NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 114 of 323

afin aurensa. Samha cikin zumuɗi da tsananin murna take faɗin,"ai Boɗejo babu zancen wani 1week, biki zamu fara from day 1 to day 10, kuma kowacce rana sai mun zubar da naira, sai doller tayi kuka ita kanta sai ta san ana bikin first born a gidannan". Nihal ta taso a kusa da Boɗejo ta dawo kusa da Turaki, ta kamo hannunsa tana cewa,"please Hammah ka sama mana Anty kaji, Allah mun ƙagu ayi bikinka, Allah duka burinmu na kan wannan ranar Hammah, I feel like your wedding day is the first wedding in the world". shima ya riƙe hannun nata yana kallon innocent face ɗinta yace,"to kun zaɓa min matar ne?". dai-dai nan Samha ta taso itama ta zauna gefensa,"ka yarda mu zaɓa maka Hammah?, akwai friends ena da friends Zaytuna da yawa da suke sonka, duk basa ƙasar nan, gasu kyawawa masu class, sai wacca muka ɗaukar maka". tana kallon Zaytuna tace,"ina wannan balarabiyar ƙawar tawa da mukai vedio call ranar nan?, kin tuna ta?, basu dace da Hammah ba don Allah?". bata jira cewan Zaytuna ba koma garesa tana ƙara cewa,"Hammah ka yarda muyi maka zaɓi?". ya kalleta sai kuma ya kalla Zaytuna wadda ke ta kallonsa da tarin murmushi. kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace,"kuyi adu'a Allah ya kawo ta gari, aure ai lokaci ne". Boɗejo tace,"a'a lokacinka fa yayi kai harma ya wuce tuni, dan dai kawai Uwarka da Ubanka sun zuba maka ido ne, sai abinda kake so za'ai, yo wannan gata ai ba gata bane. kai in baka san mutumcin mutum aure ba ai su sun sani, to ni dai ina gajiya sai na haɗaka da duk wadda naga dama, Allah na tuba ƴan mata gasu nan birjik a danki...kuma dai ma ni in faɗa maka yar gida muke so jinin sarauta ba bare ba, ah tou karma lokacin da hankalinka zai dawo jikinka kace zaka ɗauko wata can daban, ina ga Madina ce kawai ta shigo zuri'armu a bare". shi dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujerar. Nihal ta daɗa riƙe hannunsa sosai tana faɗin,"can't wai to see your wedding day Hammah, wayyo Allah wa ya ganni da Sister inlaw". ta faɗa cikin wani irin expression tana faɗawa jikinsa. ranar a part ɗin Boɗejo suka yi lunching, shi Turakin ma bai iya cin komai ba, yanayinsa kamar dai wanda bai cikin natsuwarsa. after la'asar ma da ya dawo daga masallaci part ɗin Boɗejo ya koma, lokacin da ya shiga bedroom nata tana waya da Inna Falmata. ganin shigowar tasa yasa tace,"to sai anjima Falmata, a dai ci gaba da aiki me kyau don Allah, kinga acikin sati huɗu yau munci kwana biyar, to shi haka lokaci yake sai dai idan ba'a saka shi ba, nan dai nan sai kiga yazo". daga haka ta kashe wayar ta ajiye a kusa da ita, ta kalli kan gadonta da Turaki ya kwanta, he don't know why yake jin jikinsa yayi sanyi, tunda Bello yace masa zasu yi tafiya tare yake jin wani feeling mara daɗi a tare da shi, and for the first time da yake jin kamar zai rasa rabin jikinsa, Boɗejo ta kai hannu ta taɓa ƙafarsa taji zafi like zazzaɓi ne ke shirin kamasa. tai salati tana faɗin,"baka da lafiya ne Turaki?". ba tare da ya buɗe idanuwansa ba yace,"lafiyata lau, kawai ina jin ba daɗin yanayina ne". Boɗejo tayi saurin tashi tsaye,"a'a baka jin daɗi ai yana nufin baka da lafiya, tun ɗazu dama na lura da yanayinka, to da yake kai ɗin me ƙauran baki ne ba zaka fito kace baka da lafiya ba sai dai ciwo yay ta cinka". dai-dai nan Ɗausiyya ta shigo ɗakin riƙe da ƙwaryar fura a hannunta. ta shigo da sallama ta nemi wuri ta ajiye, zata juya Boɗejo tace,"kinga garzaya da gudu ki kira min Zaytuna a, kice tazo da sauri Turaki babu lafiya. bance ki bari Uwassa taji ba balle tazo ta ɗaga min hankali da bala'ƴaƴƴan kukanta anan". in few minutes Zaytuna ta shigo ɗakin hankalinta a tashe, kai tsaye inda yake kwance ta wuce. kamar zata yi kuka ta taɓa jikinsa da yay zafi rau. "Hammah wake up mu tafi asibiti". ya buɗe idonsa da sukai jajir ya kalleta. ahankali yace,"ɗauko drugs ena". yana faɗa ta miƙe cikin sauri ta fita, bata jima ba ta dawo ɗakin jikinta sai rawa yake yi, tuni kuma hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa, bata ƙaunar wannan ciwon nasa na kidney ya tashi, idan ya tashi sai sun gama fidda rai da shi tukunna lafiya take samuwa. Boɗejo ta fito daga toilet a lokacin, tana kallon Zaytuna tace,"ciwon ne ko? ai tun jiya nake lure da shi tunda naga ƙwayar idonsa da kuma yacca ya ɗan kumbura ɗin nan, to kin sansa da ƙarfin halin jaraba, bai san cutar kansa yake ba". Zaytuna na hawaye tace,"inje in kira Maama?". da sauri Boɗejo ta girgiza kai,"a'a sam bakinki alaikum, da yardar ubangiji yana shan magani zai sami lafiya. ko kin manta itama bata da lafiya ne?, jiya likita da ya aunata yace jininta yayi mugun hawa sama, so kike tazo ta mace mana lokacinta bai yi ba, a'a bari tukunna dai a ɗaura aurensa ta gani tana raye". ta zauna kan kujera tana faɗar,"dan Allah kinga kwaɗa kira ɓangaren masu aikin nan wannan yarinyar Fulani tazo ta matsa min ƙafata, naga ta iya matsa ƙafa, kwanaki da tayi min kyace tausar inji irin wacca Hashim ke biyan uban
🏠