NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 117 of 323

e ta sunturi akan kumatunta idanuwanta a kulle. ƙwacewa take sonyi amma ta kasa saboda wani irin kasala da taji yana neman rufeta dalilin jin kanta a kafaɗarsa tana shaƙar wani ƙamshi me bala'in daɗi. yay taking deep breath yana jin kamar yayi hugging ɗinta, he feels like he doesn't want to move away from her, yana jin kamar ya fasa tafiyar just becouse of her, sai dai he has to go, ko dan gudun kar a haɗa Bello da fake kaya. ƙirjin Fillo na bugawa tace,"zanje in kira Maama". A hankali yace,"to kukan me kike yi?, ko na fasa tafiyar?, ko na kira Bellon ki faɗa masa ya kula da ni?, kuma nima ai zan iya kula da kaina". gaba ɗaya sai take jin yacca yake mata magana kamar cikin mafarki ko kuma dai ba da ita bane wata ce daban irinta yakewa magana. bata san ta yanda bakinta ya buɗe ba ma har take iya magana haka duk da uban tsoronsa dake tare da ita, dan wani irin faɗuwan gaba da take ji. ta ɗan kallesa kaɗan ganin yana kallonta tayi saurin ɗauke idonta, taja yatsanta ɗaya tace,"ba zaka iya kula da kanka ba ai, amma shi naga yana sonka, kuma yana da mutumci, Maama zata basa amanarka...Allah ubangiji ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah yayi maka katanga kan katanga daga dukkan sharrin me sharri, Allah ya ɗoraka akan maƙiyanka, Allah ya tsareka da tsarewarsa ya kiyayeka da kiyayewarsa, ka kula sosai da kanka Maama zata ji daɗin hakan, karka yi wasa da shan magani". tunda ta fara maganar yake kallonta babu ko ƙifce, da wani kalar tunani da yake akanta. kamar ya buɗe komai a yanzu, but zuciyarsa na faɗa masa not now, this is not the right time da ya kamata ya buɗe komai. yana ji ta zame jikinta a hankali tana miƙewa tsaye, so take yi ta bar ɗakin amma kamar an riƙe mata ƙafa, kuma kamar tana jiran umarninsa ne. tayi dai tsaye ta kasa motsawa balle ta tafi. tsaye shima ya miƙe yana kulle idanuwansa, jikinsa duk babu ƙwari haka yake jinsa, bai taɓa jin zai yi tafiya yana fargabar tafiyar ba ko kuma yana tsoro, amma this time around da zai tafi yayi just 4days ji yake kamar wani mugun abu zai faru kafin dawowarsa, ko kuma wani mugun abu zai faru da shi. bayan ya zuba hannayensa cikin aljihu taji yace,"bana son yawan kuka. when am back you will help me find Mum". kallon da take yi masa bana mamaki bane tunda a yanzu ta riga tasan komai, kallo kawai take yi masa me cike da tausayawa, bata ankara ba sai ganinsa tayi tsaye a gabanta dab da ita, tayi wani ƴar guntuwa a gabansa dan da kaɗan ta wuce cikinsa, magana take so tayi masa amma bata san ta ina zata fara ba, hannunta nata karkarwa taji ya sunkuyo da kansa ya ɗora goshinsa akanta yana kama hannayen nata ya riƙe. muryarsa can ƙasa taji yace,"when will these hands stop shaking?". sai taji kamar numfashinta zai yi seezing, jin an turo ƙofar ɗakin ta firgita taja da baya, ganin Zaytuna duk sai ta rikice, so take ta fice daga ɗakin da gudu before Zaytuna ta ɗago daga sunkuyawar da tayi tana ajiye abu, amma ya riƙe hannunta ta yanda duk abinta ba zata iya ƙwacewa ba, Zaytuna ta ajiye aiken Boɗejo da ta shigo da shi ta fita. tana fita Fillo ta fashe da kuka tana ture hannunsa daga riƙon da yay mata. ƙarar shigowar text a wayarsa yasa ya saketa ya nufi wayar, ita kuma ta buɗe ƙofan ta falle da gudu. Turaki ya buɗe messge ɗin Zaytuna da ya shigo yana karantawa. _Boɗejo and Maama are coming._ yana gama karantawa ya juyo da kallonsa inda ya bar Fillo, sai gani yay babu ko ɓurɓushinta, yasa hannu ya shafo wuyansa yana smiling. _sorry for the late update._ *please vote, share and comment.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *28* washegari da safe Fillo ta gama shiryawa kenan sai ga Yami ta faɗo ɗakin kamar an jefota. fuskarta a haɗe take kallon Fillo, ita kuma tana ganin hakan tasha jinin jikinta. Yami ta miƙa mata wayar hannunta tana faɗin,"ungo nan, idan ta kama ki tafi da ita can, abu ɗaya kawai na sani shine ki tabbatar kin ɗaga kiran Amir kunyi magana da shi, ki kuma basa damar zuwa idan ya buƙaci hakan". idon Fillo suka ƙanƙance tana kallon Yami da ta ɓata rai, ƙirjinta taji yana bugawa da sauri sauri domin bata tunanin zata iya bin umarnin Yami. Yami ta doka mata tsawa,"kin karɓa ko saina hamɓare ki". tuni jikinta ya hau kyarma tayi sauri ta karɓi wayar tana duƙawa a wurin ta fashe da kuka. Kaka tace,"to dama ni dai da naga ba kiyi magana ba yasa nayi shiru, zatona ko baki san komai ba". Yami tace,"ai ina sane, na zuba mata ido ne naga iyakar gudun ruwanta. sai naga rashin hankalin nata da gaske ne, to banda ma dai ɗan Adam butulu ne dan ubanki ina ke ina juyawa Amir baya, duk abinda Amir zai yi miki a rayuwa ai ke me iya shanyewa ce ba wai kiyi zuciya da shi ba, wane irin alkhairi ne yaron nan bai yi miki ba, wane kalar halacci ne bai yi miki ba, ke inda baya sonki da gaskiya har yace yaji ya gani ya aminta zai aureki sanda ake hure masa kunne da cewar ke ƴar gaba da fatiha ce. amma saboda toshewar basira irin taki har ki iya
🏠