ɗaukar fushi da shi na tsawon wata da watanni, gaskiya kin bani kunya da mamaki".
cike da takaici Yami ta ƙarasa maganar.
Fillo dai kuka kawai take yi tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta, ita ake bawa laifi?. gaskiya ko Yami da Kaka zasu haɗu su kasheta bata jin zata iya yin abinda suke so akan Amir, in har dan ta ɗaga kiran Amir ne ko ta basa damar zuwa gwara ta mutu, dan ko kaɗan bata son jinsa balle ganinsa.
Kaka tace da ita,"ni dai ban taɓa tunanin a ɗan guntun ililimin da kika samu daga wurin Amir ba, ilimin da wanda ya haifeki ya kasa baki shi, zaki iya butulcewa Amir ba, ko da kuwa me zai yi miki, irin faɗi tashin da yaron nan ya dinƙa yi a game da rayuwarki ta inganta da kuma lafiyarki yafi ƙarfin wulaƙanwa daga gareki. amma babu komai iya abinda kika yi ma kin zubar min da mutuncina a idon iyayensa, na kuma gode, domin babu wanda zai yarda cewar bani na saka ki ba".
Fillo na kuka sosai ta ɗago ta kalli Kaka tace,"shikenan ko mene ya faru sai a ɗora min laifin?, me yasa ba za'a tambaye ni abinda yayi min ba?".
Yami ta galla mata harara tace,"rufewa mutane baki, ba'a haƙuri ma'aikin Allah yay haƙuri?, ko kuma ba'a yafiya muke yiwa Allah laifi mu nemi yafiyarsa kuma ya yafe mana. to wallah tun muna shiri da juna ki sasanta tsakaninku a yau. nace masa yazo, dan haka ki tafi da wayar kwa haɗu da shi acan. mu ba mutanen banza bane da sai da aka tsayar da maganar aure tsakaninku sannan ki nuna mana ba haka ba, ƙarya kike yi kinyi kaɗan".
Kaka tace,"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni".
jin furucin Kaka yasa Fillo ta dinƙa kallonta babu ko ƙifce, ji take ina ma ta haɗiyi zuciya ta mutu, anya ma Amir bai asirce mata Kaka ba?, ko da yake babban asirin da zakai wa mutane akan suƙi ganin bad side of you shine ka zama mutum na ƙwarai a idon duniya. ta tashi ba tare da tace komai ba tai fuuu ta fice daga ɗakin tana ƙara sakin kuka.
a ƙofar ɗakin taga Maijidda a tsaye tana hawaye, tai mata kallo ɗaya ta ɗauke kai tayi gaba abinta, Maijidda tabi bayanta tana kiranta, Fillo ta juyo a fusace tace da ita,"da kika iya zuwa kika faɗawa Yami na butulce masa why can't you ki faɗa mata shi irin wulaƙancin da yay min, why not ki faɗa mata ya kira ni da ƴar zina ko sa nuna masa kuskurensa, amma sai kika karesa kika bar laifin akaina ni ɗaya. babu komai, thank you for that, ko yanzu kin nuna min matsayina wurinki, kin nuna min ni ɗaya zan iya fighting akanki ba dai ke kiyi akaina ba".
Maijidda ta riƙo hannunta tana so tayi mata magana amma Fillo cikin ƙunar ran da take ji ta fizge tayi gaba abinta. Maijidda nace mata,"wallahi ni bancewa Yami komai ba, ita ta fuskanta da kanta shine ta ɗauko wayar ta kawo miki amma wallahi ni ko ɗaga wayar Amir ban ƙara yi ba tunda kika faɗa min abinda yay miki".
Fillo dai ko tsayawa bata yi ba balle ta tsaya sauraron abinda Maijidda ke faɗa, dan tuni ta toshe kunnenta daga jin abinda ma zata ce mata wanda bata ganin she can believe her.
har ta shiga parlon Hajiya Madina bata daina zubar da hawaye ba, da tarin tunani fal cikin ranta a game da Amir da kuma Kamal, mutumin da ta fara haɗuwa da shi lokacin da ta gudo daga gida, kuma mutumin da yace ba zai iya auren ƴar gaba da Fatiha ba.
ganin babu kowa a parlon kai tsaye kitchen ta wuce, tana shiga ta kunna tap ta wanke fuskarta acikin sink, jin motsi kamar an shigo kitchen ɗin tai saurin saita natsuwarta tana daɗa komar da hawayen dake ƙoƙarin sake sakkowa.
"menene Fillo?". taji muryar Hajiya Madina a bayanta, hakan yasa ta juyo da sauri tana durƙusawa ta gaida ita.
Hajiya Madina ta ƙarasa shigowa cikin kitchen ɗin, tace da ita ta miƙe. tana kallonta sosai tace,"kukan me kike?, wani abin aka yi miki?".
Fillo ta girgiza kai,"a'a Maama, kaina ne ke ciwo".
"kuma shine kike kuka haka, baki san zaki ƙarawa kanki ciwon ba ne?". tayi shiru bata ce komai ba.
Hajiya Madina tasa hannu ta taɓa kan nata sai taji zafi rau. "subhanallah, kin sha magani?".
ta girgiza kai tana so ta riƙe sabon kukan dake ƙoƙarin zuwa. "ya haka Fillo, banda abinki ba sai da lafiya ake yin komai ba, sai kisha magani kiyi kwanciyarki tunda ga Ɗausiyya. maza jeki bedroom ɗina akwai magani cikin drowern madubi, ki buɗe ki ɗauka sudrex ki sha. sai kije ki kwanta zuwa anjima".
tace,"tom na gode Maama". sai tasa hannu a gefen zanenta ta ciro key na mota. Hajiya Madina tasa hannu ta karɓa tana faɗin,"thank you very much". kan Fillo a ƙasa tace,"kiyi haƙuri ranar ban sami damar faɗa miki ba, naga idan nace sai nazo na faɗa miki before muyi taking any action zasu cimma burinsu ne, thats why na tafi ɗakin Hamman kai tsaye".
Hajiya Madina ta dinƙa kallon key ɗin babu ko kifta ido, ci