ace, har na hangosu a lokacin biki". Daddy yana riƙe da hannunta yace,"kema Daughter ina roƙon Allah ya fito miki da miji kamin zuwan lokacin, na haɗaku gaba ɗayanku. ba ƙaramin farinciki zanyi da wannan rana ba". Haka dai suka ci gaba da harkokin su, Anie na cewa ta fasa tafiya har sai kishiyarta tazo ta gaisheta. da daddare kuwa Daddy ya shiga ɗakin Mom, ya sameta zaune a tsakiyar gado hannunta riƙe da wani medium enlargement tana kallo tana kuka. cikin hanzari ya ƙaraso gareta, ya amsa hoton daga hannunta ya ajiye sannan ya kwantar da kanta bisa kafaɗarsa yana lallashinta, sai da ƙyar ya samu ta tsagaita da kukan. yace,"yanzu Sweetheart har sai yaushe ne za ki bar wannan kukan umm? Mutasim fa ya tafi inda ba'a dawowa ya kamata ki haƙura ki fawwala Allah". tace,"Daddy a kullum ina ji ajikina wataran Mutasim zai dawo. ko a jiya nayi mafarki da shi, nafi tunanin yana raye bai mutu ba, kawai dai yana cikin wata rayuwar ne". Daddy ya sauke ajiyan zuciya yace,"but you know that dreams are not real. How can a person who has been missing for 27 years be back?, think of yourself. If he were alive ai da mun ganshi, dan Allah ki daina yawan sa shi a ranki kar wani ciwon ya kamaki". ta ɗago ta dube shi tana cewa,"Daddy karna ƙwallafa abinda na haifa a raina kenan? ni fa rashin ganin gawarsa ita tafi damuna, naso ace naga gawarsa nayi masa adu'a, yaron da bai jima da gama shan nono ba, rashin ganin gawarsa yasa har yanzu na kasa yarɗa da cewan ya mutu, Allah kaɗai yasan a wacce rayuwa yake ciki yanzu". kuka ta fashe da shi sosai, Daddy yaji tausayin matar tasa a ransa matuƙa, yana shafa bayanta yake bata haƙuri da lallashi har ta samu nutsuwa. daga nan ya kashe musu fitila suka kwanta yana manne da ita a jikinsa.
ɓangaren Muhsin kuwa tunda ya shiga ɗaki yake a fargaba, yanzu idan su Daddy suka je gidan su Beauty suma tace musu bata sonsa ya zaiyi? ya riga ya kamu da sonta wanda zai iya shiga wani hali a dalilin rashinta. wayarsa ya ɗauko yay dialling numba nata, domin ko kaɗan shi bai yi fushi da ita ba da abinda tayi masa, ya ma ta uzuri ne kasancewarta yarinya. haka wayan ya ƙaraci ringing nasa amma ba ta ɗaga ba, sai dai ya kwana da tunanin dole sai ya kama ƙafa da Yayanta da ta ke yawan masa zancensa, tunda ya lura tana sonsa tana kuma jin maganarsa, wataƙila idan yabi ta hanyarsa ta amincewa ƙudurinsa.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(29)*
"ka cire soyayyarta daga zuciyarka, ka cire burin aurenta a ranka...ka barta a wannan matsayin da kuka fara bawa juna tun farko". "saboda me?". "saboda ba zaka sameta ba, Hussain ba zaka aureta ba muddin ina numfashi a doron ƙasar nan". wannan furucin shi yasaka Alhussain saurin zuro ƙafafunsa ya sauko daga kan gadon, ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa yana ƙarewa bayan matar da baya iya kallon fuskarta kallo, kallonta yake da saƙawar mabanbanta abubuwa acikin ransa. sai dai a duk abunda ya saƙa ɗin baya iya warware shi, saboda haka yayi tattaki zuwa inda ta ke a tsaye jikinta naɗe da lafaya brown colour, tana fuskantar kusurwar ɗakin nasa ta ɓarin hagu, daga tazarar da ba zata wuce inchi 2 ba a tsakaninsu ya dakata. sannan ya tattaro yawun bakinsa da yaji kamar yana neman ƙafewa yace da ita,"wace ke?". shiru tayi masa bata bashi amsa ba, ya rufe ido ya zuƙi numfashi, gami da sanya hannu ya shafo sumar kansa yana kaiwa cinyarsa duka. "Wace ke? kuma me yasa kike min waɗannan maganganun?". ya ƙara tambayarta amon muryarsa na cika ɗakin gaba ɗaya. maimakon amsar daya tsammaci ji daga gareta sai yaji sautin murmushinta ya fita a hankali, wanda ya tabbata murmushin ya tsaya mata iyaka leɓe ne kawai duk da cewar bai ga fuskarta ba. zuciyarsa tayi wani zafi dan haka bai san lokacin daya ɗora hannu a saman kafaɗar matar ba dan juyo da ita, amma abu biyu ya hana hakan, farko wani azababben shock daya ji ya ratsa gaba ɗaya jininsa har yay saurin ɗauke hannunsa yana yarfewa, sai na biyu kuma da matar taƙi juyowa tana me ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tare da matsawa, kuma bakinta na furta masa,"ba yanzu ba Hussain, ba yanzu zaka sami waɗannan amsoshin ba, da sauran lokaci". tsaye yayi yana tsare bayanta da ido, dan ya tabbata in har ya ƙara taku ɗaya to zsta iya guduwa. "ban sanki ba, kuma kema nasan baki sanni ba, dan haka ki fita acikin rayuwata da kike ƙoƙarin shiga...ba ruwanki da lamarin soyayyata balle aurena". wannan karon a zafafe yake maganar, yana mai yin ƙoƙari wajen ganin ya wata dabarar da zata sa matar ta juyo yaga fuskarta. "tukunnama! me kike nema a wurina?". kai tsaye kuma ya ji muryarta fa fito da cewa,"kai nake nema Hussain, kai nake nema na faɗa maka muddin baka cire soyayyar yarinyar nan tunda wuri a ranka ba to la shakka zata zame maka guba, Hussain karka Ƙwalla soyayyarka akanta domin hakan zai illataka...kuma abu na ƙarshe da nake so na faɗa maka shine, Alƙalamin ƙaddara bai rubuta abunda ku ka tsarawa kanku ba Hussain". da gama faɗar hakan ɓat sai matar ta ɓace.