NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 116 of 323

aka in ƙarshen wata yayi". yace,"gaskiya nace ki faɗa min ba ƙarya ba". tai saurin ɗago ido ta kallesa kaɗan, sai taga ya rufe nasa idon ya kauda gefe ɗaya yana girgiza mata kai. "ina fa kallonki sanda kika fasa, intentionally kika jefar da shi a ƙasa har kina toshe hanci, warin me kika ji yana yi?". kawai sai ta fashe da kuka tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah zan biyaka nace". yace,"na haƙura kuma na yafe ba sai kin biyani ba, amma idan kin faɗa min reason ɗin da yasa kike toshe hanci akansa". bata san lokacin da ta saka ƙwayar idonta a nasa ba tace,"nawa ne turaren?". yace,"50k". jin ya faɗi kuɗin albashinsu gaba ɗaya tace,"warinsa ne bana so shisa". Turaki ya sauke dogon numfashi tare da sakin hannunta. kansa jingine da jikin gado ya kulle idonsa. Fillo dai nata kallon fuskar tasa, taji yace da ita,"bani ruwa zan sha magani". ta miƙe kamar wadda bata da ƙwarin jiki, ta isa ga inda taga ruwan ta ɗauko na cup ɗin dana jarkar, ta dawo ta ajiye a kan bedside. a hankali tace,"ga ruwan". ya buɗe idonsa tare da miƙewa zaune sosai. ya buɗe ledan magungunan da Zaytuna ta ajiye duka ya ciri iyakar wanda zai sha, Fillo nata kallon kwalayen maganin jikinta yay sanyi saboda hoton kidney da ta gani ajiki. ta ɗan kallesa kaɗan tace,"Adda Zaytuna tace baka ci abinci ba". shima ya kalleta kaɗan sannan yace,"nayi loosing appetite". tana jan yatsanta ɗaya tace,"ka daure kayi ko spoon biyu ne tukunna kasha maganin". idonsa a tsakiyar kanta yace,"akwai abincin anan ko sai kin ɗauko?". tace,"ga shi nan a flask". yace,"kaɗan zaki zuba". ta miƙe ta ɗauko flask ɗin da ta shigo da shi wanda Zaytuna ta bata. tana buɗe flask ɗin tace,"Adda Zaytuna ce ta dafa". hakan da ta faɗa sai yasa shi ɗan murmusa kuncinsa, tunaninta zai yi zaton ita ta girka yaƙi ci, bata san ma ko da ita ɗin ta dafa ba zaici. yana kallo ta zuba kaɗan ta miƙo masa. ya karɓa yayi spoon 3 ya ajiye. tace,"ka ƙara please, babu komai acikinka maganin ba zai maka aiki ba". idonta na kallon gefe tayi maganar, Turaki ya tsaya yana ta kallonta, kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa. ya ƙara spoon 5 akan wanda yaci tukunna ya ajiye, ta miƙo masa maganin ya sha sannan ta karɓi cup ɗin hannunsa ta ajiye. daga inda take a tsaye tace,"zanje in faɗawa Boɗejo ka tashi". ta faɗa tana shirin barin wajen, sai ta ƙara jin the same abinda yay ɗazu na kamo hannunta ya zaunar da ita gefensa. haka kawai Turaki ke ƙara jin jkinsa yayi sanyi sosai, still holding Fillo's hand har kusan 3minutes tukunna yay ajiyar zuciya ya saki hannun nata. ita dai ganin baya kallonta yasa ta sami damar kallonsa, da taga ya ɗan motsa kai sai tayi saurin ɗauke idonta. tana kallo within minutes ɗin da yasha magani kumburin jikinsa ya fara sacewa. Turaki ya duba agogon hannunsa, ya ɗauki wayarsa ya riƙe, wata ajiyar zuciyar ya sauke muryarsa a hankali yace,"you take care of yourself, zanyi tafiya but ba zan jima ba zan dawo, ba zan wuce 4days ba. if you need anything meet Zaytuna, be carefull with anything that will put you in trouble please". ita dai Fillo kanta na ƙasa idonta na kallon yatsunta, tana jin duk abinda yake cewa, tana jin maganar kamar da ita yake yi, sai dai tasan ba da itan yake ba, wataƙila kamar wancan ranar ne da yace thank you for saving my life tayi zaton da ita yake ashe waya yake yi. bata san dalili ba amma sai taji jikinta yayi matuƙar yin sanyi da jin zancen nasa, ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, sai taji ƙirjinta ya buga saboda yanayin yacca taga ƙwayar idonsa ta sauya. sai ta sami kanta da kasa ɗauke idonta daga ganinsa, tana kallo ya saki murmushin da ya tsaya a lips ɗinsa, kamar ita shima haka yake jan yatsun hannunsa. da taga ya ƙura mata ido sosai sai ta sauke kanta ƙasa ruwan hawaye na cika idonta without knowing the reason why. taji yace,"jibi zamu tafi, Hong kong zanje. ba zaki yi min adu'a ba?". duk da haka kanta na ƙasa tace,"da ni kake?". yace,"ni da waye a ɗakin?". tace,"to ai kaine mutum baya gane da shi kake magana". yace,"to da ke nake, adu'a nake so kiyi min naje lafiya na dawo lafiya sannan na dawo na tarar da ku lafiya". haka ɗaya sai taji wani iri da furucin nasa, yana maganar kamar wanda ke magana da matarsa, in same ku lafiya!, har da ita kenan?, to wace ita a cikin rayuwarsa?. sai yanzu taji wani bala'in tsoro ya kamata akan tafiyar tasa, voice ɗinta na fallasa kukan da take sonyi tace,"kai da wa zaku tafi?". yace,"ni da Bello". tai shiru kamar me dogon nazari kafin tace,"wannan abokinka ɗin me abin dariya?". ya ware idonsa tarr akanta yana mamakin maganartata yace,"ehh shi". tace,"daga kai sai shi zaku tafi?, zai iya kula da kai sosai?, ina nufin kamar yanda ba zai bari wani abu ya taɓaka ba?". tana tambayar taji tafin hannunsa akan haɓarta ya ɗago kanta, ya ɗago da fuskarta lokacin da hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa. ba tare da sani ba Turaki ya janyota jikinsa yana ƙarewa fuskarta kallo wacce hawaye k
🏠