ya ba tare da wani ba, tun abunda ya faru a jiya take jin tsoron ƙara shigowarsa.
haka ta sakko daga upstairs ɗin zuciyarta cike da tunani kala-kala. ta biyo ta corridor ɗin da zai fitar da kai ta baya, sai dai tana zuwa wajen ƙofa taja tayi turus tayi saurin laɓewa saboda abinda ta gani da kuma abinda take ji. tsabagen girgiza da Al'amarin bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana saka hannu ta toshe bakinta gudun kar numfashinta dake neman tsarƙewa ya fallasata.
ta rumtse ido da kyau cikin ranta tana ta adu'a Allah yasa kar a ganta, tayi shiru tana sauraron dukkan zantukan da ake yi, lokaci ɗaya ta ƙara girgiza taji kamar kunnenta ba daidai yake jiyo mata ba, cikin azama ta miƙe tabar wajen da sauri ta koma ta parlo ta bar side ɗin gaba ɗaya sai haki take yi.
ta jima a compound zaune a wajen flowers tana ta mayar da numfashi, kafin ta iya miƙewa ta nufi part ɗin su Turaki, cikin sanɗa kamar wacce ke gudun wani ya ganta. tana shiga ta tarar da Khalil a parlo yana kallo, ta tsuguna ta gaida shi cikin rasa makamar abinda zata ce ya kawota. sai kuma taji Khalil ɗin yace,"ke Maama ta aiko?".
da sauri ta ɗaga masa kai tace,"ehh". yace,"to kinga ba wani gyara ne me yawa ba, toilet kawai zaki wanke min kinji, yaron dake mana aiki ne bai da lafiya". ta miƙe tana cewa,"tom Hamma".
Khalil ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ganin yacca take tafiya kamar mara gaskiya.
bata ɗauki lokaci ba ta kammala wankin toilet ɗin Khalil, tana gamawa kuma ta faɗa bedroom ɗin Turaki, da shigarta shima ta wanke nasa sannan ta kimtsa ɗakin gaba ɗaya, ta saka masa turare me ƙamshin gaske.
kwalbar turaren dake kan dressing mirror ta ɗauka ta riƙe a hannunta, design na kwalbar yayi matuƙar burgeta, sai dai ƙamshin har yanzu bata ƙaunarsa, kamar wacca taga kashi haka take aikin yamutsa fuska still tana riƙe da kwalban, can kuma sai ta saki kwalban ya faɗi ya fashe, ya fashe a sanda take ƙara saka ƙasan takalminta ta murje kwalban sai ɓata rai take.
ƙarar fashewar ya haɗe da rufe ƙofar ɗakin, ta ɗago kai da sauri tana kallon door ɗin sai ganin Turaki tayi ya jingina jikin ƙofar, ya rungume hannayensa a ƙirji yana kaɗa one leg. tsoro sai ya kamata ta dabarbarce tana ja da baya, duk ta rasa yacca zata yi da kuma abinda ya kamata tayi, taji kamar ta kurma ihu saboda yanda ya kafeta da ido yana kallonta fuskar nan a haɗe, alamar ya harzuƙa da ta'adin datayi masa.
sai tai saurin duƙawa ta shiga tattara kwalban da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma tana toshe hancinta da shi, bata ankara ba kwalban ya shige mata cikin fata nan da nan jini ya fara zuba. cikin jin zafin ciwon ta furta,"wayyoo Kaka". ta faɗa tana yarfa hannu jinin na fallatsuwa a wani wurin.
ganin yanda jinin ke fita sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin,"wayyo jinina, wayyo Kaka, wayyo jinina zai ƙare".
Turaki da har lokacin yake tsaye yana kallonta yana kallon jinin dake zuba, yaja tsakin takaici ya bar bakin ƙofar ya ƙaraso ciki. akan bed ya ajiye wayoyinsa sannan ya shige toilet, after 10mints ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ƙaramin dake hannunsa kuma yana goge sumar kansa da shi. ya kai idonsa wurin da ya barta yaga bata wajen, sai kwalban sai jinin da yaɓata wajen, ya ci gaba da goge kansa yana ƙarasawa bakin gadon ya zauna.
ɗago da idonsa da zai yi ya ganta tsaye bakin ƙofa ta kama handle ta riƙe, sai aikin murɗa shi take yi duk tabi ta ruɗe, har lokacin kuma bata bar kukan ba haka kuma bata daina yarfar da hannun ba.
da mamaki kawai ya tsaya yana dubanta, jinsa yake kamar ya tashi ya mammaketa don takaici. ta juyo da kanta a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauke kansa daga kanta, karaf suka haɗa ido, Turaki ya ƙara shan murr, ita kuma ganinsa babu riga yasa tayi saurin runtse ido tana ƙara fashewa da kuka.
bayan Turaki ya saka kaya, ya dawo ya nemi waje ya zauna bakin gadon, ya ɗauki wayarsa yay dialling numbern Zaytuna. tana ɗagawa yace mata,"ki bada bandage a kawo min". yana faɗar hakan ya kashe.
ya ajiye wayar sanda Fillo ta kira sunansa,"Hammah don Allah kayi haƙuri, jinina zai ƙare". tai maganar acikin kuka, ya galla mata harara ta ƙasan ido yana ƙara jin sabon takaicinta acikin ransa.
jin ana knocking door ya taso yasa key ya buɗe ƙofar, ya karɓi box ɗin dake a hannun Ɗausiyya ya maida ƙofan ya rufe tare da ƙara sanya key sannan ya dawo ya zauna bakin gado.
"zo nan". ya faɗa idonsa akanta. kamar ba zata zo ba sai kuma ta miƙe ta taho kamar me shirin faɗuwa, ganin cewar in taci gaba da tsayuwa a haka jininta duka zai tsiyaye.
ta tsuguna a gabansa wurin da ya nuna mata, ta miƙa masa hannun ta runtse ido tana jan numfashi.
ya kalli hannun ya kalleta sannan yace,"are you stupid?, kwalban ma da ya shiga ba zaki iya cirewa ba kika barsa a jikinki?, ke shashashan ina ce wai".
cikin kuka tace,"to ai ba zan iya ba, jini ne yake fita".
"jinine yake fita shine cire guntuwar kwalba ya gagareki?".
ita dai bata ce masa komai ba banda kyarm