daɗe ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi, Allah ya huci zuciyarki uwar gijiyata...yanzu kamata yayi kisha furar nan domin ki samu kiji sanyi a ranki, tun safe babu abinda kika sa a bakinki...batun Hajiya Madina da Ɗan Ramla tamkar tsoma allura ne acikin ruwa, kisa a ranki lokacin kawar da su daga rayuwar Alƙali Dikko yazo ƙarshe, zasu barshi kamar yanda Ramla ta barsa".
Fulani tayi murmushin takaici me ciwo, sannan ta ɗago ido ta yiwa Jakadiya kallon tsab kafin nan tace,"ban taɓa yin wani shiri akan Madina ba, kasantuwar nasan Dikko ba sonta yake ba, zatona a lokacin Mai Martaba zai sawwaƙe min daga nan sai na maye gurbin Ramla, ashe duk lissafin da nayi akan hakan da ƙazamin tunani nayi shi...dukkan wani shirina ina yinsa ne akan ɗan Ramla, shirye-shiryen da nayi akan na tarwatsa yaron nan yafi ƙirgen yatsu, sai dai har yanzu na kasa ganewa Jakadiya, na kasa fahimta, na rasa dalilin da yasa cikin tarin ƙullin da nayi akan Turaki babu wanda yay tasiri, amsa ɗaya nake so daga bakinki ba daga bakin boka ba, haka kuma abu ɗaya nake so na sani daga wajenki ba daga wajen boka ba, meke warware aikin Malam?, menene ke warware duk wani ƙulli da nayi?, waye yake lalata min dukkan shirin da nayi?".
sai kuma ta miƙe tsaye a fusace, ta ɗaga murya cikin tsawa tana nuna Jakadiya tace mata,"faɗa min gaskiya, kina aiwatar da aikin da na saka ki ko kuma cin amanata kike yi?".
cike da tsoro da rawa jiki Jakadiya tace,"wallahi, wallahi Ranki ya daɗe ina sawa a aiwatar da duk abinda kika ce, wallahi kuma ko kaffara ba zanyi ba waɗanda na saka suyi ba zasu ci amanarmu ba, ni kaina ina matuƙar mamakin yanda komai ke warwarewa acikin sauƙi, sai dai ina tunanin ƙarfin adu...".
ai tun Jakadiya bata ƙarasa ba Fulani ta ƙara ɗaga murya wajen dakatar da ita acikin tsananin fushi da ɓacin rai,"dakata munafuka, tabbas sai naga bayanki Jakadiya domin babu wanda yake cin amanata na ƙyale shi...karki ƙara buɗe baki kice zaki faɗa min zancen banzan da ba yarda zanyi da shi ba, ƙarya kike yi kice tasirin adu'a zai karya aikin asirin da nake ɓarnatar da kuɗi akai, aikin boka tumbutsu ne ba aikin wani galhonaho ba, bokan da yake aiki tamkar yankan wuƙa, kuma tunda har aikinsa yayi tasiri akan Ramla ƴar Turakin Taraba, bana tunanin aikinsa zai ƙi cin wani tsiyatattan halitta Turaki, don haka kamar yanda na ɗauki alwashin ganin bayan Madina da Turaki a wannan ƙarnin, haka kema sai naga bayanki Jakadiya tunda har kika ci amanta".
Jakadiya ta zube gwiyoyinta a ƙasa ta shiga roƙon Fulani cikin tsananin ruɗewa, ana cikin haka Ilham ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. cike da shagwaɓa ta faɗa jikin Fulani ta sakin kuka da cewar,"dan Allah Mami ki barni naje, Allah ba zan jima ba zan dawo...sau biyu kenan Hammah Turaki na ciwo bana zuwa na duba shi, kuma yana ta min complain ɗin hakan".
Fulani ta tureta daga jikinta, ta fita rai a ɓace daga turakar tata. Ilham ta buta da kallo kafin daga bisani ta zube akan gado tana sakin kuka.
tana cikin kukan wayarta ta shiga ringing, ta ɗau wayar tana kallon screen ɗin, ganin sunan Turaki na yawo a jiki yasa ta sakin wani kyakykyawan murmushi sannan ta ɗaga tana cewa hello cike da shagwaɓa.
daga ɓangaren Turaki ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ba ki damu da lafiya ba right?".
Ilham ta ƙara narkewa da muryar shagwaɓa tace,"Hammah yau zan zo insha'Allah".
Turaki yace,"ba sai kin zo ba, ni gani na zo. ina ɓangaren Abbas...but ba zan jima ki hanzarta".
*_Wallahi duk son reader da ƙaguwar ai typing baku kama ƙafar yanda writer ke ƙaguwar tayi typing ba, haka kuma baku kaita ƙaguwar tayi tayi ta kammala book ɗinta ba. amma har yanzu na rasa me yasa some readers kuke kasa yiwa writer uzuri idan bata yi posting ba...duk wata writer bata ƙin yin typing haka ɗaya wallahi sai da babban dalili, this typing da kuke gani is not easy at all, a barku da rubuta comment kaɗai ya kuke ji? to balle kuma a barka da rubuta readmore sama da 3?...duk a bar wannan, ina tunanin a page kusan uku na faɗa muku biki muke yi, biki muke bana karere ba, bikin ƙannena biyu a cikin sati biyu duka a haɗe, amma a haka na dinƙa squeezing ina muku typing, har akazo gabar da duk yanda naso na samu chance na yakice nayi muku ko da babu readmore wallahi na rasa, akace Babbar Yaya Magajiyar Uwa to kuna tunanin bikin zaizo min da sauƙi ne?, sai monday muka kammala biki, to ya kuke so nayi da raina tsakani da Allah?, i think ko da aka kammala biki ku masu iya bani hutu ne kuce na huta sbd gajiya, jiki da jini...amma har aka iya samun wasu suna faɗa min magana ta private da masu kirana a waya suna faɗa min abinda suka ga dama as if umarnin wani nake bi nayi typing ɗin, to ko yau nace na daina rubuta novel ɗin nan ta zauna wallah tunda ni nasa kaina ba wani yasa ni ba...so for Godsake muke yiwa juna uzuri a lamuran rayuwa na komai ba lallai sai a rubutu ba, yanzu in ace mutuwa nayi baku da labari fa?. kuma fisabilillah da naku zafin zanji ko da na ƴan youtub