kuɗaɗe ai min, ni tunda nazo ma ban ganta ba sai wannan baƙar nake ta gani tana suntiri, yanzu ma ita ta kawo min fura kuma ba zan iya sha ba gaskiya, da ganinta ba bafulatana bace irinmu. ni Allah yasa ma ba korar Fulani ɗin kuka yi ba, ni ƴa su aka koreta kuwa ba'a kyauta ba, yarinyar ga natsuwa ga hankali ga kyau da tarbiya, in kuwa an koreta to zama a dawo da ita gaskiya, dan ina son tausarta tayi masifar iyawa".
Zaytuna tace,"tana nan ba'a koreta ba. bata jin daɗi ne". Boɗejo tace,"Allah sarki ashe shisa, ni wannan ƴa ma da ƙyar in ba sikila bace, Allah dai ya bata lafiya, anjima sai ki rakani wajensu na dubota, wannan yarinya ai tayi, idan nazo biki ga ladabin da take min ba wallahi, ba irin sauran ƴan aikin ba da sunzo sun waye sai su koma maka kallon ɗan banza, yanzu dai ban ruwa a kofi inyi masa tofi sai ki basa maganin ya sha, wannan ciwon nasa ba ƙaunarsa nake ba".
Zaytuna ta ƙurawa Turaki ido sosai, wannan gajeran numfashin ke ɗaga hankalinta, fatanta ɗaya kar akai stage ɗin da kowa zaiji jiki ata dalilin ciwon. ta sauke numfashi sannan ta miƙe ta fita ta ɗauko faro ta dawo, a cup ta zuba ta miƙawa Boɗejo. zata ƙara fita Boɗejo tace,"tsaya ki basa ya sha, kin san ba sanin kan magungunan nayi ba". tace,"ya sami bacci ne, zanje na dawo".
Boɗejo tace,"to alhamdulillah indai yay bacci ciwon ma ai da sauƙi".
kusan awa ɗaya da rabi Boɗejo na tare da Turaki, yana ta bacci har zuwa lokacin, ita kuma tana gefensa cike da tausayinsa sosai. tana tayi masa adu'a iri iri, lokacin har ƙarfe shida da rabi na yamma tayi.
lokacin Fillo ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, Boɗejo ta amsa tana yi mata maraba.
ta shigo ta tsuguna tana gaidata, idon Boɗejo akanta tace,"sannu, aiko ga shi nan duk kin ƙara zaftarewa, kina cin abinci kuwa ƴar nan?".
kan Fillo a ƙasa tace,"ina ci". "to magani fa?". tace,"shima ina sha Boɗejo". "to Allah ya baki lafiya, kunje asibiti an yi miki tasa-tsai kuwa?".
Fillo ta girgiza kanta alamar a'a. Boɗejo tace,"wannan ai sakaci ne, bara Allah ya kaimu gobe Khalil ya kaiki asibiti su gwadaki, amma wannan jiki naki ke kam ai yana buƙatar binciken likita".
tace,"to Boɗejo na gode...dama Adda Zaytuna tace kina nemana".
"ehh kinga da tausa zaki yi min irin wacca kika min ranar nan, to kuma sai take ce min baki da lafiya". Fillo tace,"ai naji sauƙi, zan iya yi miki".
sosai Boɗejo ta tsaya tana kallonta da matuƙar tausayinta, tukunna tace,"a'a bari kya yi min gobe. yanzu dai ɗauko mopper ki goge ruwan nan kafin wannan marar lafiyar ya farka yaƙi sakkowa akan gadon".
jin ance mara Lafiya Fillo ta ɗago kai ta kalli kan gadon, gabanta sai da yayi mugun faɗuwa ganin yacca fuskar Turaki ta kumbura kamar wanda yayi mummunan accident.
Boɗejo ta ɗau mayafi tana faɗin,"bara naje in dawo, wurin Dikko zanje. in kin goge ki ɗan jira ina dawowa kar a barsa shi ɗaya, in kuma Zaytuna ta dawo shikenan. ni baccin nasa ma ya fara bani tsoro, Allah yasa dai lafiyar ce".
tana Fita Fillo ta goge tiles ɗin, ta nemi wuri ta zauna tana ta kallonsa, numfashinsa da ƙyar yake fita, tausayinsa take ji har cikin ranta tana yi masa aduar samun lafiya. Turaki ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ɗakin, Fillo ta taso da sauri tazo ta durƙusa a gaban gadon ta saitin da yake.
"barka da tashi, Boɗejon ta fita amma tace yanzu zata dawo".
ta faɗa tana kallon ƙasa, ta wutsiyar ido ta kalli yanda ya cije fuska ya miƙe zaune da ƙyar, Turaki ya dinga kallonta babu ƙiftawa, tun ranar da ta fasa masa turare rabon da ya ƙara ganinta, yau ɗin kuma kamar ta rame sosai.
ta gefenta ya sakko daga kan gadon ya wuce toilet without saying anything to her, kanta na ƙasa har sanda ya fito a toilet yana goge ruwan fuskarsa da towel ɗin hannunsa. ya dawo ya zauna gefen gadon tare da kwantar da kansa a jikin gadon, Fillo dai har sannan tana tsugune a wurin sai jan yatsunta take yi.
after some minutes ta miƙe tana ce masa,"zan kirawo Maama".
ta faɗa tana juyawa zata fita. sai taji ya riƙo hannunta dake aikin karkarwa, duk sai ta dabarbarce ta juyo a tsorace, idonta na ƙasa ta kasa kallonsa, dan lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa.
ya janyota ta zauna gefen gadon, tare da kamo ɗaya hannun nata ya riƙe sosai. can ƙasan maƙoshi taji yace,"kina so kiyi kwanan ɗakin daga ni sai ke?".
da sauri ta girgiza masa kai tana son ƙwace hannunta daga nasa. bayan ya sauke nunfashi yace,"to saita natsuwarki, bana son wannan tsoron".
ba ta ko sake yunƙurin motsi ba, haka shima yana riƙe da hannayenta har sai da yaji jikinta ya daina rawar sannan ya tallabi haɓarta ya ɗago da fuskarta yana kallonta.
"me ya ramar da ke acikin 5days?". ta girgiza masa kai kawai bata yi magana ba. ya sake cewa,"in tambaye ki zaki faɗa min gaskiya?".
tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya ɗan ɗaga muryarsa sama tukunna ta ɗaga masa kai da sauri.
yace,"faɗa min dalilin da yasa kika fasa min turare?". tuni ruwa ya kawo idonta tace,"ban sani ba ne, amma zan biy