NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 108 of 323

bata so?. bata taɓa jin taji haushin kanta a wani abu da ta aikata ba sai a yau. ta san turaren me tsada ne kamar yanda ya faɗa, to yanzu da wanne kuɗin zata biyasa?, shekaranjiya Kaka ta kwashe ƴan kuɗaɗenta ta bayar an siya tumakin da suke kiwo. kawai sai ta ƙara durƙushewa a gaban mudubi tana kuma sakin kuka, ko na misƙala zarratan Turaki baya da tausayi kuma baya da imani, sam baiyi gadon mahaifinsa ba, kuma bai yi gadon mahaifiyarsa ba kamar yanda taji labarinta a bakin Maama ɗazu. tana cikin wannan kukan ne taji an buɗe ƙofar, ko bata ta ɗago ba tasan shine, hakan yasa taƙi motsawa, saboda so take yi ta taushi zuciyarta gudun aikata abinda zata zo tana dana sani, dan tasa a ranta sai Turaki yasan ya kulleta a ɗaki. yau zata masa abinda zai sa ya koyi haƙuri da yafiya, in ba haka ba kuma ta barsa da sharrin waɗanda suke neman rayuwarsa, wannan ma kaɗai ya isa ya shiga hankalinsa. Turaki ya shigo ciki yana mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙara saka key, zaton Fillo bai saka key bane, hakan yasa ta miƙe da azama cikin dabarar data tsara cewar zata bige shi ta buɗe ƙofar ta fice da gudu, irin gudun da ba zai iya kamota ba. kuma ba zata ƙara yardar ma tazo ɓangarensu aiki ba sai dai in Ɗausiyya. Turaki ya tsaya yana kallonta da mamakin yanda ta wani taso a sukwane kamar wacca taga mugun abu, ya ɗan matsa zai bata hanya gudun karta bigesa daidai nan ɗakin ya gauraye da uban duhu sakamakon ɗauke wuta da akayi. babu shiri Fillo ta cakumo Turaki ba tare da sanin inda ta nufa ba tana kurma uban ihu tare da ƙanƙame shi. "wayyo Allah nah, na shiga uku, Kakata". ihun take yi tana ƙara ƙanƙameshi kafin kuma ta shiga roƙonsa,"dan Allah ka kunna fitilar, wallahi ba zan ƙara ba, na bi Allah na tuba insha'Allahu ba zan ƙara yi maka ta'adi ba, kuma zan biyaka turarenka amma kaima Allah ka kunna hasken bana son duhu". maganar take tana ƙara cikwikwiye shi, Turaki yasa hannu ɗaya ya riƙeta sosai ajikinsa, ya duƙa ya ajiye ledar hannunsa sannan yasa ɗayan hannun a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kunna tourch. idanuwanta a rumtse suke gam hakan yasa ba zata shaida hasken fitalar wayar ba, kuma har lokacin bata bar roƙonsa ba akan ya kunna fitilar tana ƙara shigewa jikinsa. ya leƙa fuskarta ya kalla yanda duk take a tsorace, sai haɗa uwar zufa take, ya girgiza kai kawai yana mamakin bala'in tsoro irin nata. yayi ajiyar zuciya a daidai lokacin da wutar ɗakin ta dawo, yay guntun tsaki na ɗan jinkirin da aka samu before a kunna generator. shi kansa baya son wannan ɗauke wutar duk da ba kasafe aka cika ɗaukewar ba, dalilin da yasa ya dami Baffa kenan akan kawai a haɗa transformer a gidan a huta. cikin sheƙar kuka Fillo ta ƙara cusa kanta cikin ƙirjinsa wanda tuni maɓallin wajen ya cire. karan hancinta na gogar fatar ƙirjinsa tace,"dan darajan Allah Turaki kayi haƙuri, idan na kuma yi maka ta'adi kayi min duk abinda kaga dama, ni ba da gangan na fasa maka turare ba suɓuce min yayi a hannu. kai ma Allah da ma'akinsa ka kunna hasken zan biyaka". "kinyi alƙawarin zaki biyani?". da sauri ta ɗaga kanta,"ehh zan biyaka amma ba irin naka ba". guntun murmushi ya sauka akan leɓensa yana bin tsakiyar kanta da ɗankwali ya zame da kallo. kansa ya ranƙwafo saitin kunnenta yace,"to ki sakeni sai na kunna hasken". da sauri ta girgiza masa kai,"a'a ka kunna a haka, idan na sakeka wani abun zai kamani". yace,"wanne abu ne zai kamaki?". Fillo taji kamar tasa masa duka, sai kawai ta daɗa sa kuka tana cewa,"ni dai ka kunna don Allah, duhu tsorata ni yake wallah". ya kai hannu kamar zai shafi gefen fuskarta sai kuma ya fasa yace,"to idan na kunna ta ina zaki sani bayan kin rumtse ido. ki buɗe idonki tuni aka dawo da light". jin hakan yasa a hankali ta shiga buɗe idonta, sai da ta tabbatar idan ta buɗe duka idonta zata ga haske sannan ta buɗe, ta buɗe idonta duka tana saukewa ajikinsa. take ta zabura ta sake shi tana fita a jikinsa tare da ja da baya, sai aikin rarraba idanuwa take yi. sai kuma tayi saurin dafe kanta da taji yayi mugun sara mata a lokaci ɗaya, jiri ya nemi ya ɗebeta ya yasar, Turaki daya lura da hakan yay saurin kamo hannunta ya janyota ta dawo gabansa, ƙarar bugun ƙirjinta tarr a kunnensa. yana riƙe da hannunta da take son ƙwacewa ya sunkuya ya ɗauki ledar, ya jata suka zagaya zuwa ɗaya side na gadon. cikin fargaba da tsoron matakin da zai ɗauka akanta na yadda tasa rigarsa ta cikwiwiye kamar an ƙwato a bakin jaki. idanuwanta sukai rau-rau tasa hannu tana ture nasa tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba". bai ko kalleta ba fuskar nan a haɗe ya zaunar da ita a gefen gadon. sannan shima ya zauna kusa da ita yana janyo table gabansa, ya buɗe coolern abincin dake kai yaga dambu ne na cous-cous da yaji hanta acikinsa sai ƙamshi yake. daga buɗewa duka wajen ya baɗe da ƙamshi. ya juyo da kansa kaɗan ya kalleta tana ta matsar ido, ya tamke murya yace,"when did you wake up?". taja majinar hancinta cikin
🏠