NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 98

fuskata ba sai ƙara ɗaureta da nai, na miƙe ina cewa,"muje kitchen ɗin". itama kuma sai ta ɓata tata fuskar, tai kicin-kicin da ita har muka sauko muka shiga kitchen, kuma da yake zuciyar kowa a wuya take ko Hajiya dake mana magana ma bamu saurara ba muka shige Kitchen, na ƙarasa drowern dana hangi ƙaton cooler ɗinsu da anan ake zuba abinci, ita kuma ta tsaya gefe tana kallona, ƙaramin plask na ɗakko na zuba dankalin da ƙwan a ciki, na samu wani plask na tea ƙarami bayan na haɗa tea ɗin na zuba a ciki sannan na dubi Farhana nace,"muje ki raka ni". tana dubana da mamaki tace,"gida ko ina? ban fahimce ki ba, cin abincin ne ba zakiyi anan ba ko me?”. na ƙara jan ɗogon tsaki saboda tana neman ta ɓata min lokaci da wannan shegiyar tambayar tata. "kinga Gwaggo Farhana, wannan abincin ban zuba dan cikina yaci ba...so rakiya zaki yi min, idan baza ki raka ni ba sai na tafi ni ɗaya ba komai bane ai tunda ni ba makauniya bace balle tafiyata ta zama dole saida ɗan jagora". na faɗa ina bin gefenta zan fice, sai tayi saurin kamo hannuna tana faɗin,"daɗina da ke kenan, babu baya ni sai saurin fushi. kin shigo da damuwa tare dake, ke biki yi min bayani ba sai neman sauke fushinki kike akaina...ina zamuje dama?”. "anguwa”. na bata amsa a taƙaice. tai ɗan jim tana min kallon tsanaki, sai da ta gama nazartata tsaf tukunna tace,"wurin mahaukacin jiya zamu koma?". tayi tambayar da rainin hankali. a ƙufule kuwa nace da ita,"kin faɗa sau biyu kenan, karki gigin ƙara jingina shi da wannan mummunar kalmar a karo na uku, ina faɗa miki ne dan kinji da kyau. Farhana mamaita kalmar can daidai ta ke da yankewar alaƙar dake tsakaninmu, i dont fucking care dan mun rabu". ina faman huci nasa kai zan fita taƙi matsawa,"ki ban hanya zan wuce. ina ce kince ba ki rakani ko. kinga ki daina ganin kamar idan babu ke ba zan iya tafiyar nan ba, nasan hanya sarai, so da ace jagora za ki min sai na tsaya ki gama faɗa min baƙaƙen maganganunki...kinga tafiyana". ina kaiwa nan na tureta na fita, ta ƙofar baya nabi yadda Hajiyarsu ba zata ganni ba. nayi sa'a yanda nake saurin nan ina fita na sami napep, Allah ya taimaka bai tsawwala min kuɗi ba, dama ba isashshen kuɗi ke garen ba, shi yasa ma nace Farhana tazo muje tunda ita a motarta ne. ina sauka daga napep ɗin na nufi cikin bolar, kai tsaye kuma cikin kangon na faɗa, a tunanina zan ganshi amma sai ban ganshi ba, na fito ina ƙara dudduba bakin bolar da gefe da duk inda dai idona idan ya wurga zaiga mutum, amma sam babu shi, sai naji wani abu mara daɗi na bin jikina, na koma cikin kangon na aje basket ɗin abincin na fito ina ƙara dube-dube. ta hannun haguna na gange shi can ƙarshen bolar kwance shame-shame, da sauri na nufi wajen, ina zuwa ban kula da komai ba na durƙushe a wurin na rarumo shi jikina ina faɗin, "subhanallah! Yaya meye sa kazo nan ka kwanta, baka da lafiya?". na tambaya duk a ruɗe ina taɓa kansa, amma babu zafi. "Yaya tashi mu bar nan dan Allah". Kallona kawai yake yi, yayinda ko leɓan shi bai samu damar furta kalma ɗaya ba, yayi min nauyi amma a hakan nake ƙoƙarin ganin na janyo shi da iya ƙarfina, sai dai sam na kasa, kuma ganin hakanne yasa shi miƙewa zaune kafin ya dubeni da kyau yace,"tashi”. muryarsa na fitowa da kaifi kamar na reza. na miƙe lokacin da idona ya cika tapp da ruwan hawaye, sannan shima ya miƙe, nai saurin kama shi ganin kamar zai faɗi, kayan jikinsa duk wari suke amma wannan sam bai dameni ba, haka nake kamashi ajikina bana ko lura da ɓacin da kayana zasu yi da najasar wurin. ya ƙwace a jikina yana cewa,"bar nan wurin". ƙwayar idonsa ce ta shaida min baya so ya ƙara maimaita min, hakan yasa naja da baya har na sauka daga saman bolar, tukunna naga ya fara takowa a hankali har ya sauko daga kan bolar shima, bai ko kalleni ba ya wuce ya shige cikin kangon, ganin haka yasa nima nabi shi na shiga ciki. A ƙasa na same shi zaune, nima na samu wuri na zauna ina duban shi kafin na furta, “Yaya baka da lafiya?...au ina kwana". bai amsa ba, sai ido daya kafe ni da shi yana nazarin rashin hankali irin nawa, tsawon wasu daƙiƙu kaina yana ƙasa na jiyo muryar shi na fita da faɗin, “Sabina ko?”. nai saurin ɗago kaina, “eh” .na bashi amsa. sai kuma muryarsa tayi ƙasa, "me yasa kika dawo inda nake?, wai meye sa baki da tsoro ne?, ke bari kiji na faɗa maki, nifa ɗan iska ne, ɗan yan kan kai ne, ina yanke kan mutane na kai ayi tsafi dasu, ki daina zuwa wuri na idan ba ki son na yanke kanki, ko nayi maki fyaɗe, dan duk na saba yinsu”. abunda zance a wannan lokacin maganarsa ta bani nishaɗi, furuci ne da ko kusa baiyi kama da shi ba, ya faɗa ne kawai dan ya tsoratani, dan da ƙyar ma ya dinga haɗo kalmomin. na saki ƴar ƙaramar dariya ina faɗin. “Yaya ai babu mai yiwa bawa wani abu fa ce abinda Allah ya rubuta zai sa me shi, kuma idan kai ɗan yankan kai ne, ai da baka zauna a haka ba, da baka zauna anan ba, da tuni kana da dukiya mai yawa kamar yadda masu yi suke da ita, ni bana jin tsoro
🏠