ba amma sai ya juya ya tafi ya barta da zummar zaije ya dawo ya bata haƙuri, ashe juyawa yayi ya tafi da zuciyarta.
ya tafi da dukkan nutsuwarta da tunaninta, don haka a ranar buɗe company da ta ƙara ganinsa ba zata yi saken da zai suɓuce mata ba. a lokacin Ilham faɗa mata tayi kai tsaye cewar indai Hammah Turaki ne ba zai sota ba, hasalima ko kulata ba zai yi ba talkless of batun soyayya har ta kaisu ga aure. ta faɗa mata bai taɓa soyayya da wata mace ba.
sai dai buɗar bakin Gimbiya Aisha ce mata tayi,"Ilham, ni kuma ki rubuta ki ajiye, zan sauke duk wani jin kai dake kansa, zai soni, zai nemi aurena, zai aure ni a sanda ya gama haukacewa akaina".
Ilham tace mata,"asirce min ɗan'uwa zaki yi?". Gimbiya Aisha na murmushi tace,"bana fatan watarana tazo da zan aikata saɓon ubangiji Ilham, amma ki sani, zan haukata ɗan'uwanki ne kawai da salon soyayyata me zafi, irin wacca zai hanaku sakat har sai kunzo kun ɗaukar masa ni kun kai masa gidansa. da gaske nake miki Ilham ina son Brothernki sosai wallahi, kuma ina adu'ar Allah yasa ya zama mallakina, nasan kuma zan samu tunda dai har sarauta ce ta haɗu da sarauta".
Ilham ta rumtse idonta sosai tana jin wani iri a ƙasan zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan. ta wutsiyar ido take kallon Turaki dake driving cikin ƙwarewa, yana bin karatun ƙur'anin da ya kunna. ta mayar da murfin idonta ta rufe tana jin a ranta kamar zata yi kuka.
Turaki ya kai sanyayyan hannunsa ya taɓa goshinta, lokacin ta buɗe ido tana miƙewa zaune.
yace da ita,"did anything happend?". ta girgiza masa kai,"ba komi Hammah". "kuma kika yi silent bayan na san wannan bakin baya rabo da labari".
tai murmushi tukunna tace,"to ai naga kana bin karatu ne". Turaki ya kai hannu ya kashe karatun sannan yace,"ina jinki, bani labari".
"wanne iri to?". yace,"irin fitinar da kika dinƙa yi da kina yarinya bayan na koma Europe wurin Granny".
tasa hannu ta rufe fuska tana cewa,"to ai kasan wannan time en, kaga babu batun a baka labari". ya ɗan waigo ya kalleta yana cewa,"give me my phone". ta miƙa masa yay dialling numba ɗin Zaytuna ya kira.
sai da kiran ya kusa katsewa sannan tai picking, bayan picking ɗin shiru yay baice da ita komai ba. sai itace tayi murmushi daga inda take tana duban Fillo dake bacci hankali kwance akan gado tace,"bata tashi ba".
Turaki yace,"up to now?, lafiya kuwa?".
Zaytuna tace,"lafiya lau, rashin bacci ne da bata yi ba jiya". "why is that?".
tace,"naje wurin Kaka nace mata ko da zata ji shiru Fillo bata dawo ba zata kwana a wurina, saboda naga kaman bata jin daɗi tun ɗazu tana ta bacci...so Kakan sai take ce min ai jiya ma kwana tayi bata rumtsa ba tana ta kuka, kuma tayi tambayar meke damunta bata sanar mata ba, ta dai bar hakan a rigimarta kawai...dana dawo kuma naji jikinta da zafi, kukan da tayi ma zai iya sa mata zazzaɓi".
Turaki took a deep breath with out saying anything, hakan yasa Zaytuna kwantar da murya tace,"i will prescribe some drugs sai ka taho da su saboda ciwon yatsanta. like da fever ma a jikinta".
yace,"oak send it to me right now via message".
sai kuma yace,"Bello fa?". Zaytuna tai dariyar da ya bayyana haƙoranta tace,"he left since, da ƙyar na taushe shi wai sai yaje wurin Maama anyi wacca za'ai".
tsakin Turaki ya fita da ƙarfi yana cewa,"mahaukaci ne ai...don't pick up his calls again".
Zaytuna na murmushi tace,"na hannun daman naka Hammah?". yace,"ehh shi". ya faɗa yana katse wayan.
ya kashe kiran yana parking a ƙofar store ɗin da suka zo. suka fito a tare da Ilham wacce ya zagaya yana tambayarta dalilin sauyawan mood ɗinta alhalin ba a haka suka fito ba.
****
a hankali Fillo ta buɗe idonta daga ɓaccin da ta tashi, ta sauke ƙwayar idonta akan gadon da ta san ba katifarsu bace ita da Kaka.
tayi wani mugun zabura ta tashi zaune tai saurin durowa daga kan gadon, cikin ranta tana faɗar kalmar innalillahi.
ta rasa ma da wanne irin tunani zata yi amfani wajen tuna komai. bakin ƙofar da ta san ta riƙe handle tana kuka kawai take bi da kallo, da yaushe tayi baccin?, kuma ya akayi tazo kan wannan gadon?. kawai sai ta duƙe a wurin ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, lokacin kuma taji kiran sallah ya shiga cikin kunnenta wanda ko ba'a faɗa ba tabbata na magriba ne.
ta miƙe da sauri ta wuce ƙofa zata buɗe taji ƙofar a rufe, ta dawo a hargitse ta shiga duba keys acikin drowers bata gani ba, taji zuciyarta ta ƙuntata. shin Turaki wanne irin mutum ne shi mara uzuri da yafiya a rayuwarsa, akan kawai ta fasa turare zai kulleta a ɗakinsa ita ɗaya?. kawai sai maganarsa ta dawo mata sanda yace idan ta fita a ɗakin nan to biyansa turarensa tayi.
kulle idanuwanta tayi tana jin hawaye na biyo kuncinto da tsananin jin haushi da takaicin kanta. me ma ya kaita?, har sai yaushe ne zata daina shiga hurumin da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba?, dan ana so a cutar da Turaki doesn't mean ana so acutar da Hammah Hamid ne. ina ruwanta da Turarensa ma da har zata fasa kawai saboda