NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 113 of 323

sai ta kasheku". da gaske Fillo ke ta maganarta, bayan tafiyar Sabira Maijidda tace mata,"yau ba zaki je aiki ba?". Fillo tace,"tun ranar dana fasawa Turaki turarensa nake shakkar komawa, so nake a bamu albashi tukunna sai na siyo masa tsiyarsa. shisa naiwa Maama ƙaryar banda lafiya". Maijidda tace,"to yau dai Dr Yusuf yace zai zo, ki tashi mu san abinda zamu yi masa". Fillo ta kalleta ta taɓe baki,"ni ba abinda zanyi tunda ba gayyatarsa nayi ba". sukai shiru for some seconds sannan Maijidda ta katse shirun da faɗin,"Fillo Amir fa?, ya kamata ko me yayi miki kiyi haƙuri ke kam, tsakanin harshe da haƙori ma an saɓa, kuma shi dama zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa ne. zatonki zaki samu masoyi kamar Amir?, karki zama butulu ki mance da irin halaccin da yay miki a rayuwa, ni dai dan Allah ko mene yayi miki kiyi haƙuri ki manta, tunda ni kinƙi ki faɗa min". Fillo tai guntun murmushi na takaici,"shi bai faɗa miki abinda yayi min ba?". Maijidda tace,"ni ba abinda yace min, kuma bana so na sani tunda har ke kika kasa faɗa min, abinda nake so kawai shine ku dawo daidai...". Fillo tai saurin tarar numfashinta,"har gaban abadan, igiyar soyayyar dake tsakanina da shi na datseta har mutuwa, kije ki faɗa masa hakan, in ma yana wani lissafin rayuwa tare da ni ne to ya daina deceiving kansa, domin ni Halima na barsa har gaban abadan, wallahi ko Amir ne kaɗai ya rage namiji a duniya ba zan auresa ba". sai kuma ta fashe da kuka,"idan har da gaske Amir sona yake tsakani da Allah ba zai taɓa goranta min ba, duk da banga laifinsa ba. laifin Hayyo ne da ya sheganta ni da bakinsa, in ace Hayyo bai kira ni ƴar Zina ba yau da Amir bai buɗi baki yace min ƴar gaba da fatiha ba...". furucinta na ƙarshe yasa Maijidda tayi zumbur ta miƙe,"kika ce me?, Amir ɗin ne ya faɗi haka?". cikin matsanancin kuka tace,"Allah shahida idan nayi masa ƙarya Allah kar ya ɗagani anan wurin, kije ki tambayesa. daga nace bana so naje gidansa babu kayan ɗaki gudun gori shine ya tashi ya juya min baya yana faɗa min wai kar na manta ni ƴar zina ce, saboda haka ko ba'a min gorin kayan ɗaki ba ana iya min gorin an haifeni without marriage. Maijidda wanda nake so da aure ya faɗa min haka tun ban auresa ba, just imagine anyi auren, waɗannan kalamai kike tunanin zai dinga gaya min?". Maijidda ta sauke numfashi da matuƙar mamakin ace Amir ne zai faɗi haka. ta rasa abin faɗa saboda tayi matuƙar girgiza, idonta kawai Amir ɗin yake hango mata, bata taɓa tsammanin zai iya faɗawa Fillo haka ba saboda bala'in son da yake yi mata. Fillo dai kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa, har sai da wayar hannun Maijidda tayi ƙara ta ɗaga suka gaisa da Dr Yusuf yace musu ga shi a waje, sannan Fillo ta goge hawayenta ta shi suka tafi bayan ta wanke fuskarta. *** A ɓangaren Bello, Turaki da Khalil. zaune suke a parlo bayan sun kammala breakfast, kowanne da takardu a gabansa da kuma biro, suna tattaunawa akan batun sabon company da Baffa yace za'a ƙara buɗewa. Khalil na kallon takardar dake gabansa yace,"anawa tunanin gaskiya gwara a buɗe na sarrafa kayan miya a maida su na gwangwani ko leda. tunda shine kamfanin mafi ƙaranci da muke da shi a nigeria, kuma ina ganin hakan za'a sami abinda ake so fiye da tsammani". Bello yace,"view ɗinka yayi kyau, sai dai yanzu mu fara kammalawa da wannan da Maama tace". Turaki ya kalli Bello tace,"me Maaman tace?". Bello ya duƙa yay rubutu jikin takardar gabansa tukunna yace,"Company ɗin dake Lagos da Baffa yace a siyar, tace ba za'a sayar da shi ba za'a maida shi na fulawa, Shine batun da nai muku jiya cewar zanje Hong Kong, saboda injinan da za'a siyo na yanda za'a sarrafa fulawan. but ina ganin tafiyan ba ni ɗaya zanje ba da kai zamu tafi Turaki, zanyi convincing Maama mu tafi tare. tunda tafiyan jirgi ne ba wai a mota ba, becouse kai ka fini sanin kaya masu kyau, idan ni ɗaya ne za'a iya haɗani da fake one". Turaki ya ɗan ciji leɓensa kaɗan sannan yace,"why not su turo da kayan kawai ba sai anje ba". Bello yace,"yanda ma fake one's ɗin zasu fi zuwa kenan. Maama already ta riga taga hotunan su, dan ko launching nasu ba'ayi ba, shisa tace naje ayi a gabana, so ta re da kai dai zamu tafi". Khalil yace,"shikenan Turaki Flour Mills ya tabbata kenan, dan nasan hakan za'a saka tunda Maama ce ta kawo idean". Bello da sigar tsokana yace,"ah haba dai sai kace shi ɗaya ne ɗa, ai sai dai a haɗa sunan mu duka". Turaki ya taɓe baki ya miƙe tsaye yana faɗin,"i don't think i will go with you, kayi tafiyanka kawai ko kuma kuje da Khalil. beside; Sameer ma na Hong Kong ɗin kana iya samunsa acan". Bello yace,"aiko dole sai kaje, ka zama cikin shiri kawai Malam, coux daga nan ma tictiket ɗinmu zanje amsa". ba tare da Turaki ya ƙara cewa komai ba ya fice daga parlon. direct part ɗin Boɗejo ya nufa, acan ya tarar da sisters nasa duka a zaune sun saka Boɗejo a tsakiya sai hira suke, sai bayan ya zauna kan kujera ya fahimci lissafi suke tayi, liss
🏠