NOVEL SHARES -
fa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa.
tace,"maza kira min sarkin gida". fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube agaban Boɗejo tace,"ɗau waya ka kira min Hakimi".
Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. yay saurin miƙawa Boɗejo. ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa tace,"kana jina?".
a ladabce yace,"ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". tace,"amin, Allah yayi maka albarka...dama magana zanyi da kai".
kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi yace,"tom shikenan, ɗazu ance min kin fita, gidan Dikko zanzo ko fada?".
tace,"a'a yi zamanka akan kujerarka. dama batu ne na aure nazo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham, ba kuma na so ya wuce wata guda tunda da arziƙinmu, wata gudanma saboda zan gyara jikata ne banda haka cikin sati ɗaya za'ai komai a gama".
Hakimi yace,"tom shikenan ranki ya daɗe, za'ayi yanda kika ce. Allah ya tabbatar da alkhairi".
tace,"amin ya Allah". da haka suka yi sallama, da yake a handsfree ta saka duk conversation ɗinsu su Mai Martaba sunji.
"da akwai wanda zai ja ne?". ta faɗa tana kallon su duka. a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"a'a, Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi". tana nuna musu fushinta na gardarma da suka yi mata a farko tace,"kai Dikko ka kira min Falmata yanzu a waya".
Baffa ya ɗau wayarsa ya kira Falmata ya miƙawa Boɗejo, sallamar Falmata kawai ta amsa tace da ita,"anjima za'a kawo Ilham gidanki, ki gyarata gyara na ban mamaki Falmata, gyaran da ba zai sa Turaki ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba har mutuwarsa, irin gyaran da ba zai so Ilham ta matsa a kusa da shi ba".
Inna Falmata ta amsa da,"tom ranki ya daɗe".
Boɗejo ta dubi Mai Martaba bayan gama wayar tace,"sai kuma me?".
ya rissinar da kansa yace,"ya kamata a sanar da Fulani Azima da kuma Madina".
Boɗejo ta haɗe rai tace,"ashema ba so nake auren ya tabbata ba. gwara ma in Madina kace, amma wace wata Fulani Azima?...to maganar aure dai cikin sirri nayi ta, ko yaran ba zasu sani ba sai ranar ɗaurin aurensu, magana daga ni sai ku nayi ta, idan naji ta a wani waje kuma wallahi tallahi akwai Allah".
tana gama faɗar hakan ta miƙe. "Dikko tashi muje gidanka zan wuce".
*Comment, Share and Vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*27*
Fillo ce zaune akan dakalin bayan ɗakinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta.
ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi".
Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa.
"kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala".
Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta.
cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne ɗan halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne ɗan halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daɗi daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da ƴar zina alhalin akan shimfiɗar sunnah ya samar da ni...".
muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka.
"Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce nayi rashin sa'ar uba, ta dalilin baƙin cikinsa har yau ban san inda Ummina take ba, bamu san ina ta tafi ba, ki tayani adu'ar duk inda take Allah yasa tana cikin kariyar ubangiji, jikina na bani Ummina bata rasu ba tana raye, amma Kaka wai sai tayi ta ce min Ummi ta mutu".
kukanta ya ƙaru sosai, kuma daga ita har Maijiddan kukan suke yi. "Maijidda i wish ace ana sauyawa tuwo suna dana sauya Hayyo a matsayin ubana, i wish Hayyo is not my father, I wish I could take revenge for what Hayyo did to me and my mother. but i can't, i can't do that Maijidda, duk da lalacewarsa i still feel his love in my heart".
da ƙyar kukan Fillo