NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 94 of 98

wanda hakan ya zama dalilin farkawar Alhussain a gigice yana ambaton sunan Allah. ya shiga murza idanuwansa yana daɗa ƙarewa ɗakin nasa kallo dan tabbatar da mafarkin da yay ba gaskiya bane. ya sauke ajiyar zuciya yana mai duban agogo dake saƙale ajikin bango. "10:00am". ƙarfe goma na safe haka agogon ya nuna, sai ya mayar da kansa ya jingina ajikin gado yana me haɗe murfayen idonsa ya rufe. lokaci ɗaya mafarkin da yake yi tsawon kwanaki uku a jere ya shiga tariyo masa acikin kansa, kwana uku kenan wannan matar tana zuwar masa da magana ɗaya. _"wace ita?, kuma me yasa take waɗannan maganganun?, wanne irin saƙo take so ta bar masa? me alƙalamin ƙaddarar ya rubuta? sunan Hussain da ta ke kiransa da shi daga ina ya samo asali?"._ sai kawai ya shiga sauke nunfashi da sauri-sauri. _"ba zaka aureta ba, ka cireta a ranka muddin ina nunfashi."_ wannan maganar ta kuma haskawa acikin idonsa, a wani zabure ya buɗe idonsa yana fitar da huci yayin da yake damƙar zanen gadon da kyau yana jin kamar zai jijjige ɗakin baki ɗaya. ** yau sati guda kenan ina fama da ciwo, zazzaɓi yay min wani irin kamu duk na rame na fita a hayyacina. yaune kawai na samu ɗan dama-dama na fito parlo, shima a kujera na kwanta dan bana iya zama saboda rashin ƙwarin jikina, ko school ban je ba tunda aka koma yau sati biyu kenan. kuma ba komai ya haifar min da wannan ciwon ba sai mafarkin da nayi, mafarkin wani dattijo da nayi yana min nuni da wani mutum dake zaune kan kujera kamar wani sarki, yayin da yake faɗa min cewa wannan mutumin shine mafarin ƙaddarata, kuma akansa ne alƙalamin ƙaddarata yay rubutu. a yayin da ƙaddara ta ɗauremu ni da shi a wannan lokacin zan tsunduma a duniyar farinciki, sai dai kuma abu biyu zai haɗe min a lokacin, wannan lokaci gudan da nake cikin farinciki zai haɗe min da kuka mara iyaka. a duk lokacin da nai ƙoƙarin ganin naga fuskar na kan kujerar sai na gagara, a jiya ne dana tunkare shi ina taɓa kafaɗarsa sai naga ya faɗo daga kan kujerar, kuma ta ke iska ta ɗauko wani farin ƙyalle wanda yayi kama da linkafani ta rufeshi gaba ɗaya, ban san ta yanda zan kwatanta tashin hankalin da na shiga ba, amma dai nayi dakiyar tsugunawa gaban gawar na kai hannu zan buɗe fuskar dan ganin waye, kuma a daidai lokacin dana kama likafanin zan ɗaga lokacinne Gwaggo ta shigo ta tasheni daga barci. dalilin daya sa gabana yake ta faɗuwa kenan har zuwa yanzu, na kuma gagara gane fassarar mafarkin, tashin hankalina ɗaya kar ace silar taɓa shi ne na zama ajalinsa, gashi ban san ta inda zan yiwa Gwaggo bayani ba tunda ance ba'a faɗar mummunan mafarki. "ya jikin naki". muryar Anty ta faɗa a sanda ta ke shigowa parlon, na ɗaga kai na kalleta ina amsa sallamarta har ta ƙaraso inda nake ta zauna. masu karatu kunji abun kamar almara ko, haka dai muka wayi gari Allah ya shiryar da Anty, hakan kuma yay ma kowa daɗi musamman ma ni, dan yanda ta ke lura dani babu ha'inci sai nake jin kamar ƙanwar uwata. "kinci abinci?". ta tambaye ni cike da kulawa, na girgiza ma ta kai ina cewa,"komai naci ɗaci Anty, bakina ba daɗi". ta kamani tana miƙar dani zaune ta ke cewa,"to haka za'ayi mutum dan Allah babu cin abinci babu shan magani, Sabina sauƙi fa muke nema dole sai kinyi haƙuri". ta taɓa kaina taji zafi rau, pillow'n kujera ta samun ta bayana ta jinginar dani, ta miƙe ta shiga ɗakin Gwaggo, tana sallah ta sameta, sanin sallar Gwaggo ba mai ƙarewa bace da wuri yasa ta tambayeta ina maganina, tayi ma ta nuni da drower, ta ɗauko ta fito. curstard ta dama, duk sona da shi kasa sha nayi, har Gwaggo ma ta fito suna ta fama da ni amma naƙi shan ko da spoon ɗaya bare nasha maganin, kowa sai roƙona yake akan na daure nasha maganin amma naƙi sai ƙara narkewa nake inawa Gwaggo kuka. ita dai duk hankalinta tashe yake, sam bata so ta rasani, ana haka Yayana ya dawo daga school, shima duk yanda ya lallaɓa ni ƙememe naƙi shan maganin, Yaya Abba kuwa dama shi ko ta kaina baya bi, ga jikina ƙara tsananta yake zafi rau kamar wuta, ga uban amai da nake kyalawa. Gwaggo kuka ta saka tana cewa,"wannan yarinya kwai muguwa, kawai dan kinga ke ɗaya Allah ya jarabceni da mahaukacin sonki shikenan sai ki dinga yi min baƙincikin rayuwarki, yanzu idan ba ki sha maganin ba taya za'ai ki samu sauƙi, an san dai sauƙi na wurin ubangiji amma don Allah dan Annabi Sabina ki daure kisha maganin nan ko kema kyaji ƙwarin jikinki, tun safe ake fama dake akan abu guda". na miƙe zaune ina cewa Anty ta bani curstard ɗin na sha, ina kai cokali ɗaya bakina nayo amansa, na fashe da kuka domin nima Allah ɗaya yasan irin wuyar da nake ci. Yaya Haidar ne ya shigo, kowa ya maida hankalinsa ga sallamar da yake. "a'a Haidar an sauka?". da yake yaje ganin gida kusan satinsa uku. "ehh Anty". ya faɗa yana zama a kujerar kusa damu. ya miƙawa su Yaya Abba hannu suka gaisa, kallon ball ɗinsu suke hankali kwance, Yayana da Yaya Abba sai uban musu sukeyi akan ball ɗin. Gwaggo ta miƙe tana masifa taje ta kashe TV ɗin, ta fuskancesu ta
🏠