okacin da ya shaƙu da ita, ya saba da ita, ya shaƙu da ƴarta, yake ganin ta zamar masa uwa, sai Fulani ta rikiɗe ta koma kalar wata mace ta daban, mace me cike da tuggu da makirci, ta shiga muzguna masa tana goranta masa akan zaman da yake yi acikin masarautar alhalin ita ta rabosa da Hajiya Madina, ba wani ya ɗaukosa ya kawosa ba.
ta ƙala masa sharrin satar gwal a lokacin da baiji ba bai gani ba, ta ƙara da faɗin ya satar mata kuɗaɗe, kuma ba tare da wani tunani ko bincike ba Mai Martaba ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata, hukuncin da Hajiya Madina tayi tsalle ta dire agaban Mai Martaba tace muddin aka ga an saka ɗanta a prison to wallahi sai dai idan bata numfashi. ta kuma fuskanci Baffa gaba da gaba tace ya sani, idan har matsayinsa na alƙali bai shigar da ƙarar Fulani akan ƙazafin da ta yiwa ɗanta ba, to la shakka babu kaffara sai ya rabu da ita, kuma ya rubuta ya ajiye, rabuwarsu ba yana nufin zata tafi ta bar masa Turaki da Zaytuna bane, a'a zata tafi da gaba ɗayansu ne ta kowanne hali, ko da zai dinƙa yankar naman jikinta yana goranta mata ba ita ta haife su ba.
asalin samo gaba me ƙarfin gaske kenan da ta shiga tsakanin Hajiya Madina da Fulani, har tsawon shekaru masu yawa, har sai lokacin da Turaki ya kammala degree ɗinsa na biyu sannan gabar tasu ta ƙare, bayan Hajiya Madina ta tambayi Turaki ya faɗi kyautar da yake so tayi masa yace mata yana so ta daina gaba da Fulani, domin gaba abar ƙyama ce tunda Allah baya so, kuma ma'aikin Allah yace kar mutum ya rama sharri da sharri dan haka ta bar batun ɗaukar fansa da tace zata yi akan abinda Fulani tayi masa, ta yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata.
a duk sanda ya nemi abu a wurin Hajiya Madina take a wurin take yi masa ba tare da ɓata lokaci ba muddin bai fi ƙarfinta ba, amma a wannan roƙon da yay mata sai da ta ɗauki tsawon kwana biyu shi kansa bata shiga sabgarsa ba, wai sunan shawara take tayi da zuciyarta taga idan zata iya yafewa wanda ya ƙalawa ɗanta sharrin sata. daga baya kuma sai komai ya warware tunda suka ƙara tausarta shi da Khalil da Bello, daga nan kuma Hajiya Madina ta sauko ta ci gaba da bawa Fulani girmanta na matsayin da take da shi.
yana zaune cikin tunanin abubuwan da suka faru a baya Ilham ta dawo, sai da ta taɓasa tukunna ya buɗe idonsa ya sauke akanta. tayi kyau acikin shigar da ta sauya na sky blue ɗin code less me shegen tsada, ya miƙe yana ɗaukar key ɗinsa ya kalli Abbas yace,"babban Yarima zan wuce".
ba tare da Yarima Abbas ya ɗago daga operating laptop nasa ba yace,"ka gaida Maama da Zaytun".
fitowarsu daga sashin Yarima Abbas suka ci karo da Fulani Azima ta fito daga turakarta kuyangu uku na biye da ita. haka kawai Turaki yaji gabansa ya faɗi da ganinta, lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarsa ta shiga karanto wasu ayoyi na kariya dake cikin alƙur'ani, ba wai yana nufinta da mugun abu bane, a'a haka kawai tun a ranar da taje asibiti dubasa yaji zuciyarsa ta kasa kwanciya da ita, kuma yana ta ƙoƙarin yakice abinda zuciyarsa ke raya masa akanta amma hakan yaci tura, in yayi ƙoƙarin watsarwa sai maganar Fillo ta dinƙa dawowa cikin kansa na batun asirin da tace ta ɗauke akansa.
*ASIRI!* har yau kalmar nan tsaye take a cikin ransa. kenan inda Allah bai shigo da Fillo cikin rayuwarsa ba shikenan duk kalar asirin da yaji ta ɗauke akansa sai ya kama shi?.
ya rufe ido ya buɗe yana kawar da wani tunani dake shiga sashen tunaninsa.
Fulani Azima ta tsaya da tafiya tana kallon Turaki da Ilham dake tafiya, wai Turaki ne tare da ƴarta?. lokaci ɗaya zuciyarta tayi wani mugun matsewa. taji kanta ya sara mata, lallai bata ga ta zama ba, sai ta sake sabon shiri, dole ne ma ta koma wurin boka, zata faɗa masa ya sauya tsarin aikinsa, sannan kuma yayi mata duba akan duk shegen dake lalata mata aiki.
a harzuƙe ta juya ta koma ta fasa zuwa inda ta nufa.
cikin motar Turaki dake tafiya akan titin zuwa PERKY FRAGRANCE STORE, wayarsa dake hannun Ilham tayi ringing a karo na huɗu, kuma a karo na huɗun ta ƙara ce masa,"Hamma ya kamata kayi picking call ɗin nan".
shima a karo na huɗun ya ƙara bata amsa da cewar,"picking ɗin ba ya da wani amfani".
a karo na biyar da kiran ya ƙara shigowa Ilham ta tsaya tana kallon lambar da babu suna ajiki. kasancewar kiran ba huruminta bane dalilin da yasa tun farko bata bi ta kan lambar ba, sai a yanzu da idanuwanta ke kallon lambar cikin kanta kuma na karanto mata lamabar ƙawarta Gimbiya Aisha.
har sanda kiran ya katse Ilham bata bar kallon lambar ba, haka ɗaya sai taji kamar an soketa da kibiya a ƙirjinta. kenan dama da gaske Aisha take yi mata.
conversation ɗin su na last haɗuwarsu ya shiga yawo acikin kanta. ranar buɗe company ɗin su Turaki, ranar da Turaki yay kwalliyar da babu macen da zata kalle shi bata kwaɗaitu da ya zama mallakinta ba. kuma a sannan Aisha ke bata labarin ta taɓa ganinsa a asibiti sanda taje duba wata cousin sister ɗinta, taso tayi masa wulaƙanci irin wanda kare ba zai shinshina