ɗaya daga kujeran dining tana cin fruit tace,"Mom, thats what am thinking, but he might be on his way back ko kuma ya tsaya wurin seminer da Daddy yace zaije". Mom tace,"I don't think so, he could have informed me if that was the case. wayansa ma fa not recherble gaba ɗaya, fatana Allah ubangiji yasa lafiya". she spoke in anxiety way har tana jin ƙirjinta na beating faster. "ni fa am worried da rashin dawowan yaron nan har yanzu, is everything alright? haba he's a determined boy, banda haka me ne zaisa shi fita aiki? ya zauna wuri guda tunda ubansa ya tara dukiyar nan ya ajiye musu. anyway to ya dawo yau ɗin ya sameni". Tsohuwar Matar dake sakkowa daga stairs ke wannan maganar cikin faɗa, sanye take da lapaya orange colour fuskarta kuma ɗauke da glass me yanayin na fashions amma kuma medical ne, kana kallonta kaga mahaifiyar Mom saboda tsananin kamansu, Mom da Muhsina suka maida dubansu gareta. ta kuma cewa,"Fa'iƙa zaman me kike da ba za ki tashi muje dubo shi ba? yaran da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba". Mom tace da mahaifiyartata, "Anie we are sitting here driver went to pick him up. ni ba wannan ba ma, not knowing the reason for their returning early shine yafi damuna, since he had never reached such a time. ga wayoyinsa duka basa tafiya". Anie sighed and said,"shi drivern babu waya hannunsa ne da aka gagara tuntuɓarsa aji halin da suke ciki?". dukansu basu kai ga kuma furta ko wacce kalma ba wayar Muhsina ta fara ringing, ta ɗauka da sauri tana cewa,"yauwa Mom gashi ma ya kira". daga ɓangaren Muhsin yace,"Sister am back". yana faɗin hakan ya kashe wayan. dukansu suka sauke ajiyan zuciya, sai yanzu nutsuwa ta samu a garesu hankalinsu ya kwanta, lallai ba ƙaramin ji da shi ake a wannan gida ba, minti biyar kawai ya ƙara akan lokacin dawowansa amma hankalin kowa ya tashi, ana tunanin ko ba lafiya ba, tabbas shi ɗin ɗan gata ne gaba da baya. Anie tace, "lamarin Hassan sai shi, wato har yanzu idan ya dawo dole dai sai Muhsina taje tarbo shi tukunna zai shigo". Mom tace,"ai haƙurinsa ɗaya idan bata nan, amma anan kuma dole ni ce zan fita. yace damuwa yake shiga indai yagansa shi ɗaya yana tafiya a keken nan, kuma baya so yake saka ma'aikata turo shi". Muhsina na isowa entrance ta iske Mami na balbalin masifa, ita dai wannan mata kwai jarababba, ko da yaushe acikin masifa ta ke muddin wani abu zai shiga tsakanin ƴaƴanta dana kishiyarta, Muhsina tayi tsaki taja ta tsaya cike da takaici, ta tsaya ne kawai saboda Mom ta hanasu saurarenta idan tana wannan haushin karen, amma da bata isa ta tsaya kan Brother tana masa wannan hargowan ba. Khaleesat ita dai ƙuri tayi ta rakuɓe daga bayan keken Muhsin, ita kanta yarinyar bata son wannan halin na uwarta, sai noƙewa takeyi gudun karta kawo mata duka, muryarta a hankali tace,"Mami kiyi haƙuri please". aiko kamar ta watsa mata petrol ta damƙo kafaɗarta tana cewa,"kin rufe min baki ko saina zubar miki da haƙora anan wurin, shashasha wadda bata da kishin uwarta, to dama kin zama ma'akaciyar jinya ne da kika zo kinibibin taimako?, ke ga ƴar neman suna, ko kuma dama ke kike taimaka masa tun asali?. Abid ne ya rasa ƙafa da za ki tashi hankalinki akansa? keken nasa ai da inji yake aiki me ya hana ya kunna ya gurgura da kansa?, a'a ke ga ƴar neman gindi ya zama dole kiyi aikin da babu lada, ni dai wannan ƴa banda a hayyacina na haifeki wallah da zance ba jinina bace ke, tunda na haifeki ba ki taɓa faranta min rai ba kullu yaumin acikin baƙanta min kike, anya Khaleesa kina so ki gama da duniya lafiya kuwa? ni fa uwarki ce wata goma cif haka na ɗau cikinki. na kuma sha baƙar wuya kamin ki fito saboda an riga an min asiri ba'aso na haihu dan baƙin ciki da zalunci, haka aka jefeni da ciwon nono saina waccan shegiyar matar ubanki yasa aka dinga ɗirka miki kina zuƙa, to banda Allah yasa ma na tashi tsaye na nemi maganin tsari a gareki ai wallahi da babu abinda zai hanaki ɗauko baƙin halinta gaba ɗaya tunda kin sha a ruwan nono. banza kawai kin wani taho da rawar jiki kamar ƙanin uwarki ne ba lafiya, ana gudun nakasassu amma ke tusa kanki cikinsu kike saboda hankali bai gama isarki ba, haka kawai ina zaman zamana ki jawo min masifa kema ki shafi ciwon gurgunta a haɗa biyu, dama ana min baƙinciki da ku, yanzu ace akanki tattalin arziƙin ubanki yake ƙarewa, dan shi Ubanki ko duka arziƙinsa zai ƙare wurin ɓarnatarwa wannan gurgun ba zai taɓa gani ba tunda tsatson waccen ne, ta riga ta gama da shi, amma ke kuwa daga ke harni wuya zamu sha". ita dai Khaleesa shiru tayi ta rasa abin cewa, yanzu tana buɗar baki Mami zata aikata abinda tace, ita kuwa bata shirya rasa haƙoranta ba, yanzunma sai dai Allah ya kiyayeta idan sun koma part nasu, dan Mami ba dai mita da jaraba ba. Mami ta maka ma ta wani shegen kallo tare da kamo kunnenta ta murɗe har saida Khaleesa tayi ƙara. "yau ya zama rana na ƙarshe da zan faɗa miki bana so kike kula wannan gadon tsiyar, idan kuma kinƙi ji wallahi saina tsine miki tunda ke kunnen ƙashi gareki, ke ko u