annuna ya tsira min allurar da har ta sa ni zillo ina sakin ihu. "dalla can tsaya".yace dani murya a ɗage. na maida kaina jikinsa ina sheƙar kuka. _wannan zafin jikin is worst, to me ya sameta haka?_ ya yiwa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa sai likita. haka aka kuma yin sauran test aka gama duk ban motsa ba, sai bayan da aka gama yaga ashe ma nayi bacci, kamar ya zareni daga jikinsa sai ya yatsinci kansa da kasa aikata hakan, dan haka da sanyin jiki ya gyara mata kwanciyar kanta, ya zauna jiran amsar result ɗin test ɗin.
yana zaman jira sai ga wani abokinsa ya kawo matarsa shima, sun jima basu haɗu ba nan suka shiga musabaha, matarsa ma ta gaida Haidar kafin ta nemi wuri ta zauna itama. "a'a kace kaima Madam ka kawo". cewar Mustapha dake kallon Haidar. Yay masa wani kallo yace,"who told you she is my beb, rigimammiyar ƙanwata ce na kawo babu lafiya. kasan ranon Kaka sai a hankali". "ehh gaskiya kam, rainon Kaka ai akwai rigima". suna hira nurse ya kawowa Haidar result ɗin, ya shiga tashinta a hankali har ta buɗe idon, ni kaina nai mamaki dan ba ƙaramin bacci nayi ba, yana riƙe da hannuna muka koma office ɗin wancan likitan, ya amsa result ɗin yay masa bayanin typhoid da maleria suka haɗar min, nan ya rubuta mana magunguna muka fito muka wuce pharmacy, ni dai duk na gaji da tafiyar hakan yasa naja na tsaya ina hutawa, sai da yayi gaba ya juyo ya ganni na jingina da bango. "mene kuma?". "Allah Yaya Haidar na gaji da tafiyan, kamar zan faɗi nake ji". tsaki yaja ya harare ni kamin ya dawo ya kama hannuna ya kaini mota yace na jira dawowansa. ya jima kamin ya dawo, a hanya ya tambayeni ko da abinda nake son ci, ina kallonsa nace,"Pure bliss wafer da choculate". sai kawai yay min kallo mai kama da harara ya ɗauke tare da cewar,"ba zan saya ba". har muka iso gida kuma bai kuma ce min komai ba, yau dai ƴan mutunci yake ji dasu dan sai nan da nan yake dani, yanzu ma daya ga zan faɗi kamani yay ya jingina ni da jikinsa. muna shiga parlo yace na nemi wuri na zauna, zan kwanta yace,"karki sake ki kwanta". na langaɓar da kai ina yamutsa fuska yace,"ke abu kaɗan kuka ko gajiyaba kya yi, mtsww". yaja tsaki ya wuce friedge, roban faro ya ɗauko ya buɗe ya haɗa min ɗaya daga cikin maganin da akace da mun dawo na sha. ya haɗa ya miƙo min yace nasha, ban samu fuskar gaddama ba na amsa na sha, Iklima tazo tana min sannu. nace ma ta ina Gwaggo tace taje wajen Anty. na tashi zan tafi wajenta naji muryarsa yana dawo ki zauna, na koma na zauna ina kumbura fuska. "kalla yanda kika bi kika wani rame". yana maganar yana hararata, ni dai na tashi na bar masa wurin nai wucewata ɗaki dan ban shiryawa bala'insa ba. ban fito ba sai dana jiyo muryan Gwaggo, na sameta ta riƙe ledar magungunan da ya bata tana ta masa godiya tana faɗi,"ai kaf cikin jikokina babu mai halin kirki irinka Haidar, shi yasa kake burgeni a ko da yaushe, yanzu ka duba waɗancan yaran, daga zagalon har lagwanin duk cikin kwanakin nan babu wanda yay tunanin kaita asibiti, kai dai Allah yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya". "ameen". yace da ita. Yaya Abba kuwa yace,"daga baya kenan". ta harare shi bata ce masa komai ba. Haidar yace ma ta,"idan da gaske kina son ta samu sauƙi da wuri saiki sa ta dinƙa shan magani, idan kuma kin biye ma ta sai kiyi ta zaman jinya". "insha'Allahu Haidar". ni ko alluran da aka mani har naji daɗin jikina sosai, har na ɗau wayana na kunna data muka hau hira da ƴan school namu ina tambayansu game da lectures. har yamma Yaya bai dawo ba, na ɗau waya na kira shi ina tambayansa Pure bliss dan Gwaggo ta hana a siyo min wai na fiya cin zaƙi. ina jinsa ya sa ki murmushi yace,"go slow ne yay tsaida ni amma saura ƙiris na ƙaraso, ki haƙuri Cutien Yaya". kamar ina gabansa nayi knooding kaina nace,"Allah ya dawo da kai lafiya". yace, "amin Cutie nah".
kamar ina gabansa nayi knooding kaina nace,"Allah ya dawo da kai lafiya". yace, "amin Cutie nah".kamar ina gabansa nayi knooding kaina nace,"Allah ya dawo da kai lafiya". yace, "amin Cutie nah".
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfan