NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 92 of 98

kuka cike da takaicin wannan hali na uwarta. Abid ya shigo ya sameta ahaka, ya nemi kujera ya zauna a hakimce yana ma ta wani mugun kallo, ƙafa ɗaya akan ɗaya yana girgizawa. "kin bar kukan nan ko saina tashi na zane miki jiki". yace da ita murya a ɗage. ta dube shi tace,"Bross dan Allah ka cewa Mami ta sauya halinta wannan ba hali ne mai kyau ba". shima murya a fusace yace,"ke ai jaka ce, ba ki san inda yake miki ciwo ba sam. taya za'a Mami ta ƙaunaci mutanen da suke sa ubanmu ya muzguna mana. tunda kike kin taɓa ganin Daddy ya ɗorani akan wani harkar business ɗinsa?, ya ɗau komai ya bawa wancan Muhsin ɗin, shege Allah ne ma yasan manufar jaki da bai bashi ƙaho ba, shi yasa aka riƙe masa ƙafafu". ta tashi zata wuce ɗaki tace,"ai mai gaskiya ake ɗorawa akan komai ba maha'inci ba. da kayo kyawun hali irin nasa da babu ta yanda Daddy zai nuna banbanci tsakaninku". tana ganin ya biyota tai hanyar ɗakinta ta gudu, tana faɗawa ciki tasa key ta rufe tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, dan da ace ya kamata sai taci ɗanyen kashinta yau. washe gari ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo daga Italy daya tafi. Muhsin na zaune kujera ɗaya da Daddy a kusa da shi, suna magana ƙasa-ƙasa da alama zancen sirrinsu ne, suma gefe ɗaya su Mom ke tasu hiran. Daddy ya lura tun ɗazun idon Muhsina na kansu, so kawai ta ke taji me suke cewa, yay murmushi cike da tsokanar ƴar tasa ya kuma yin ƙasa da kansa suna ci gaba da mgana. da ƙarfi Muhsin yace,"a'a Daddy ba ita ya kamata a bawa sabon company ba, Muhsina ai tayi yarinya da yawa, macece fa ita ba zata iya aiwatar da ayyukan company ba, a barta kawai da lecturing nata idan yaso sai a bawa Abid, shi zai iya lura da komai". ai kuwa tana jin haka ta miƙe ta fara dukan ƙafa tana kukan shagwaɓa har saida ya koma na gaske, tana cewa da Mom,"Mom kinji abinda Brother yake cewa ko, shi dama duk abinda yaga za'ayi min sai yace a'a, shi Abid ɗin ba ni ke gaba da shi ba. haka fa aka yimin wancan karon ma, ni dai gaskiya Daddy ban yarda ba". Daddy yana dariyar manyance yace,"to kwantar da hankalinki Daughter nah, we're just kidding you". sai ta fara dariya itama ta dawo kusa da Daddy ta zauna, yasa hannu ya kwanto da ita jikinsa yana faɗin, "wato dai sirikina zai sha fama, har yanzu kinƙi girma". kunya ya bata tai saurin rufe fuskarta. Muhsin na duban Mahaifiyarsa yace,"Mom kin manta ba ki faɗawa Daddy saƙona ba ko?". tana masa wani duba tace,"O'O! ba mantawa nayi ba, ina jira ne ya gama hutawa sai na sanar masa". Daddy yace,"hutun mene dama zan kuma yi?, good 3hours da dawowa na fa, hutawana yafi saƙon ɗana ne?". yay maganar da sigar faɗa. tace,"kayi haƙuri, dama cewa yay na sanar maka aure yake so domin ya samu mata, sauran bayani kuma kaji daga gare shi". Daddy ya dubi ɗansa cike da farinciki a fuskarsa yace,"are you serious? da gaske ne ka samu wadda ta yarda da aurenka a haka?". Ya ajiye file ɗin hannunsa gefe guda ya kamo hannun Muhsin yana daɗa kallonsa yace,"ina jinka son, ka sakani a farinciki, wace kake so kuma take sonka?". Shafa ƙeya Muhsin yay yana sunkuyar da kai ƙasa yace,"Daddy da gaske ne, Yarinyar ta aminta da ni". sai kuma ya marairaice fuska yace,"amma Daddy kar ayi westing time saboda ina gudun mahaifinta ya bawa wani ita, ba zan iya jurewa ba". Murmushi Dad yayi, ya shafa kan ɗan nasa shima kuma ya shafa gemunsa kafin yace, "Okay Son, Anything for you, ba zanyi sanya ba zaka sameta insha'Allahu. Uncle naka baya nan yana Cairo, but ending of this week zai dawo, so as soon daya dawo za muje mu gana da mahaifinta". Muhsin ji yake kamar zai mutu dan murna, ya kusa mallakar Beauty tasa, duk da ya yarda bata sonsa amma ya yarda zata so shi yayin daya mallaketa. Daddy yace,"Anan garin ta ke ko a wani state ɗin ka samo ta?". yace,"anan Abuja ta ke sai dai ban sa ni ba ko ƴan asalin ina ne". "Okay son, it shall be well, za muje ayi komai, worry not kaji. but can i get some information about her? like part of her education and her parents". yace,"Yeah Dad why not, her name is Sabina Auwla, she is one of my students yanzu haka L1 ta ke, she is well educated both arabic and boko, her father is the MD of PHCN. I recently went to their house, kuma da ganin gidansu gidan mutunci da karramawa ne duk da ban samu ganawa da wani a gidan ba, amma naga hakan daga wurin gate man nasu". "Okay Son, kamar an gama ne, karka wani damu kaji, kasa a ranka kama gama samunta". Cike da jin daɗi Muhsin ya rungume mahaifinsa, ya kuma buɗewa Mom hannu itama, ta taso daga inda take tazo ta rungume shi, Wadda kallo ɗaya za kai ma ta kasan tana farinciki da wannan maganar. Muhsin yace da Anie,"Anie ke ɗaya ne ba za ki tayani murna ba?". tana shafa makekiyar wayarta tace,"to Alhaji Hassan murnar me zan tayaka alhalin kana ƙoƙarin yimin kishiya. ai sai dai kawai na bika da adu'a Allah yasa yarinyar ƙwarai ce". Muhsina ta amsheta da cewa,"wallah kamar kin sa ni Anie, ga kyan hali gana fuska. wallahi duk kyauna dana ganta sai dana raina kaina, ai Brother nah yay d
🏠