, Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, tana ƙara jin yarinyar na shiga can cikin ranta.
a dining Fillo ta zuba chips da awara da souce, ta hau sama ta ɗauko maganin sannan ta dawo ta ɗauka abincin da wuce ɗakinsu, kamin ta fito Khalil da ta samu a parlo yana kallo yana ta tsokanarta da acici. kaɗan ta samu taci abincin saboda bakinta da take jin babu taste, tana shan magani ta kwanta a wurin, ko da teacher ɗinsu yazo ma bata samu ta iya zuwa ba, Ɗausiyya na tashinta tace ta faɗa masa bata da lafiya.
bata tashi ba sai 12, shima ƙarar wayar ɗakinsu ce ta tasheta. daga ɓangaren Nihal tace da ita,"Fillo please if you are not doing anything zo ki taimaka min da gyara closet ena".
Fillo tace,"toh". ta ajiye wayar ta shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce.
tana shiga parlo ta tarar da Zaytuna zaune, sai taji gaba ɗaya ta kasa ɗaga ƙafarta saboda azaban kunyar Zaytuna ɗin. sim sim kanta a ƙasa ta ƙarasa shiga ta durƙusa har ƙasa ta gaida Zaytuna.
Zaytuna dai data san komai kuma ta fahimci komai sai tayi murmushi sannan ta amsa gaisuwar. tace da ita,"sai yanzu kika shigo?".
still kanta na ƙasa tace,"na shigo tun safe, Maama tace na kwanta saboda kaina dake ciwo".
"ayyah Allah ya sauƙe, ko ayi allura?".
cikin azama Fillo ta miƙe tayi upstairs bayan tace,"a'a na warke".
Zaytuna ta rakata dariya, ta jima bata ga me tsoron Allura kamarta ba, duk zafin ciwo aka ambaci allura sai tai firgigita ta taashi wai ta warke, ko da ace ciwon cinta yake.
a ɗakin Neehal tare suka gyara kayan closet ɗin, Nihal sai labari taketa bata, mostly duk akan school ne wanda hakan ke ƙarawa Fillo jin kwaɗayin tayi karatu sosai, har itama ta kai matakin university, dama Maama tayi mata alƙawarin indai lesson teacher ɗinsu ya bada good perfomance akanta to zata zana private waec, in yaso idan zata je malasia course na phd nata sai su tafi tare, wanda hakan ya ƙara mata ƙaunar Hajiya Madina.
sosai Nihal ke burgeta saboda sauƙin kanta, ita da Khalil sune kaɗai suka yo halin mahaifiyarsu.
after azhar Fillo na parlon Boɗejo tana yi mata tausa, Boɗejo sai labarai take yi mata kala-kala. kuma labarin sosai yake yi mata daɗi, wani wurin tayi dariya wani wurin kuma tai murmushi, wani wurin kuma ta jinjina irin tuggu da ke cikin gidan sarauta, cikin ranta tana godiya ga Allah da yasa bata da haɗi da sarauta.
can sai taji Boɗejo tayi shiru, ta ɗago kai ta kalleta, sai taga hanyar bedroom ɗinta take kallo, Fillo ta waiga taga Turaki ne ya wuce, gabanta taji ya faɗi, da sauri ta juyo tana ci gaba da matsawa Boɗejo ƙafarta, fatanta ɗaya Allah ya kawo abunda zai tasar da ita daga wurin nan yanzu, kuma Allah yasa kar Boɗejo tace zata aiketa ɗakin nata, dan sam bata so ta haɗu da Turaki.
Boɗejo tace,"ina faɗa miki to haka ake yi fa idan biki ya tashi, in kika ga yanda ake kashe kuɗi sai kiyi zaton ko ba'a san ciwonsu ba ne. to da yake al'adar gidan sarauta ce hakan, indai