NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 109 of 323

muryar kukan da bai barta ba tace,"kayi haƙuri dan Allah". Turaki ya daki gefen gadon yayo kanta gaba ɗaya yana sakar mata tsawa,"nace when did you wakeup?". da bala'in tsoro tasa hannu ta kare kanta jikinta sai kyarma yake yi, cikin rawar murya tace,"ban jima ba". bai ƙara bi ta kanta ba ya tashi ya fita, after few minutes sai gashi ya dawo riƙe da wani ledan daban. ya ajiye akan gadon ba tare da ya kalleta ba yace,"ci abinci". tsananin tsoron yanayinsa da ya rikiɗe bata tunanin zata yi masa musu, don haka da azama ta sauka a gefen gadon, hannu na rawa ta ɗauki plate ta buɗe coolern ta zuba abincin ta ajiye a gabanta. tunda ta zuba taji idanunsa akanta, hakan yasa ta kasa sakewa, kuma ta kasa ɗagowa ta kallesa balle ta nemi izininsa taje ta wanke hannu, shi kuwa ciwon hannunta kawai yake kallo da Zaytuna ta ƙara dressing. sai da ta ga ya yunƙura zai tashi sannan tayi saurin cewa,"zan wanke bakina". yay gaba abinsa bayan yace,"karki je ki wanke kici a haka". yana fita a ɗakin ta miƙe ta shiga toilet, bakinta ta wanke da macline sannan ta ƙara wanke toilet ɗin tukunna ta fito. har lokacin kuma hawaye bai bar sauka a fuskarta ba, ita tsoron da take yi kar Maama ta nemeta, duk da tasan zuwa yanzu Kaka na can tana jiran dawowarta. ba zata iya cewa ba zata ci abincin ba don tana jin yunwa sosai, ga shi kuma girkin ya burgeta, ƙamshinsa kawai taji tasan girkin Adda Zaytuna ne. tana cikin ci taji ƙarar buɗe ƙofa, tun da ta hangosa ta wutsiyar ido tayi mugun tsorata da sauri ta ajiye spoon ɗin ta kama jan yatsunta. ya dawo ya zauna a inda ya tashi, ya kalla plate ɗin abincin tukunna ya kalleta yaga yanda take ta raba idanu, yaja tsaki cike da takaici. zai ɗaga murya sai kuma yay controlling kansa, calmly yace,"du ka za ki cinye, ke kika zuba ai ba wani ya zuba miki ba...finish eating and take your drugs". ya faɗa yana jefata mata ledan magungunan. ta ɗan kallesa taga baya kallonta tace,"idan na cinye to zaka barni na tafi?". yace,"idan kin biyani abinda kika fasa min ba. ko an faɗa miki da kuɗin banza aka saya". tace,"insha'Allahu zan biyaka amma ba irin wancan ba, sai dai wani daban, Kaka bata da kuɗin wancan". yay mata shiru, tana ɓata rai tace,"kuma ni lafiyata lau ai". ta faɗa tana ture ledan maganin daga kusa da ita. sai da ta cinye abincin da ta zuba tass sannan ta miƙe ta wuce toilet ta wanko baki ta dawo, ta ɗauke plate ɗin ta ɗora akan table. kamar bada ita yake ba yace,"ba da kuɗin banza na sayo su ba, ɗauki kisha". ba don komai ba sai saboda gudun kar ya sakar mata tsawa ko kuma yay mata wannan kallon da bata so tayi saurin ɗaukan maganin tasha, tana sha tana hawaye, bata miƙe ba sai da taci kukanta duk yana jinta amma bai ko kalli inda take ba. bayan ta gama kukan ta zagayo ta gabansa ta zube duka gwiwanta biyu a ƙasa, ta haɗa hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tace,"dan darajan Allah kayi haƙuri, kaga dare yayi Kaka na can tana jirana. kuma nasan Maama zata neme ni". ta faɗa sabon kuka na taho mata, amma sai ta danne shi. Turaki yaci gaba da kallon wayarsa, kamar ba zai yi magana ba can sai taji yace,"thank you for saving my life which you have done so many times. but i want to ask you something and please you tell me truth". furucinsa ya bata mamaki matuƙa, how does he knows that?, zuciyarta ta ambatar mata sunan Maijidda, ita kaɗai tasan wannan sirrin nasu. to amma!...sai ta ɗago kai don kallonsa ƙirjinta na bugawa, gani take kamar maganar da yay ba da ita da yayi ba, ganin waya ce kare a kunnensa yasa ta sauke dogon numfashi, hakan ya shaida mata ba da ita yake magana ba. cikin wayar da Turaki yake da Bello ta faki idonsa ta ƙarasa zaro key ɗin da ya leƙo ta aljihunsa ta yanda ba zai ji ba, ga mamakinta harta miƙe sai taji ya riƙe hannunta gam. ta rumtse ido kamar zata yi kuka, ganin za tai magana yay saurin ɗora yatsansa saman lips ɗinsa alamar tai shiru. hakan yasa tai gum tana bo ne fuska. bayan ya gama wayar ya dubeta, tai tsaye ta rufe idanuwanta gam ko motsi taƙi yi tunda ya riƙetan. tsoronta Allah tsoronta kar yaga key ɗin motarsa da ta ɗauke, dan a second fitarsa ta ɗauke tasa acikin rigarta. taji yace,"ni zan shanye sauran maganin?". ta buɗe ido ta ɗauki ledan da yay mata nuni da shi, cike da ƙaguwar ya sakar mata hannu. tace,"wa zan kaima?". yana sakin hannunta yace,"ki wuce da shi". tace,"ina?". yace,"duk inda kika ga dama". tana hararsa ta ƙasan ido tace,"ƙofan a rufe yake". ta faɗa tana yamutsa fuska. ya miƙe yaje ya buɗe ita kuma ta fice da gudu, wannan gudun nata kuma yasa shi sakin gajeran murmushi yana girgiza kansa. cikin sanɗa ta fita daga side ɗin nasu gaba ɗaya, ko tsayawa ba tayi ba a compound tayi ɓangarensu dan bama taso su haɗu da Maama a yanzu, sai safiya kuma. sai after take jin wani mugun ƙamshi me shegen daɗi na binta, ta dinƙa jan hanci tana so taji daga ina ne, sai da ta shinshina jikinta taji ƙamshin a jikinta yake. tsabar daɗin ƙamsh
🏠