NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 103 of 323

ar jiki da take yi, yaja dogon tsakin da yayi duka har cikin kunnenta, ya kamo hannun ya cire kwalbar sannan ya shiga treating mata ciwon, tunda yasa spirit ya goge jinin ta tsala uban ihu tana neman fincike hannun, hakan yasa ya riƙe hannun da kyau yanda ba zata ko iya ja ba balle ta iya fizga har ya ɗaure mata wajen da bandage sannan ya sakar mata hannun. zuwa lokacin tayi kuka ta gode Allah. muryarsa a tamke ba tare da ya duba irin zafin ciwon da take ji ba yace,"tashi ki gyaran waje, saura ki ƙara saka hannu tunda baki da hankali". ta miƙe sai sheƙar kuka takeyi ta ɗauko tsintsiya ta tattare wajen. tana kammalawa ta nufi ƙofa zata fita taji ya ƙara saka key ya kulle. "na gama ai". ta faɗa tana kallonsa a ɗarɗarce. ba tare daya kalleta ba yace,"kin san tsadar turaren da kika fasa?". da sauri ta girgiza kai tace,"a'a, amma don Allah kayi haƙuri bada sani na bane". ya ɗauke idonsa daga kan wayarsa ya ɗora akanta sannan yace,"balle ma da saninki kika fasa ɗin, dan haka abu ɗaya na san da shi sai kin biyani turarena, kuma a yanzun anan wajen ba sai anje ko'ina ba, if kika biyani sai ki sami damar fita daga room ɗin nan". maganarsa yasa ta ruɗe ta shiga ba shi haƙuri tana roƙonsa. tayi mugun basa tausayi amma ya ɗauke kansa kamar baya jinta. wucewar mintina biyar sai yaji shiru ɗakin, kukanta ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, tun before ya juyo da kansa ya kalli bakin ƙofar ya fara tunanin ta yanda akayi ta fita after yasa key, sai dai yana juyowa ɗin sai ya ganta ta ɓingilar da kanta ajikin ƙofa baccin kuka ya ɗauketa kamar jaririya. zai iya cewa bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba, banda yasan abubuwa da dama ba, to tabbas zai rantse wannan rigimammiyar yarinyar ba itace hatsabibiyar dake cusa kanta cikin haɗarin da ba nata ba. ya jima yana kallonta a hakan, matsawar ya barta ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci a haka wuyanta sai yayi ciwo sosai saboda yanda ya barƙale, hakan yasa ya sakko a gadon yazo ya ɗauketa ya dawo ya kwantar da ita akan gadonsa, yaja blanket ya rufeta yana jin zuciyarsa na matsewa. for few minutes yana daga kishingiɗe ajikin pillow daga ɗayan side ɗin, tunani kawai yake yi kala-kala acikin ransa, daga bisani ya miƙe ya bar ɗakin, yana fitowa yaci karo da Bello na niyyar shigowa, ganin junansu yasa duk suka ɗaure fuska. Bello na ƙoƙarin ya ture shi ya shiga room ɗin, shima Turaki na ƙoƙarin ya turasa baya ya nuna masa hanyar da ta fi dacewa da shi. "Malami ban hanya". Bello ya faɗa cikin tamkewar fuska yana sa hannu ya ture Turaki gefe, ya murɗa handle ya shiga bed room ɗin. sai dai yana shiga ya fito da sauri yana dakatar da Turaki daga tafiyar da yake yi zai sauka daga benen. "Turaki me nake gani a ɗakinka?". a fusace Turaki ya juyo yace da shi,"uban wa ya kai ka shigar min ɗaki dama?". shima Bellon a fusace yace,"da sai da izininka nake shiga?, ko kuma dama Baffa ce yayi ɗakin naka ne kai ɗaya?...ba wannan ne a gabana ba Muhammad, faɗa min me na gani a ɗakinki?, warware min komai tun ban fara shakku akanka ba". Turaki yaja tsaki ya sauka a benen ba tare daya ce masa komai ba. Bello yayi ajiyar zuciya yana sa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Zaytuna. *Masarauta Kaltungo.* "nifa duk bayannan naki a banza nake jinsu, shekaru ba su zasu hanani cimma alwashin dana ɗauka ba Jakadiya, tunda har naga bayan Ramla to babu abinda zai hanani ganin bayan Madina, ki rubuta wannan ki ajiye, ko bayan raina zaki faɗa cewar ni Fulani nace duk wata mace da Dikko zai aura rayuwarta a hannuna take". furucin da Fulani tayi kenan a sanda idanuwanta ke sauka a ƙasa, tana jin zuciyarta na zafi da tafarfasa, tana jin yanda zuciyarta ke kuka, kukan da ta ɗauki tsawon shekaru masu yawa tana yi kuma har yanzu bata daina yinsa ba. ƙafarta kawai take kallo wadda tasha adon sarƙa na gwalagwalai da azurfa, kallon ƙafar tata take yi a zahirance, amma a baɗini ƙafar Alƙali Dikko take kallo, ƙafarsa take kallo tana tuno yanda ta riƙe ƙafafunsa a wancan lokacin tana roƙonsa akan kar ya rabu da ita ya aureta ko da bayan auren zaisa wuƙa ya kasheta, da kuma yadda ya fizge ƙafafunsa ya fita daga ɗakin ya barta ba tare da ya waigo ya kalleta ba, waigen kallon da bai ƙara yi mata ba har yau tsawon shekaru 37, duk da kasancewarta matar Yayansa Mai Martaba Hashim. ta rumtse idonta sosai tana jin zafi a zuciyarta, ganewa ne kawai mutane ba su yi ba, amma zafin so yafi ƙarfin kwatance, ita zata iya cewa zafin so yafi zafin wuta zafi da raɗaɗi, muddin wanda kake so bai bar tasirantuwa a zuciyarka ba. Allah ya sani har duniya ba zata taɓa daina son Alƙali Dikko ba duk da cewar akwai igiyar auren wani akanta, auren ma da har suke da rabon ƴa a tsakani, ƴa me shakaru 21 a duniya, son Alƙali Dikko ba daga gareta bane, so ne daga Allah. taja wani dogon numfashi ta sauke, a sannan ta buɗe ido ta sauke akan ƙaton tray ɗin dake gabanta. Jakadiya Haulat tace,"ranki ya
🏠