NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 112 of 323

ya tsaya bayan da ta ɗau tsayin mintuna tana bawa zuciyarta haƙuri da kalar tata ƙaddarar. tana riƙe da hannun Maijidda tace,"ina key ɗin motar Turaki dana baki ajiya?". Maijidda tace,"yana ƙasan kayanmu. amma Fillo ba kya tsoron garin mayarwa a ganki". tana kallon wani side na daban tace,"idan ma an ganni there is no problem, and ba ma komawa ɗakinsa zanyi na ijje ba, Maama zan kaiwa". Maijidda tayi ajiyar zuciya tace,"gaskiya Hajiya Madina ta dabance, ni tunda kika ban labari na rasa ma abinda zance, nayi matuƙar girgiza da lamarin". Fillo tace,"ni kaina farko ban yarda ba sai da kunnuwana suka jiye min...kiji fa wai a tsinke burkin motar, wai sai ta kira shi tace yaje ya ɗaukota a anguwa motarta ta lalace, wai in ya taho sai me tirela ɗin yasha gabansa kawai yabi takansa". Fillo ta rumtse ido gam tana jin kanta kamar zai buga. "Maijidda wannan masifa har ina?, ace ka dinga harin jinin ɗan'uwanka?, me ya yi musu?, Allah da ƙyar ƙafafuna suka iya ɗaukata suka kai ɗakinsa, ke yanda na tafi a rikice ko a hannunsa naga key ɗin motar sai nayi kokawa da shi na ƙwace, ko kuma na faɗa masa komai kowa ya huta, saboda Hajiya Madina yasa kawai ban faɗa masa ba amma wallahi nayi niyya, to kawai dai ina tausayin halin da Maama zata shiga ne. kuma nayi rashin dabarar na faɗa mata ma tun a daren, dan da wuya in babu spare key da zai ce zai yi amfani da shi". Maijidda tace,"to Allah dai kar ya tsare shi daga dukkan shirinsu". "amin". Sabira wacca itama jika ce a wajen iya Hanne abokiyar aikin su Yami tazo wajen ta zauna. taci kwalliya daga yanda ta riƙe jakar hannunta kasan shirin fita tayi. tace da su Maijidda,"nan kuka yo ashe?". Maijidda tace,"ehh, nan ɗin yafi iska". Sabira tace,"duk yanda akayi ba'a sanar da me gidan nan wutar ɓangaren nan ta lalace ba, ji fa kwana huɗu muna cikin duhu da zafi". Maijidda tace,"ita kanta Hajiyan bata sani ba, kwana biyu basa zama. amma naji Yami tace sun faɗawa incharge zai bar mata saƙo". tace,"gwara haka, cikin daren nan duk sai ka kasa bacci wallah, ga zafi ga sauro". cike da tsokana Fillo na kallon Sabira tace,"uwar yawo sai ina aka dosa?". Sabira ta ƙara turo ture kaga tsiyanta gefe ta tauna cingom dake bakinta, bayan ta karkaɗa ƙafa tace,"ni zan so ma ki rakani, dan wannan shirin nawa da kika gani bana wasa ba ne". Fillo tayi ƴar dariya tace,"rufani ki saya, ke dai da yawonki amma ba dani ba, sai dai ko Maijidda gata nan itace uwar yawo irinki". Maijidda tace,"balle ma ba zuwan zanyi ba". Sabira tace,"ko zaki je ma ba zaki bini ba dan abinda zanje yi ba da irinki sanyi ƙalau ake zuwa ba, dan sai ki lalata min aiki. Fillon dai itace daidai da tafiyata". Fillo tace,"wai ina zaki haka, naga sai wani faman cika kike kina batsewa". Sabira tace,"ruwan masifa da bala'i zanje na juye". ta jijjiga kanta tana yin ƙwafa me ƙarfi,"ai na rantse yau idona idon kishiyar Anty Jummai sai na rotse mata kai". sai ta karkato tana facing su Fillo da kyau ta shiga basu labarin kishiyar Yayarta. "wai fa kawai dan Anty Jummai tana da haƙuri, kuma ita ƴar talakawa ce shikenan kullum sai cin kashin da kishiyar taga damar yi mata. tayi ta zaginta wai ƴar matsiyata kyace ita ubanta haifarsa akayi da kuɗin, ga shegen haɗa makircin tsiya tayi ta jawa Anty Jummai Faɗa a wurin me gidan, jiya Allah ne ya taƙaita bai saki Anty Jummai ba". Fillo da tausayawa tace,"kishiya dai kowacce kala ce bata da daɗi, Allah kai mana tsari da sharrin kishiya dan ni har ga Allah a duniyata inda abinda na tsana bai wuci kishiya ba wallahi". ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah,"ubangijina na roƙeka ba don nafi kowa ba Allah karka sa mijin da zan aura yay min kishiya, ko na shiga na tarar ko a shigo a tarar da ni". Maijidda tace,"ki dai roƙi Allah ya haɗaki da abokiyar zama ta gari shine kawai, ba wai batun kar a miki kishiya ba, in haka ne ina kike so akai sauran matan?". zuciyar Fillo na sosuwa tace,"mu bar zancen nan kawai, zan iya haɗiyar zuciya a wurin nan. kishiya fa! ni Fillo da kishiya?, to ta ina ma za'a fara zaman?, in ke ganin abinda nake so tare da wata?, Allah karka nunan wannan ranar. Maijidda cewa fa kike wai kishiya ta gari, ke a duniyar nan har akwai kishiya ta gari?, hmmm yarinya baki san wace kishiya ba, amma kishiya babu ta kirki, ba sai na faɗa miki ba tunda kin riga kin san tarihin gidanmu, kin san baƙar wuyar da na sha hannun kishiyar uwa...ke Allah ya tsinewa kishiya kowacce kala ce ma". Maijidda tace,"to Allah ya kyauta". Sabira ta miƙe tana faɗin,"bari naje, dan zuciyata azalzalata kawai take yi". Fillo tace,"je ki wallah ki ƙwatarwa Yayarki ƴanci, ki tsaya tsayin daka karki fito a gidan nan sai kin nunawa kowa Antynki na da gata, ke idan ta kama ma kiji wa Anty Jumman ciwo ki fito waje kina kururuwa, waye bai iya makirci ba ai sai in bai so ba, karki yarda ki taho sai an garƙame shegiya a cell, ke inta kama ma ki ɗau wuƙa ki saka a hannunta kafin akawo ɗauki, ana shigo kice gata can da wuƙa wai duk
🏠