shin haihuwar Ramla, to kuma sai Allah ya nuna ikonsa ko da ta shigo gidan itama sai da ta shafe shekaru masu yawa bata ko yi ɓarin ciki ba, har Allah ya bawa Ramla ciki ta haifi 2wins maza, ranar suna yaran akasa musu sunansu Muhammad da Lateef, Muhammad shine aka saka masa sunan mahaifin Ramla suke kiransa da Turaki kamar yanda ake kiran mahaifin nata, shi kuma Lateef shine yaci sunan mahaifin Dikko zasu ke kiransa da Abi, to kuma a ranar sunan da daddare sai Lateef ɗin ya rasu.
sai da Muhammad Turaki ya shekara huɗu ciff a duniya sannan Hajiya Madina ta haifi nata yaron wanda yaci sunan mahaifinta Ibrahim suke kiransa Khalil, shekararsa biyu shima Ramla ta ƙara haihuwar ƴa mace me suna Zaytuna. part ɗin kowacce daban amma baka ganinsu ba'a tare ba, in kuwa ka gansu separately to dare ne yayi za'a tafi makwanci, amma da zarar safiya tayi sun tafi breakfast side ɗin Baffa, har sanda wani acikinsu zai yi baƙo, ko kuma idan Hajiya Ramla zata tafi office, idan wannan tayi ba daidai ba ɗaya zata gyarawa ƴar'uwarta kuma su amshi gyaran cikin sauƙin kai.
wucewar sati da watanni anata saka ran ganin ko Hajiya Ramla zata dawo amma shiru kake ji, da haka har aka shafe shekara guda, kuma a lokacinne aka sallama da cewar ta rasu.
dalilin da yasa Hajiya Madina ƙara jan Turaki da Zaytuna a jikinta kenan saboda tausayin maraicin su na uwa, ta rungume su a ƙirjinta tamkar ita tayi naƙudarsu, babu ranar da bata kallonsu bata zubar da hawaye ba har suka girma, ƙarshe ma sai ya zamto tana nuna musu tsantsar so da kulawa fiye da waɗanda ta haifa a cikinta, son su take yi domin Allah ba da wata manufa ba.
haka kuma kwata-kwata bata nufar yaran da sharri, abinda zai samesu sai ya ɗaga hankalinta wanda zai sami Khalil ko Samha bai ɗaga mata hankali ba ko kusa, don gani take tamkar in wani abu ya samesu lallai Allah xai tuhumeta domin amana ce da tayi alƙawarin ta ɗauka, ta ɗauki alƙawarin zata riƙe su kamar yanda Ramla zata riƙe su, kuma tayi alƙawarin ba zata kalle su da sunan ƴaƴan miji ko ƴaƴan kishiya ba sai ƴaƴan da ta haifa acikinta.
bayan shekara goma a wata rana ta laraba sai ga message a wayar Baffa, saƙon da Hajiya Ramla ta turo musu kan cewar tana nan a raye bata mutu ba, kuma ko da xa'a ɗauki tsawon shekara 100 kar su taɓa sawa a ransu cewa ta mutu, tana nan a raye nesa da su sai dai ba zata taɓa dawowa gare su ba har abada.
wannan saƙon ya girgiza kowa, kuma wannan saƙon shi ya haddasa jin haushi a zuciyar Zaytuna, take jin tana tsananin fushi da mahaifiyarta, tana jin yau ko da ace za'a kawo mata gawarta ba lallai ne ta dubeta ba.
saɓanin Turaki da saƙon ya ƙara haddasa masa damuwa a ransa, lokacin shekarunsa goma sha shida, yana can europe wurin Kakarsa ta wurin uwa, kuma tun daga lokacin har kullum tunaninsa guda ɗaya ne, a wanne hali Mum take ciki?, ya lafiyarta take?, menene damuwarta?.
abu ɗaya har kullum ransa ke basa akan barinta gidan shine, wataƙila tayi fushi da shine, tayi fushi da shi akan tana tunanin cewar shi ya haddasa kamawar wutar ɗakin, alhalin shi bai san da komai ba, bai ma san da cewa wutar ta kama ba sai da tayi magana, time ɗin da ta fito ɗaga toilet tayi wanka tana tsane jikinta da towel, shi kuma yana zaune akan gadonta yana homework ɗin da Hajiya Madina ta basa, sai ji yayi Mum ɗin na tambayarsa aina ya sami ashana har yayi mata ta'adi, ta tambayesa ɗin tana yowa wurin da labulen ya ɗan fara ci zata kashe wutar.
yana iya tuna yacca taja tsaki a sanda ta kama labulen da sunan zata watsa ruwan dake hannunta, sai yaga kawai ta tangarar da jug ɗin ya faɗi ya fashe, ta wuce ta isa wadrobe ta ɗauki abaya ta zira ta fita ta barsu a daidai lokacin da wutar ta fara ci sosai, yaji tsoro ya sakko akan gadon yabi bayanta da gudu, sai kawai ta hankaɗosa ciki tana doka masa tsawa bayan ta ambaci ainihin sunansa da bata taɓa faɗa ba tunda ta haife shi, taja ƙofar ta rufe tasa key ta cire ta tafi da shi.
wannan ɗalilin ya barwa kansa, kuma har kullum yana roƙon Allah ya haɗa fuskokinsu kamin ya kai ga kushewa ya roƙeta ta yafe musu, ya faɗa mata gaskiyar cewar bai san komai ba akan kamawar wutar.
"Hammah Hakimi na magana a waya". maganar Zaytuna ta dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi. ya karɓi wayar yana karawa a kunnensa tare da yin sallama. sun ɗau lokaci suna waya Hakimi na tambayarsa yanayin lafiyar tasa, kafin daga bisani suyi sallama.
washegari ƙarfe goma na safe akayi discharge nasu suka koma gida. kuma suna komawa inda ya fara dosa bayan sunyi lunch shine ɓangaren ma'aikata, dalilin ganin tun dawowarsu bai ga gimlawar Fillo ba, tun da suka dawo yake ta zuba ido ko zai ga ta wuce amma ko inuwarta bai gani ba, kuma yana ta sauraren yaji wani yayi zancenta har da Maama amma sai yaji ba wanda ya ambaci ko da sunanta.
_Dan Allah kuyi haƙuri, jiya naso kuyi breakfast da sabon post sai kuma aka sami akasi, na gana typing ɗin banyi saving ba caji ya ƙare, typing ɗin ya goge gaba ɗaya. sai yanz