NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 95 of 98

na cewa,"ku kam dukanku baku da imani, kuna ganin yarinya babu lafiya amma kunzo kun saka ƙwallo a gaba kuna kallo, me makon ku zauna kuyi ma ta adu'ar samun sauƙi". tana rufe baki Yaya Abba ya miƙe ya raɓawa ta gefenta yaje ya sake kunna tv ɗin, bai kai ga ɗago kai ba yaji saukar ranƙwashi zazzafa akansa. "haba dan Allah Gwaggo, kin san kuwa yanda wasan nan yake da zafi". ya faɗa yana sosa wurin yana kuma ɓata rai. "matsamin". ta faɗa tana bangaje shi a wurin ta kuma kashe tv. "wallahi idan kun kuma ganin kayan kallon nan a kunne to yarinyar nan ce ta samu lafiya. wai ku ina naku ma yake da baku da aiki sai zuwa ku addabi nawa salon ku lalata min, to wallah kar yaron daya kuma kunna min kayan kallo tunda kuma duk ansa muku naku. ni kar a ƙara kunna min ko socket ne tunda jikata babu lafiya, wanda ba zai jura ba sai ya daina shigo min ɓangarena". "mtswww". Yaya Haidar yaja tsaki, ta waigo gare shi tana masa wani duba. "ka dawo zaka fara ɗan iskan halin naka ko Aliyu. ni dai ka kuma yimin tsaki kaje kai da Allah tunda ni ba tsaka bace". ya ɗago ya kalleta ta wurga masa harara. "kai dama sam baka yo gadon arziƙi ba, mutumci sam bai gama ratsa ka ba da alama baka tsotsa ba. banda haka ka shigo ka kallemu da mara lafiya amma ko sannu baka mata ba kasa kai ka wuce, saboda zuciyarka sam babu tausayi bare imani". "to idan na tsaya ni zan bata lafiyar, ke fa Gwaggo akan waccen yarinyar kina da matsala Allah". bata kuma magana ba ta jiyoni ina wayyo Allah nah, ta iyo kaina da sauri tana zabga salati, Amina da Zainab sun riƙeni ina aikin kyala amai kore shar, sai Anty dake zuba min ruwa a fuska. shi kuwa Yayana gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa, tun ɗazu idonsa na kaina ganin idon Anty a wurin ya kasa zuwa inda nake, sai na ɗago ido sai naga yana ta kallona da tausayawa, yanzuma ina maida numfashi muka haɗa ido, ya haɗa hannu yana roƙona akan na daure naci abinci na sha magani. yanzu kam Allah ya taimaka na shanye curstard ɗin duka sai dai na kasa shan maganin. "Anty kawo maganin". Yaya Haidar yace da ita a lokacin daya iso wurinmu, ta miƙa mishi yace su Zainab su bashi wuri. ya ɗaure fuska tamau yace min buɗe bakin, zanyi gaddama ya ɗaga min hannu yana min wani mugun kallo, ya kalla Gwaggo yaja tsaki kaɗan yace. "don Allah tsohuwa ki mana shiru, duk kin cika mana kunne. kukan naki ne zai sanya ta samu lafiya". aikuwa cikin masifa tace masa,"ba zanyi ba, ba zanyi ba, nace bazanyi ba ɗin idan ka isa kuma ka hanani. mara mutunci kawai". ta kuma rungumeni tana ci gaba da kukanta. a hankali yace,"dama ta mutu kowa ma ya huta". "ɗan banza mai mugun jafa'i kaga mutuwa akanka. dalla Malami ka tashi anan wurin uban wa ma ya kawoka". bai kulata ba ya kama bakina ya matse ya zuba min maganin, tukunna ya zuba ruwa ya matsen hanci yace idan na dawo da shi sai raina ya ɓaci, haka babu yanda na iya dole na shanye inata kakarin amai. "ina da ina ke miki ciwo dama?". ko kallonsa banyi ba na nuna masa kaina kawai, ya kama kan yay min adu'a tukunna ya tashi ya fita. ba jimawa kuwa bacci ya ɗaukeni dan naji daɗi sosai dama ciwon kan ne ya addabeni. washegari da safe ina zaune ni ɗaya a parlo na ɗan ji daɗin jikina, Yaya Haidar ne ya shigo, nai saurin miƙewa zan wuce ɗaki saboda irin rigar dake jikina, ya kalleni ya taɓe baki, na harare shi ta ƙasan ido nima na murguɗa masa baki na wuce ɗaki. a dining na dawo na sa me shi yana zuba tea a cup, na wuce na kwanta kan kujera ina ci gaba da kallon cartoon ɗina, ya dawo ya zauna a kujeran dake facing ɗina. ya ɗau remote ya sauya channel yana kurɓan ruwan tea, ina marairaicewa nace,"Yaya Haidar dan Allah ka mayar min". ta gefen ido yay min kallo ɗaya, kamar ba zai mayar ba sai kuma ya maida ya aje remote ɗin, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana cigaba da kurɓan tea ɗinsa. "tashi zaune". nayi kamar ban jisa ba, sai daya kuma ɗaga murya yace,"ba za ki tashi zaune ba. ke ko gajiya ba kya yi da kwanciya, a haka za ki ji ƙwarin jikinkin naki". nan ma shiru na masa sai murguɗa baki da nayi ta gefe. "idan ba ki miƙe zaune ba babu abinda zai hanani juye miki ruwan tea ɗin nan idan na iso nan wurin". ya faɗi hakan yana ƙoƙarin miƙewa, aiko nai saurin tashi zaune ina aikin zumɓura baki, dan nasan kaɗan daga cikin aikinsa. Gwaggo ta fito tana cewa,"kai dai wannan yaro anyi mugun mutum. to ni dai karka ƙara ɗaga ma ta murya bata da lafiya. ka barta taji da jikinta". "ina kwana Gwaggo". yace da ita. "lafiya". ta amsa masa a daƙila kafin ta kuma cewa,"na ganka da sassafe haka". ya ɗaure fuska dan yasan yanzu zata yi halin nata, yace, "breakfast nazo yi". "to baka da labari na daina ciyar da ƙatti ne, to gaskiya anjima karka dawo saboda ni yanzu bana girki da ku. Zara'u ce ta ke dafa muku saboda Allah ya shiryeta, yanzu ma idan kaje ƴan'uwanka suna can suna kwasa, da mai cin da mara cin duk acan suke yanzu. jiya ma naji batun katan ɗin taliyarta ya ƙare, nace ai sai dai haƙuri kuma". yace,"to ni gaskiya anan nake son cin abincina kuma anan
🏠