in nunfashinta har kusan sarƙewa yayi, tana tafe tana lumshe ido har ta kusa zuwa ɗakin Yami. aina ta samo wannan ƙamshin to?, ƙamshin da zata iya ce duk duniya babu ƙamshin da ya kaisa daɗi.
idanuwanta a lumshe ta ƙaraso ƙofar ɗakinsu, lokacin Maijidda ta fito daga ɗakin suka yi karo da juna. Maijidda ma taja hanci tana shaƙar ƙamshin tare da cewa,"kai Fillo wannan ƙamshin fa?".
****
Boɗejo dake zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba tace,"ah tou ni ɗin dai na gama magana...idan kuma kun lalace ne to sai naji, amma batun auren Ilham da Ɗan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon me sama".
Mai Martaba ya sauke numfashi yace,"amma Hajjah...". da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne me shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko?, kasan Allah karka bari raina ya ɓaci akanka, ya nazo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da kasan bana so".
cikin kwantar da murya Mai Martaba yace,"kiyi haƙuri".
Boɗejo ta ƙara haɗe rai tace,"ka riƙe haƙurinka. muyi batun da ya kawoni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai inji".
Baffa ya ɗago kai ya kalleta yace,"balle ma kin isa Boɗejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tunda bamu san ba ko su yaran nan zasu so haɗa su auren da za'ai".
Mai Martaba yace,"abinda nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abinda ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar tasu muddin babu soyayyar junansu, amma kuwa idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba".
Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin tace,"na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe?, kai kasan a yanda akayi aurena da ubanku kuwa?, tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba...shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci akayi ba, amma kana batun wani idan basa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi?, ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu!, maganar nan naka har ga Allah yayi min zafi, to karka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu me mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi...tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa?, kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata me baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa jinina ya hau".
Mai Martaba zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"a'a dakata, dakata ba sai kace komai ba. ɗaga waya kawai ka kira min Hakimi yazo yanzun nan, ban sani ba ko haɗe kanku kuka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata".
Baffa ya tausasa murya yace,"ba bijire miki zamu yi ba Boɗejo, zamani muke so ki duba. kuma muma fa bamu ce ba za'ayi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi".
Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu tace,"to bara kaji Dikko, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kirani akai min zancen aurenmu da shi...ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai inje fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa?, saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da akayi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. yo da ike ni me biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban naku, hasalima shi tausata yake yana cewa muyi haƙuri mubi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to dana aure shi Dikko mutuwa nayi ko me?, gashi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. sai akan ƴaƴanku zaku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham yayi, to banda dai rashin tsoron Allah irin naku ina ku ina cewa baya sonta?
ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. na tabbata babu abinda zai sa yarannan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa to amma shima na san na ƴan mintina ne tunda yana da ladabi, kana cewa haka kake so ba zai ja ba zaice ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne".
daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta ta