zan dinga ci". "tabɗi aikuwa dai baka isa ba, wannan na baka trki hanyar neman zaman lafiya ba. sam ba zan iya ci gaba da ciyar da ƙaton gardi kamar ka ba, kalla fa yanzu daga dawowarka ka yashe min rabin madara, dama kai anan kafi kauri. ni fa na gaya maka zancen gaskiya ma banji daɗin dawowar nan taka nai ba...irin kune abun gudu, lokacin da muna tsohon gidanmu ai baka zuwa, amma da ike mun dawo gidan aljannar duniya shine ka gagara zama a naku gidan". shi dai bai sake ce mata komai ba, ita kuma ta kwashe kayan tea ta wuce da su kitchen tana mitar yashe mata madara da yayi. na gyara zan kuma kwanciya saboda ganin idon Gwaggo ya kuma doka min tsawa, babu shiri na saita hankalina, kamar an jefo Gwaggo sai gata ta fito tana cewa. "kaga Aliyu ni dai idan ba zaka iya zama haka kawai ba dan girman Allah ka bar min ɗaki, ba fa ni na gayyatoka ba, haka kawai ba zaka zo ka dinga firgita min Ƴa ba na rasa yanda zanyi da daddare, dama ya aka cika da wannan zafin zazzaɓin nata, ni kaina idan ka ɗaga murya furgita nake yi da wannan ƙatuwar muryar taka". ya ɗaure fuska yace,"dama meye ne yake damunta?". sai kuma tayi ƙasa da murya tana cewa,"wallah tun tafiyarka take fama da zazzaɓi mai zafi, gaba ɗaga fa sai yaune ta samu kanta". "kunje asibiti?".
"ehh to likita dai yazo har nan ya dubata. ni kuma kasan ba son takura ma ta nake ba tunda naga bata son asibitin nace a ƙyaleta". "saboda anga Baba baya nan ko, da yanan ai ko gwal ce ita sai taje asibiti". ya dubeni yace,"tashi kije ki shirya muje ai miki test". nai saurin ɗagowa ina dubansa, ya haɗe rai yana min wani wawan kallo, na shagwaɓe fuska na kalla Gwaggo ina shirin fashewa da kuka. "Gwaggo ni fa naji sauƙi". nace da ita ina karayar da kai. tace da Yaya Haidar, "shi abunda ka faɗa idan anyi ma ta zata samu sauƙi ne?". "me zai hana, ai kawai ki rufe ido ki barni da ita. haka za'a zuba ma ta ido ciwo na cinta. idan kuma kinƙi sai na ƙyaleta zazzaɓin yanzu ne kashe mutane yake". babu shiri ta juyo tana ce min. "kinga miƙe dan Allah bana son tashin hankali". na miƙe ina dukan ƙafa nayi ɗaki, ba dan naso ba shirya na fito, na samu Yayana ya shigo ma Gwaggo sallaman zai tafi makaranta, na taho tagal tagal kamar zan faɗi, ya riƙoni zuwa jikinsa yana tambayana sauƙin jikin. "da sauƙi". nace da shi ina kuma kwacewa a jikinsa. "me zan taho miki da shi idan zan dawo?". yace dani yana sunkuyo da fuskarsa saitin tawa. "pure bliss wafer". nace ina ɗago ido na kalle shi. murmushi yayi ya ɗan ja hancina yace,"Cutie nah wai sai yaushe za ki girma ne? pure bliss pure bliss dai". na karyar da wuya bance koma ba, ya kama hannuna ya zagaya dani na zauna a kujera, yace "Gwaggo zan tafi". "to ɗan albarka a dawo lafiya Allah ya bada sa'a. duk cikin jikokina kai ɗaya ne mai tausayi, cikin Abba da Haidar babu mai yiwa yarinyar nan magana a hankali sai kai". Ya murmusa kawai, sannan yay hanyar fita ina cewa,"Yaya a dawo lafiya". sai daya kalleni ya sakar min wani ƙayataccen murmushi tukunna ya fita. shi kuwa Yaya Haidar tunda na fito ko kallona bai kuma yi ba, har Yaya ya fice, sai daya gama jan ajinsa da miskilancinsa tukunna ya miƙe yace na biyo shi. muna isa hospital ɗin ya samu wani likita abokinsa, yay min tambayoyin abunda yake damuna, duk na faɗa masa, yace ba kya iya cin abinci ko? na gyaɗa masa kai alaman ehh, yay rubuce rubuvensa ya dubi Yaya Haidar yace ga wannan, ni dai tunda naji batun test hankalina ya tashi, dan naƙi jinin allura, tuni na fara kuka a hankali, na ruƙo hannunsa na damƙe ina roƙonsa, yay banza da ni kamar bada shi nake ba. test har uku haka likitan ya rubuta, ya miƙo masa takardar ya amsa, ya kalle ni fuska a haɗe kamar hadari yace,"tashi muje". na miƙe har lokacin ina riƙe da hannunsa har muka isa lab ɗin, suka masa bayanin wurin biyan kuɗin, yace dani na zauna anan na jira shi, bai jima ba ya dawo da reciept hannunsa, ya miƙawa mutumin, nan yace na taso dan ma a hakan ya roƙi alfarma ne amma da mutane da yawa kan layin. muryana a dashe nace,"dan Allah Yaya Haidar kar a min allura wallahi bana so, ka tambayi Gwaggo kaji ba'a min allura magani nake sha". yay min wani kallo yace,"to ni Gwaggo ne, dilla Malama tsaya kiyi abinda aka ce miki". na runtse ido kawai nayi surrender, Nurse ɗin yace dani na ɗaga hannun rigata, ina jinsa nai masa banza dan har shi nake jin haushi, Yaya Haidar yaja tsaki ya kama hannuna ya yaye hannun rigar tawa, sai dai lokaci ɗaya yaji tausayinta ya kama shi yanda yaji jikinta yayi zafi rau. yay ƙasa da Murya ya kira sunana, na amsa da umm, yace,"kiyi haƙuri ki daure ba za'a miki da zafi ba". ina sheƙar kuka nace ni fa ko da zafi ko babu bana so a ɓula min jikina. shiru yay ya jawo kujerar da yake zaune kusa da ni, ya kwantar da kaina saman cikinsa, a hankali yaji zafin jikinta yana ratsa kayansa ya shiga jikinsa, ya rumtse ido ya furta"Ya Salam, dama haka jikinki yay wannan zafin shine za kice wani ba za'a maki allura ba". ina jinsa ni dai bance masa komai ba, Mutumin ya kama h